African LanguagesHausa

Gaskiya ne! Mutumin da ke cin abinci da kyau na iya samun olsa ko kuma gyambon ciki

Zargi: Masu cin abinci sosai ba za su iya kamuwa da olsa (Ulcer)  ba

Gaskiya ne! Mutumin da ke cin abinci da kyau na iya samun olsa ko kuma gyambon ciki

Duk da cewa rashin cin abinci na iya ta’azara cutar gyambon ciki, ba shi ne ke janyo cutar ba. Domin mutun na iya cin abinci sosai amma kuma yana iya kamuwa da cutar duk da haka.

Cikakken bayani

Na wani tsawon lokaci yanzu, mutane da yawa na ganin kamar idan dai mutun na cin abinci da kyau ba zai taba kamuwa da cutar ulsar ba wato ciwo ko kuma mikin da kan bayyana a baki ko kuma cikin hanjin cikin dan adam, inda da yawa ke ganin talaka ne kadai wanda ba safai ya ke samun abincin ci ba, ya ke kamuwa da cutar.

Kwanan nan, wata abokiyar mai rubuta wannan labarin ta bayyana mata yadda aka gano cewa tana dauke da cutar ulsa amma ya kasance mata abin mamaki tunda a ganin ta tana cin abinci sosai kuma cuta ce da ke kama wadanda ba su cin abinci sosai. Saboda haka idan har Ulsar ta kan kama masu cin abinci sosai me ke janyo ta?

Ulsa dai kamar marurai ne wadanda ba su warkewa da sauri, kuma suna iya bayyana a gabobin jiki daban-daban, misali akwa na kafa, na baki, na cikin ciki da na al’aura.

Olsar Ciki

Ulsar da akan gani ciki suna fitowa ne a jikin hanji wanda ya sa ake kiransu Ulsar ciki. Irin wannan ne aka fi sani amma kuma ba’a ganin ta da ido tunda tana cikin ciki. Ga mutane da yawa ciwon ciki ne alama ta farko.

Akwai iri uku, akwai wada ke fitowa a tumbin ciki, sai kuma wanda ke fitowa a hanyar abincin da ke hada makogwaro da tumbin ciki wanda ake kira esophageal ulcers a turance, akwai kuma duodenal wanda shi kuma ya kam bulla ne a barin farko na karamin hanjin dan adam.

Wata sa’a mutun na iya samun iri biyu a lokaci guda misali na cikin tumbi da kuma wanda ke gabar karamin hanjin, wanda ake kira gastroduodenal a turance.

Abubuwan da ke Haddassa Cutar

Wata kwayar cuta mai suna H.Pylori na iya haddasa cutar, da kuma wadansu magunguna sai kuma wani yanayi da dalilai.

H.Pylori

Wannan kwayar cutar ce ta fi janyo cutar ulsa saboda ya kan shafi gamsan da ke kare tumbi da hanji, idan ya yi haka sai ya baiwa wasu sinadaran cikin da ke da kaifi sosai su raunata jikin hanjin da cikin.

Duk da cewa ba’a kai ga gano yadda wannan kwayar cutar ke yaduwa ba, masu bincike na ganin cewa ta na yawan bin gurbatattun abinci, ruwa da kuma kayayyakin cin abincin kamar su cokali, kwanoni da sauransu. Ana kuma iya samun shi cikin miyau.

Magunguna

Yawan amfani da magungunan da akan saya a kemis yawanci ba tare da izinin likita ba musamman masu rage zafi irin na ciwon kai kamar aspirin, ibuprofen, naproxen da sauran magungunan da kan rage kumburi na iya janyo ulsa

Akwai wadansu abubuwan kuma da kan kasance dalilai masu hadarin gaske musamman ga wanda ke dauke da kwayar cutar ta H.Pylori, wadannan sun hada da shan giya, damuwar da ya shafi rashin kwanciyar hankali, shan taba, rashin shawo kan damuwa, da cin abinci mai barkono.

A Kula: Wadannan abubuwan da ke da hadari, ba su ne ke janyo ulsar ba sai dai suna hana ta warkewa da wuri.

Yadda ake gano cutar a jikin dan adam

Akan yi amfani da hanyoyi biyu ne wajen gano cutar. Na farko daukar hoton cikin da karamar kyamerar da ake sanyawa a cikin a yi yawo da shi dan daukar hotunan gabobin cikin a abin da ake kira endoscopy a turance. Na biyun ma daukar hoto ne amma ba’a sa kyamera a ciki a kan dauki hotunan gabobin cikin baki daya daga waje a abin da ake kira X-RAY. Shi kuma salon ana kiran shi GI Series.

Alamun Olsa

Ba ko da yaushe ne alamun cutar ke bayyana ba, amma idan sun yi, a kan sami ciwon ciki mai tsanani, kumburin ciki da yawan gyatsa, rashin jurewa ire-iren abinci masu mai, yawan jin amai da kwannafi.

Idan cutar ta yi tsanani sosai a kan sami yawan amai ko kuma aman jini, numfashi sama-sama, jin suma, zubewa ba tare da wani dalili mai kwari ba, da rashin jin cin abinci.

Yana da mahimmanci a je a ga likita a duk sadda aka sami irin wadannan alamun musamman idan magungunan da akan yi amfani da su wajen samun saukin wasu daga cikin alamun ba su yi aiki ba.

Maganin Olsa

Wata sa’a cutar ta kan bace da kan ta, wata sa’a kuma tana bukatar magani idan ba haka ba tana iya kai wa wani hali na hau’ila’i

Idan har ba’a yi maganin ta ba, tana iya janyo zub da jini a ciki, tana yin rami a bangon cikin wanda zai iya hana abinci wucewa ko kuma ma ta toshe hanyar abincin baki daya, tana kuma iya kawo cutar daji/kansa.

A Karshe

Duk da cewa rashin cin abinci na iya ta’azzara cutar olsa, ba shi ne dalilin kamuwa da cutar bam kuma mutun na iya kasancewa mai cin abinci sosai amma duk da haka zai kamu da cutar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button