African LanguagesHausaNews

Farfesa Amina Mustapha: Ta Kafa Tarihi a Matsayin Mace ta Farko wadda ta taba kasancewa Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano

Getting your Trinity Audio player ready...

Yayin da duniya ke shirin bikin Ranar Mata ta Duniya (International Women’s Day), ranar 8 ga watan Maris idan Allah ya kai mu, Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta yi nasarar kafa tarihi bayan da ta naɗa Farfesa Amina Mustapha a matsayin mace ta farko wadda za ta fara rike mukamin mataimakiyar shugaban jami’a (bangaren Bincike da Ci Gaban Ilimi) a tarihin jami’ar.

Wannan babban matsayi da ta samu na nuna bajintar mata a fagen ilimi da shugabanci, tare da kasancewa abin da zai bai wa mata masu himmar cimma manyan mukamai a harkar ilimi kwarin gwiwa.

Professor Amina Mustapha kwararriya ce a fannin Tattalin Arzikin Noma (Agricultural Economics), kuma ita ce farfesa ta farko daga masarautar Yauri a Jihar Kebbi. Ta fara karatunta a fannin Kimiyyar Noma (Agricultural Science) a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, sannan ta samu digirin digirgir a fannin Tattalin Arzikin Noma da Nazarin Kasuwaci na Kayayyakin Gona (Agricultural Marketing and Value Chain Analysis) daga Jami’ar Ibadan a shekarar 2012.

Ta fara aiki a BUK a shekarar 2002, kuma ta ci gaba da taka rawar gani har ta zama farfesa a 2018. Kafin naɗinta a matsayin Mataimakiyar Shugaban Jami’a mai kula da Bincike da Ci Gaban Ilimi, ta rike mukamin Mataimakiyar Darakta a Sashen Bayar da Ilimi da Wallafe-wallafe a Cibiyar Nazarin Ayyukan Gona a Kan tsandauri BUK (Centre for Dryland Agriculture – CDA), inda ta taka rawar gani wajen inganta bincike da ci gaban noma mai dorewa. Baya ga hazakarta a fannin bincike da koyarwa, shigowarta cikin shugabancin jami’a wata alama ce ta jajircewar mata wajen cimma matsayi mai daraja.

Wannan naɗi ya zama wani mataki na bunkasa shigar da mata a harkokin shugabanci a jami’o’in Najeriya. A yayin bikin naɗin nata, Shugaban Jami’a, Professor Sagir Adamu Abbas, ya yaba da irin gagarumin gudunmawar da take bayarwa, tare da nuna kyakkyawan fata na cewa za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa bincike da ci gaban jami’ar.

Yayin da ake ƙara ƙarfafa daidaito tsakanin maza da mata a ilimi da shugabanci, tarihin Professor Amina Mustapha ya zama abin alfahari da kwarin gwiwa ga mata masu neman cimma gagarumin matsayi a harkokin ilimi. Naɗinta ba wai nasara ba ce kawai a gare ta, har ma wata babbar nasara ce ga dukkan mata masu fafutukar zama jagorori a manyan makarantu da sauran fannoni na rayuwa a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »