African LanguagesHausa

Da’war cewa Bill Gates ya bukaci a tattara bayanan jarirai (digital IDs) a Kenya, yaudara ce 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wata mai amfani da shafin Instagram tayi da’awa cewa Bill Gates ya bukaci a tattara bayanan yara ta hanyar dasa masu karamar na’ura a jikinsu a Kenya.

Da’war cewa Bill Gates ya bukaci a tattara bayanan jarirai (digital IDs) a Kenya, yaudara ce 

Hukunci: YAUDARA CE! Sashi-sashi na bidiyo da aka yi amfani da su basu da wata alaka, an tsakuro su ne daga wasu taruka daban-daban daya a 2015 dayan kuma a 2023. Babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta fitar da rahoto da ya tabbatar da wannan da’awa. 

Cikakken Labarin 

Shahararren mai kudin nan mai kuma taimaka wa al’umma Bill Gates a baya-bayan nan ana ta cece-ku-ce a kansa a dangane da ba da bayanan da ba haka suke ba kan abubuwa da suka shafi lafiya da fasaha musamman a nahiyar Afurka. Tsawon shekaru ana yada labarai da ake alakanta shi da su kan abin da ya shafi rage al’umma ta hanyar allura da sauran abubuwa wadanda sau tari ba haka abun yake ba.

A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin Instagram @digitalproductsuk ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa a baya-bayan nan  Bill Gates ya bukaci a tattara bayanai ta hanayar  dasa karamar na’ura a jikin yara da ake haifa a kasar Kenya. Wannan bidiyo ya rabu zuwa kashi uku, inda aka yi bayani cewa yaran da ake haifa za a dasa masu bayanai a jikinsu kafin ma su bar asibitin. 

A bangare na biyu na bidiyon, Bill Gates ke magana a kan mdashe yana cewa “za mu dauki abubuwa wadanda kwayoyin halitta ne da aka jirkita za mu yi dashensu”a cewarsa.

Bidiyo na karshe sai ya nuna Shugaban kasar Kenya William Ruto, yana bayani kan batun tattara bayanai a tsarin na zamani wato (digital) a yayin wani taro.

Wannan da’awa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 26,200 (likes) da masu tsokaci 6,473 (comments), da masu sake wallafawa 4,802 (reposts), da  masu yadawa 85,200 tun daga ranar 23 ga Disamba,2025.

@cmentzing ya fitar da nasa martani da cewa “Duk abin da ka ga Bill Gates na gaba-gaba labari ne mara dadi ga al’umma.”

Wani mai amfani da shafin mai suna @i_am_mstparker01, ya bayyana cewa, “Me yasa duk lokacin gwaji ake zuwa Afurka me zai hana su je Nahiyar Turai?”

Ganin irin tsokaci da mutane ke yi da mutanen da ke cikin wannan da’awa, shirin DUBAWA yaga dacewa a gudanar da bincike don tantance wannan da’awa. 

Tantancewa

Mun lura cewa akwai tsakure ne na bidiyo har guda uku da aka hade, wanda bai fice a yanko a jona ba don a isar da wani sako. Mun yanke shawarar bincikar kowane bidiyo daga cikinsu.

Mun duba asalin bidiyon mai gabatar da shirin sai muka ga bidiyon a shafin nata an wallafa a ranar 1 ga Nuwamba,2023. Wannan na nuni da cewa bidiyon haka yake kuma da’awar ta faro ne daga ita.

Hoton bidiyon Bill da yake magana kan batun yiwa yara allura an dauko shi a 2015 inda yake tattaunawa kan maganar inganci na gwajin kayan amfanin gona da aka jirkita halittarsu wato (GMOs). Yayi maganar allura ne kan abin da ya shafi abinci ba yana magana ba ne kan yadda za a yi wa yara allura ta GMOs.

Bidiyo na biyu na William Ruto ne shima an dauko shi tun can baya a ranar 30 ga Oktoba,2023 inda yake magana a kan Maisha Namba tsarin da ake tattara bayanan mutane a sa a kankanuwar na’ura a sanya jikin halittarsu karkashin tsarin da suka bayyana da zama na zamani da ake kira digital.

A bidiyon babu inda yayi magana kan Bill Gates ko kamar a da’awar cewa za a dasa wani karamin abu a cikin jikin yara jarirai.

Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ko za mu ga wani rahoto da yayi magana kan tattara bayanai a tsarin na zamani na digital. Mun gano rahoto daga 2023 a kan sabon tsarin tattara bayanan na Maisha Namba a Kenya.

Maisha Namba wata hanyar tantancewa ce da kasar Kenya ta fitar wacce ke zama ta musamman da ake ba wa yara lokacin da aka haife su, wanda kuma da ita za su ci gaba da amfani tsawon rayuwarsu. Tana kunshe ne da bayanai daban-daban kan abin da ya shafi rayuwar mutum, ana amfani da ita a matsayin shedar haihuwa ta sabbin haihuwa, lambar dan kasa don amfanar abubuwan da gwamnatin kan yi tanadi kamar a fannin ilimi (NEMIS) da inshorar lafiya (NHIF),  wanda kuma ita ke zama lambar dan kasa lokacin da yaro ya kai shekaru 18.

Babu wata sheda da ta nuna cewa karkashin wannan tsari za a sanya wata kankanuwar na’ura ko chips da za a makalawa yaran ko cewa Bill Gates ya dauki nauyi kamar yadda mai yada shirin tayi da’awar.

Haka kuma baa sami wani rahoto ba sahihi da ke nuna cewa Bill Gates ya bukaci a tattara bayanan yara kan tsarin na digital a kasar ta Kenya.

A Karshe

Da’awar cewa Bill Gates ya bukaci a tattara bayanan yara a tsarin na zamani (digital) a Kenya yaudara ce, an hada wasu bidiyo ne marasa alaka na Bill Gates da William Ruto don isar da sakon cusa kankanuwar na’ura a jikin yara  mai tattare da bayanan yaran da aka haifa tun a lokacin haihuwa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »