‘Yan kwanaki kadan bayan da DUBAWA ta tantance gaskiyar labarin da ke zargin wai shahararren dan wasan nan na Amurka mai suna Steve Harvey na Najeriya, shafin Facebook ya sauke batun da aka wallafa a shafin shi. Wannan ne ma ya sanya su kan su wadanda su ka fara wallafa labarin soke batun baki daya daga taskar ta su.
Da ma labarin na zargin wai mai watsa shirye-shiryen a talibajin da ma wasannin barkwanci ya shigo Najeriya ranar asabar domin nuna goyon bayan shi ga dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar Leba wato Mr Peter Obi.
To sai dai binciken da DUBAWA ta yi ya nuna cewa mai shekaru 65 na haihuwan bai shigo Najeriya ba kuma bai nuna wani goyon baya ga Mr. Peter Obi ba.
Kafin DUBAWA ta yi wannan binciken, wani shafin Facebook ya yi amfani da labarin wajen samun mutanen da suka yi ma’amala da shafin su fiye da 13,000.
Mun yi kokarin zuwa shafin don ganin yadda labarin ya yadu amma sai muka tarar cewa an cire labarin. Baya ga haka ko da mutun ya latsa adireshin da ke dauke da labarin ba zai tarar da komai ba amma zai mayar da mai binciken zuwa babban shafin .
Da muka yi kokarin amfani da sunan “Steve Harvey” dan ganin ko wasu ma sun dauki labarin ba mu ga komai ba dangane da ba-amurken.