African LanguagesHausa

Da gaske ne gwamnatin jihar Jigawa ta tilasta wa jami’an tsaro mata sanya hijabi?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Gwamnatin Jigawa ta tilasta wa jami’an tsaro mata sanya hijab a jihar.

Da gaske ne gwamnatin jihar Jigawa ta tilasta wa jami’an tsaro mata sanya hijabi?

Hukunci: Yawanci Gaskiya ne. An umurci cibiyoyin tsaro ne da su bai wa ma’aikatansu damar sanya hijabi a lokacin aiki, amma gwamnati ba ta tilasta musu ba.

Cikakken Bayani

A duk lokacin da ake magana a kan batun tilasta sanya hijab, yana daukar hankalin al’ummar Najeriya mai mabanbantan addini da kabilu daban daban, saboda banbancin al’adu tsakanin mazauna kudanci da arewacin kasar

A ranar Laraba 16 ga watan Afrilu wani shafin Facebook mai suna Indaranka ya wallafa cewa gwamnatin jihar Jigawa ta bullo da wani tsarin tilasta wa jami’an tsaro mata sanya hijabi.

Wannan labari ya karade shafukan sada zumunta musamman Facebook kamar yadda DUBAWA ta gani a nan da nan da kuma nan.

Mutane da dama sun yabawa wannan matakin da wasu ke ganin gagarumin ci gaba yayin da wasu ke ganin ba wannan ne al’umma ke so ba.

“Wannan ba shi ne matsalar mu ba, idan za ku gyara ku gyara, ba zamu yarda da renin Hankali ba wallahi.” a cewar Ahmad Ahmadiy.

Ganin yadda wannan labarin ya haifar da cece-kuce, ya sa DUBAWA yin bincike domin tabbatar da sahihancin wannan labari.

Tantancewa

DUBAWA ta fara garzayawa a shafin Facebook na gidan gwamnatin jihar Jigawa domin duba ko ya wallafa wannan labarin da ake yadawa.

Mun samu wani bayani mai dauke da sa hannun Sagir Musa Ahmed, kwamishinan yada labarai da al’adu na Jigawa, wanda aka yi wa taken “Takaitaccen bayanin bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a ranar Litinin 1 ga Afrilu 2025”

A cewar kwamishinan, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro uku da ke aiki a jihar,  da su ba wa mata jami’an tsaro damar sanya hijabi a lokacin da suke bakin aiki.

Ya ce wannan shawarar ta biyo bayan rahoton da kwamitin samar da tsaro ga makarantu, asibitoci da kuma kotunan jihar ya gabatar.

“Wannan na daga cikin kokarin gwamnatin jihar Jigawa na samar da yanayi mai hade da walwala ga dukkan ‘yan kasa musamman mata, daga cikin matasa 9,969 da ke aikin samar da tsaro a wurare daban daban” in ji Sagir Musa Ahmed

Jarida Punch da Pulse duk sun ruwaito labarin.

Na yi kokarin jin ta bakin sakataren yaɗa labarai na  gwamnatin jihar Jigawa, Hamisu Gumel, sai dai bai amsa sakon da na tura ba da kuma kiran waya.

A Karshe

Binciken DUBAWA ya gano cewa gwamnatin ta bayar da damar san ya hijabi a lokacin aiki, amma gwamnati ba ta ce tilas ne ba kamar yadda wasu su ke zargi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »