African LanguagesHausa

Duk abubuwan da mu ka sani dangane da tsarin albashin ‘yan sandan Najeriya bayan da aka wallafa labarin nan mai daukar hankali  a shafin X

Getting your Trinity Audio player ready...

A ‘yan shekarun da suka gabata, an yi ta tattaunawa dangane da batun albashin ‘yan sandan Najeriya, wanda ya hada da tsarin albashi mara tsoka da gidaje marsa inganci a barikokin ‘yan sandan.

Yawancin tattaunawar kan ta’allaka ne a kan ko ana biyar jami’an da ke aiki a Rundunar “Yan Sandan Najeriya (NPF) albashin da zai wadace su har su yi gudanar da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora musu alhakin yi na kariya, gano miyagun laifuka a kasar da kare rayuwa da dukiyar al’umma.

Da yawa sun danganta zarge-zargen karbar cin hanci, cuta da cin zarafin da ake yawan yi wa jami’an na NPF da karancin albashin da suke da shi.

Irin korafe-korafen da ake yi kan cin zarafi da karbar cin hanci da rashawar ne ya kai ga rikicin #EndSARS din da ya tayar da hankalin ‘yan kasa a watan Oktoban 2020 ke nan.

A wancan lokacin, matasan Najeriya da yawa suka fantsama kan tituna dan nuna adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke wa al’ummar Najeriya musamman kan wannan sashen na musamman wanda ke kula da miyagun laifukar da aka rusa yanzu, wadda aka rika kira SARS, wadda kuma ta yi kaurin suna sosai.

Zanga-zangar, wadda ke da nufin jan hankali kan bukatar gyara aikin ‘yan sanda, ya fara ne daga soshiyal mediya bayan da aka wallaga bidiyon wani matashi da aka yi zargi jami’an SARS sun kashe. Daga nan ne aka rika amfani da alamar hashtag wato # wajen raba batun har sai da ya shiga ko’ina. Sa’annan sai matasan Najeriya da dama su kuma suka fito suna bayyana albarkacin bakinsu dangane da irin abubuwan da su ma suka fuskanta daga wannan sashen ‘yan sandan na SARS.

Tun bayan zanga-zangar, an sami sauyi a yadda ake sanya ido kan ‘yan sanda inda al’ummar Najeriyar da dama ta ke so ta san yawan kudin da ake bitan ‘yan sanda a matsayin albashi na wata-wata.

Wannan batun na kula da jin dadin ‘yan sanda ya sake bulla kwanan nan sadda mai magana da yawun ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa hoton wata jami’ar ‘yan sanda wadda ya kwatanta a matsayin mataimakiyar sufeto, (DSP), David Victoria, wadda ke zaman sakatariyar sufeto Janar na ‘yan sanda.

A hoton da ya shiga ko’ina yanzu bayan da aka sa a shafin X, an ga DSP din tana rike da wayar Samsung Galaxy babba irin wanda ake kira Fold. Bayan nan kuma tana sanye da babban agogo wanda ake kyautata zaton irin mai tsadar nan ne.

Hoton ya sha kakkausar suka sosai daga ‘yan Najeriya wadanda suka ce babu yanda za’a yi a ce albashinta ne ya sayi wadannan kayayyakin, kamar yadda muka gani a nan, nan, da nan.

Wani mai amfani da shafin X @Akint0mide, wanda ya yi amfani  da hoton, ya ce, “Ma’aikaciyar gwamnati (DSP) da wayar da ya kai miliyan daya. Lol. Ire o.”

Amma da ya ke mayar da martani dangane da batun, mai magana da yawun ‘yan sandan ya kalubalanci bayanin @Akint0mide ya ce ‘yan sanda ba matalauta ba ne.

Mr Adejobi ya tambayi wanda ke sukar ko ya san abun da ya ke nufi a ce mutun ya kai mukamin DSP a ‘yan sanda. 

Sai dai shi kan shi wannan martanin na mai magana a madadin ‘yan sanda bai yi wa ‘yan Najeriya dadi ba.

Wani mai amfani da shafin na X @tataseboydej shi ma ya sa baki a batun, inda ya makala hoton da ke dauke da tsarin albashin ‘yan sanda a kowani mukami – a wani yunkuri shi ma na kalubalantar matsayar Mr Adejobi.

@tataseboydej ya ce, “ga albashin da ake bai wa ‘yan sanda a hukumance, sir. Yanzu sai ka bayyana mana, wani aiki take yi a bayan fage da zai iya ba ta damar sayen wannan wayar?”

Sai dai shi kansa wannan bayanin, ya janyo ra’ayoyi mabanbanta tsakanin masu amfani da shafin na X wadanda su ka yi zargin cewa alkaluman da aka sanya cikin hoton  da @tataseboydej ya wallafa ba daidai ba ne. 

DUBAWA ta yi kokarin tantance wannan lamarin domin yana iya yiwuwa cewa shi mai amfani da shafin na X zuwa ya yi wani shafi kawai ya dauko bayanan ba tare da ya tantance ba. 

Tsarin albashin ‘yan sanda a fayyace

Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ne ya bayar da tsarin da ake amfani da shi wajen biyan ‘yan sandan Najeriya NPF albashi. Rundunar ‘yan sandan na karkashin tsarin gudanarwa da kungiya.

NPF a bayanin da ke shafinta, ta ce tsarin rundunar na la’akari da yanayin tsarin mulkin ‘yan sanda kuma ana tafiyar da komai ne bisa mukami ko matsayin da mutun ke rike da shi.

Dan haka, ga tsarin girmar da ake bi: Sufeto-janar na ‘yan sanda, mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda, Kwamishinan “yan sanda (wanda ke kula da abubuwan da ke farywa a jiha) mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da babban(Cif) sufeton ‘yansanda. 

Saura kuma sun hada da sufeton ‘yan sanda, insfeton ‘yan sanda, sajent manjo, sajent, corporal da constable.

Wasu daga cikin mukaman an kara raba su zuwa gida biyu ko uku saboda hawa-hawa ne. Wadannan hawa-hawan ne ke bayyana mukamin da ma ingancin shi. A kan wadannan tsare-tsaren ne ake gina tsarin albashin ‘yan sandan.

Yunkurin mu na tantance gaskiya

Da farko mun yi binciken mahimman kalmomi a shafin google wanda ya nuna mana cewa yawancin shafukan Najeriya — in ban da wasu ‘yan kadan — sun yi amfani da alkaluman nan ne da wannan mutumin na shafin X ya wallafa a shafinsa ba tare da sun tantance ba, kamar yadda za ku gani a nan, nan, da  nan, da dai wasu da yawa. 

DUBAWA ta lura da cewa alkaluman sun zo daidai da wanda jaridar Premium TImes ta hada cikin wani rahoton da ta wallafa a watan Nuwamban 2020, ko da shi ke akwai wasu ‘yan banbance-banbance kalilan.

Idan ba mu manta ba, a lokacin da aka rika korafin cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa ‘yan kasa, shugaban kasa na wancan lokacin Muhammadu Buhari ya amince a kara wa ‘yan sandan albashi. 

A ganawar da ya yi da manema labarai, ministan kula da harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ta fadawa ‘yan jarida cewa majalisar zartarwar kasar ta amince da wata “alawus ta musamman” wa ‘yan sanda, wadda za’a fara ba su daga watan Janairun 2022.

Wannan a cewarsa, zai kara yawan albaashin da ake biyan ‘yan sandan da kashi 20 cikin 100.

A wancan lokacin, ‘yan sanda sabbin dauka na samun  N9,019 kowani wata sa’annan kuma  N108,233 kowace shekara, yayin da shi kuma Sufeto Janar ke samun N711,498 kowani wata, sa’annan  N8,537,976 kowace shekara, a cewar rahoton Premium Times.

Wata takarda da DUBAWA ta samu kwanan nan, ta bayyana cewa ba wani karin a zoi a gani ba ne aka samu kan albashin bayan da aka kara shi alawus din na musamman.

An sanya wa takardar suna “Sabon tsarin albashin ‘yan sanda (CONPOSS) da karin kashi 20 cikin 100 (wanda ya fara aiki daga watan Janairun 2022).”  A cewar wannan takardarm kudin sabbin ‘yan sanda ya karu zuwa  N10,114, da karin kashi 20 cikin 100 wanda ke zaman N2,022, jimilar albashin na zaman N12,137, yayin da jimilar kudin da sukan samu bayan an cire kudin fanshow kuma ke kasancewa N11,378. 

Wannan takardar ta kuma nuna cewa ‘yan sanda na samun albashin ne bisa mukamin da suke rike da shi. Alal misali, mataimakin sufeton ‘yan sanda a mataki na daya zai iya samun jimilar N259,000 bayan an cire fanshow yayin da wani DSP din wanda ke mataki na takwas shi kuma za shi gida da N301,000.

Banbancin albashin bayan kudin fanshow, abu ne da ake iya gani a duka mukaman baki daya in banda kurata, ko kuma sabbin ‘yan sandan wadanda ba su dade da kama aiki ba.

Haka nan kuma, DUBAWA ta yi magana da ‘yan sanda wadanda suka bukaci da a sakaya sunayensu, kuma su ma sun bayyana mana cewa alkaluman da mutumin na shafin X ya bayyana ba daidai ba ne, sabon tsarin albashin ‘yan sandan ya fara aiki kuma akwai wadansu kudaden da ake janyewa daga kudin da ake ba su.

“A hukumance, ‘yan sanda za su ce an kara mu ku albashi, amma bayan nan, kawai sai ka ga ana janye mu ku wadansu ‘yan kudade,” wata majiya ta bayyana.

Majiyar ta kara da cewa yayin da za’a iya samun jami’ai a mukami daya, shekarar da aka dauke su aiki na tasiri sosai a kan yawan albashin da kowa zai kai gida, abun da ke kara haske kan abun da ya sa albashin wasu kan fi na wasu duk da cewa mukami daya suke rike da shi.

Ya e: “Idan dai aikin ‘yan sanda ne, muna da sabon shiga, koforal, sa sajent da sauransu. Amma idan ya zo albashi akwai hawa-hawa. Mu biyu muna iya kasancewa konstabul amma an dauke mu a shekaru daban-daban (misali 2021, 2022). Haka nan batun ya ke wa wadanda ke rike da mukamin koforal su ma, da sajent, amma inda aka kai mukamin insfekta, akwai insfekta mai layi daya, da mai layi biyu, sa’annan da manyan insfektoci. Su kan shafe shekaru bakwai a mukamin isnfekta kafin su samun karin girma zuwa ASP 2 (mai tauraro daya) daga nan sai su yyi shekaru biyu kafin su je ASP 1 (taurari biyu) kafin DSP, taurari uku sa’annan SP.

“DSP zai iya shage kusan shekaru biyar kafin ya zama SP. Kuma wasu lokuta a kan kara mu su dubu daya kowace shekara a kan albashin. Idan har aka biya ka N70,000 bana, wata kila a kara N2,000 a badi, ko kuma wata kila idan suna so su dauki sabbin ma’aikata sai su kara muku albashi da kadan. Wata sa’a kuma ba za su kara ba sai bayan shekaru biyu zuwa uku haka kafin su kara.”

Wani dan sandan da DUBAWA ta yi magana da shi cikin sirri shi ma ya tabbatarwa DUBAWA da hakan.

Idan ba ku manta ba, tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda IGP Baba Usman ya dora alhakin jinkirin da aka samu wajen aiwatar da sabon tsarin albashin a kan rashin iya gyara manhajar bayanan da ke rajistar bayanan mutane wanda aka fi sani da IPPIS.

Bayan nan, wata takardar da ta fito daga wurin ‘yan sanda mai kwanan watan 22 ga watan Yuni, wanda jaridar Punch ta samu, ta nuna cewa mahukuntan ‘yan sandan sun ce karancin kudi ne a bangaren ‘yan sandan ya yi sanadin jinkirin.

Wani bangaren bayanin da ke dauke a cikin takardar ya ce, “Bisa bayanan da muka samu ranar 22 ga watan Yunin 2022 daga ofishin PAB da ke Abuja, akwai karancin kudi na biyan albashin ‘yan sanda, kuma idan har aka tura wadanda aka karawa girma zuwa matakin da ya kamata a sa su, hukumar ‘yan sandan ba za ta iya biyan albashi ba.”

Sai dai watanni kadan bayan nan, wata takardar ‘yan sandan ta bukka wadda ta ce sashen da ke kula da IPPIS ta “fara bayar da kudaden alawus din da aka yi bita a albashin ‘yan sanda daga watan Yulin 2022.”

Tare da bayanin cewa yayin da aka biya karin albashi na watan Yuli, sauran watannin shidan da ba’a riga an biya ba za’a biya daga baya.

Hukumar ta yi alkawarin biyan kudaden ne daga watan Agustan 2022.

To amma har yanzu ba a fayyace ya ke ko sun biya albashin da alawus din da ya kamata a ce sun biya yadda ya kamata ba.

Ranar 13 ga watan Oktoba, DUBAWA ta tuntubi sashen kula da raba arzikin kasa da kudaden gwamnati RMAFC dan samun karin bayani dangane da tsarin albashin ‘Yan sandan Najeriya. Duk da cewa hukumar ta amsa sakon imel din mu a kan kari, da cewa za su turo mana cikakken bayani daga baya, har yanzu ba su yi haka ba, kusan kwanaki fiye da 15 bayan nan.

Ranar 27 ga watan Oktoba, DUBAWA ta sake yi wa hukumar tuni. A wannan karon ma sun sake amsawa a kan kari sun ce za su rubuto mana sako da cikakken bayani amma har yanzu ba mu ji daga wajen su ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button