Albashin ma’aikatan gwamnati a Laberiya ya karu zuwa kashi 70 cikin 100 na yawan kudin da aka tanadar dan batarwa a kasa wanda ya kai jimilan dala milliyan 320 a karkashin Johnson Sirleaf
Jimilar kudin da ake kashewa kan albashin ma’aikata a gwamnatin tsohuwar shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ya kama kashi 59 cikin 100 ne ba kashi 70 ba bayana daga kasafin kudin shekarun 2018 and 2019 da ma wani rahoton da aka samu daga USAID duk sun karyata wannan zargin
Cikakken bayani
Wani sanannen mai goyon bayan gwamnatin Weah a Laberiya na ikirarin cewa tsohuwar gwamnatin Ellen Johnson Sirleaf ta bar su da dokar biyan albashin da ba zai iya dorewa ba.
A cewar Samuel Jackson, masanin tattalin arziki, dokar albashin wanda aka amince da ita a karkashin tsohwar gwamnati ta kai kashi 70 cikin 100 na adadin kudin da aka ware dan batarwar kasa baki daya, abin da ya kai dala miliyan 320. Ya ce wannan ne ya hana gwamnatin samun kudin gudanar da manyan ayyukan da za su kawo wa kasa jari abin da ke da mahimmanci wajen sake gina Laberiya bayan da ta yi fama da yaki.
Jackson ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke mahawara da Amos Twek Sakatare Janar na jam’iyyar Unity wadda ta sauka daga mulki kafin zuwan gwamnatin George Weah.
An gudanar da wannan mahawarar ne a gidan rediyon Okay FM 99.5 inda aka kuma watsa shi kai tsaye a shafin Facebook ranar 19 ga watan Satumban 2022
Ana iya samun zargin Jackson bayan sa’o’i biyu da mintuna biyar na mahawarar mai tsawon sa’o’i uku.
Bisa bayanin da Jackson ya bayar, sakamakon yawan kudi wanda aka gada daga gwamnatin da ta kasance a karkashin jagorancin jam’iyyar CDC, Asusun Bayar Da Lamuni na Duniya wato IMF ta bukaci gwamnatin Weah da ta rage yawan albashin da dokar ta tanadar, inda ya ce wannan ne ma ya taimakawa gwamnatin wajen daidaita shirye-shiryenta a shekaru biyun ta na farko da kama aiki.
Wannan matakin da gwamnatin ta dauke ne ya janyo zanga-zanga tsakanin ma’aikatan gwmanati a kasar.
Tantancewa
Asusun ba da lamuni na duniya na kwatanta dokar albashi a matsayin kudi ko wani abun alheri da gwamnati za ta bai wa kowani ma’aikaci bayan ya kammala aikin da ta sa shi. Wannan ya hada da albashi, kudin alawus, insora, fansho da dai sauran kudaden da gwamnati ke taimakawa ma’aikata su tara. (IMF 2014b)
A bayanain da ya yi cikin kasidar da ya wallafa, mai taken “Tasirin kudin da gwamnati ke kashewa kan albashi a kan kasafin kudi, IMF ya ce idan har albashin na da yawa musamman a kasashe masu tasowa, za’a sami rashin daidaito a kasafin kudin kasa baki daya.
Bisa la’akari da gaka da ma yadda batun ya janyo muhawara a tsakanin al’umma, DUBAWA ta yanke shawarar gudanar da bincike dan gano gaskiyar furucin da ya yi.
Lokacin binciken, DUBAWA ta gaone cewa kasafin kudin na karshe wanda aka amince da shi a karkashin gwmanatin Johnson Sirleaf an ganatar da shi ne 2017/18 kuma ya sanya yawan albashin ma’aikatan gwamnati a kan kashi 59 cikin 100 abin da ke zaman dala miliyan 298.020,404. Ana iya samun wannan a shafi xiii (3) na kasafin kudin 2017/18 na Laberiya.
Bacin haka a shafi na biyu na rahoton USAID: Nazarin hanyoyin yin kwaskwarima a kudi da albashi a gwamnatin Laberiya shi ma ya bayar da tabbacin cewa albashi na kaman kashi 57 cikin 100 na kudin da kasar ta batar tsakanin 2017-18. Ana iya samun shi a karkashin shafin da aka yi wa taken “Fiscal Conditions”
A Karshe
Sakamakon binciken da aka yi, DUBAWA na iya tabbatar da cewa, bisa la’akari da bayanai da ma takardun da ta samu, kudin albashin ma’aikatan gwamnati a karkashin gwamnatin Sirleaf tsakanin 2017 da 2018 bai kai kashi 70 cikin 100 na kudaden batarwar gwamnati ba. Kudin ya tsaya ne a kan kashi 59 cikin 100.