African LanguagesHausa

Gaskiya ne, Idan mutun ya latsa wadannan alamu da lambobin *#62# a wayar hannu, ya na iya ganin lambobin wayoyin da aka karkatar, wadanda wayoyinsu ba su shiga ko sun bugo

Zargi: Wani sakon da ake yadawa a WhatsApp ya bayyana wadansu lambobin da za su iya nunawa duk mai waya ko ana karkata wayoyin da ke shigowa da ma yadda za’a iya dakatar da hakan daga faruwa.

Gaskiya ne, Idan mutun ya latsa wadannan alamu da lambobin *#62# a wayar hannu, ya na iya ganin lambobin wayoyin da aka karkatar, wadanda wayoyinsu ba su shiga ko sun bugo

Wannan gaskiya ne, bincikenmu ya tabbatar ma na cewa duk abubuwan da aka ce lambobin da alamun na yi a cikin sakon wanda aka yi ta yadawa, su na yi

Cikakken bayani

Ranar 20 ga watan Satumba 2022 aka fara yada wani sakon da ke gargadin cewa masu zamba na karkatar da wayoyin mutane zuwa wayoyin wadansu wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba. Sakon ya bayar da wadansu lambobi da alamu wadanda ya ce idan aka yi amfani da su ana iya gane ko hakan ya shafi waya kuma ana iya dakatar da shi ta yin amfani da wadannan lambobi da akamu.

Sakon ya ce idan aka latsa *#62# za’a gane ko an karkatar da wayoyin da ke shigowa waya zuwa wata lamba ta daban idan kuma aka ga hakan ya faru sai a latsa ##002# wannan zai soke duk wata makarkashiya da aka yi na karkatar da wayoyin.

Wani mai amfani da WhatsApp ne ya raba sakon yana bayanin cewa akwai hannun manyan kamfanonin wayar Najeriya irin su MTN, Glo da Airtel.

Mutane da dama suka turo wannan sakon suna bukatar DUBAWA ta tantance gaskiyar batun shi ya sa mu ka gudanar da binciken.

Tantancewa

Binciken da mu ka yi na mahimman kalmomi ya kai mu ga shafin Calcare wadanda su ka yi bayani dalla-dalla dangane da yadda za’a iya gyara wayar da aka karkatar da wayoyinta zuwa wata waya ta daban ta yadda mai shi ba zai iya amsa wayoyinsa ba. Shafin ya kuma kara da bayanin yadda duk mai waya zai gane idan wayarsa na fuskantar irin wannan matsalar.

Mun tuntubi kamfanonin da aka ambata wato MTN Glo da airtel ta hanyar email da kuma sako na kai tsaye a shafin tiwita. Kamfanin Glo ne kadai ya amsa mu.

A amsar da Glo ya ba mu a shafin tiwita, ya ce “gaskiya ne ana iya amfani da *#62# a duba ko an karkatar da wayoyin da ke shiga lambar, abin da ake kira call forwarding ko call divert da turanci. Haka nan kuma da zarar aka yi amfani da ##002# ana iya maido ta yadda ta ke,” a cewar sakon da suka rubuto.

Mai bincikenmu wadda lambar wayarta airtel ce, ta yi amfani da wadannnan lambobi dan gani a zahiri ko suna aikin da aka ce suna yi. Da ta sanya lambobi, ta gano cewa akwai wadansu daga cikin wayoyin da aka yo mata da ba ta amsa ba saboda an karkatar mata da su zuwa wata wayar. Dan haka sai ta yi amfani da lambobin na biyu wadanda aka ce suna warware matsalar. Bayan haka sai ta sake komawa ta sanya lambobin farko ta ga ko abin ya yi aiki inda ta ga cewa da gaske lambobin sun yi aiki yadda aka ce suna yi. 

Kwararre kan fasaha kuma shugaban kamfaniun Reni, Ore Afolayan shi ma ya bayar da tabbacin cewa lambobin na aiki kuma ba za su jefa mutun hannun mazambata ba. 

“Lallai ana iya amfani da su ba su da wata matsala,” ya ce.

A Karshe 

Bincikenmu ya nuna cewa wadannan lambobi da alamu suna aiki kamar yadda aka ce suna yi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »