African LanguagesHausa

Hattara, Ba sanyi ne ke janyo ciwon huhu/Namoniya ba

Zargi: Sanyi ne ke janyo ciwon huhu ko kuma Namoniya

Hattara, Ba sanyi ne ke janyo ciwon huhu/Namoniya ba

Bincikenmu ya nuna mana cewa yanayi mai sanyi baya janyo namoniya sai dai kwayoyin cutar da ke sanadin shi sun fi samun karfin aiki lokacin sanyi.

Cikakken bayani

A watan Disembar 2021, na je asibiti da ‘ya ta aka ce tana da namoniya, abin da ya fara zuwa mun rai shi ne “sanyi”

Lokacin da muke yara na dan ji batutuwa kadan dangane da ciwon huhun kuma a duk wadannan lokutan an danganta shi da sanyi shi sai ya zo mun rai.

“Amma na kare ta daga sanyi sosai yaya aka yi haka?” wannan na daya daga cikin tambayoyin da suka rika zuwa mun a rai lokacin da na sami wannan bayani sai na tambayi likitan na ce na kara diya ta daga sanyi sosai yaya aka yi ta kamu da irin wannan cuta? Likitan sai ya kwashe da dariya ya ce ba sanyi ne ke janyo ciwon huhu ba sai dai yanayin sanyi ya kan kara assasa cutar a muhalli irin namu. Duk da cewa wannan amsar ya dan rage yawan laifin da na rika dorawa kai na ya kara yawan tambayoyin da suka rika zuwa mun kamar “me ke janyo ciwon huhun? Kuma yaya ake kare kai daga kamuwa da ita? Yaya ake gano ta yaya kuma ake warkewa?

Wannan bayanain zai amsa wadannan tambayoyin da ma karin wasu:

Namoniya/Ciwon Huhu ma’ana da ire-iren shi

Kwayoyin cuta ne ke janyo ciwon huhu, wata sa’a su kan makale a huhu daya ko kuma duka biyun.

Wannan kwayar cutar kan janyo kumburi a hanyoyin da iska ke shiga da fita a cikin huhun (Ana kiran hanyoyin iskar alveoli da turanci). Kumburin kan zo da ruwa saboda tamkar maruru ne ke fitowa a wurin. Wannan ruwan ne kuma ke sa numfashi wahala.

Akwai abubuwa sama da 30 da ke janyo ciwon huhu amma an sanya su cikin rukunnai hudu, wadanda su ka hada da kwayoyin cutan da aka fi sane da bacteria, (wadanda ake iya kashe su da magunguna masu karfi wadanda ake kira anti-biotics) da na virus (Wadanda ba su jin magani) da mycoplasma (kwayoyin cutar da ke bukatar jikin mutun ko wani abu mai rai su rayu) sai kuma sauran cututtukan na huhu.

Ciwon huhun da ke da nasaba da Bacteria

Irin wannan ya kan afku ne a sanadiyyar shigar kwayar cuta cikin jikin mutun. Akwai dalilai da dama wadanda ke janyo hakan kuma sun hada da rashin cin abinci mai inganci da gina jiki, wasu lokuta kuma tsufa, akwai kuma garkuwar jikin da ya riga ya raunata da ma kasancewar wadansu cututtuka a cikin jiki. Wadannan ne ketaimakawa kwayar cutar ta shiga cikin huhu.

Irin wannan ciwon huhun ba ya la’akari da shekaru, ba babba ba yaro, kowa na iya kamawa amma wadanda ke yawan shan giya, ko sigari ko kuma suna fama da wata cutar da ta shafi kwakwalwa, ko wadanda ba su dade da yin tiyata ba da ma wadanda ke da cutar da ta shafe numfashi ko kuma wadanda garkuwar jikinsu ta riga ta yi rauni sun fi fiskantar hadarin kamuwa da cutar.

Ciwon huhun da ke afkuwa a dalilin kwayoyin cutar da aka fi sani da virus da turanci

Kwayoyin cuta masu nau’in virus din da yawa ne ke janyo cutar a ciki har da wanda ke janyo mura (wato flu ko kuma influenza da turanci) hasali ma kwayar cutar ce ke sanadiyyar kashi daya cikin uku na ciwon huhun da ake samu.

Bacin cewa yawancinsu na iya warkewa cikin ‘yan makonni ba tare da wata matsala ba, akwai wadanda ke da babban barazana ga rayuwar dan adam

Ana iya samun nau’o’i biyu na cutar wato mai nasaba da bacteria da mai virus din duk a lokaci guda.

Ciwon huhu na Mycoplasma 

Wannan nau’in ya banbanta da wadanda muka bayyana da farko, domin yadda ya kan bayyana daban ne kuma alamun da ke sa ana gane shi  ma daban ne. Wata kyawar cuta ce mai suna alamun Mycoplasma pneumoniae ke janyowa. Wannan ma ya kan shafi kowa, ba babba ba yaro. 

Sauran nau’o’in cutar wadanda ba’a sani sosai ba ana iya samu daga wadansu cututtukan 

Alamun ciwon huhu

Alamun sun banbanta domin ya daganci nau’in cutar da mutun ya kama da ma irin kwayar cutar da ta yi sanadin ciwon. Alamun wanda ke da nasaba da bacteria sun hada da bayyanar launin shudi ko ruwan bula a kunbunan hannu da labba, rudewa musamman a tsofaffi, tarin da ke fitar da majina mai launin ruwan kwai ko ruwan ganye, zazzabi, zufa da kin abinci, rashin kuzari da gajiya, numfashi sama-sama da kuma zafi a kirji wanda kan karu a duk sadda aka ja numfashi ko kuma aka yi tari, sai kuma daukewar numfashi a duk sadda aka yi kokarin yin wani abu. 

A wadanda ke dauke da nau’in virus, alamun farko kan kasance daidai da wadanda aka bayyana da farko sai dai wata kila ana iya samun ciwon kai, daukewar numfashi, zafin jiki, kasala da kuma tari. 

Alamun Mycoplasma kuma sun banbanta tunda yawanci dai tari ne mai tsanani wanda ke zuwa da majina.  

Yaya ake gane ciwon huhu? 

Tarihin lafiyar mutun wanda ya hada da irin aikin/tiyatar da aka yi ba da dadewa ba, mura, ko tafiyar da ta kai mara lafiyar wuararen da ke da cututtukan da ke da hadari, da ma nisan ciwon a jiki, na daga cikin irin abubuwan da ake la’akari da su wajen gane ko mara lafiya na dauke da ciwon huhu.

Baya ga haka akan yi wasu ‘yan gwaje-gwaje dan tabbatar da cutar kamar daukan hoton kirjin mara lafiyar dan ganin yanayin da huhun ke ciki, gwajin jini da miyau da yawan iskar da ke cikin jini da ma ruwan da ya taru a cikin huhun.

A’a! Ciwon huhu zai iya shafar kowa daga yaro har zuwa babba amma akwai wadanda suka fi fiskantar hatsarin kamuwa da shi. Rukunan irin wadannan mutanen sun hada da manyan masu shekaru 65 da fiye na haihuwa, yara wadanda ke kasa da shekaru biyu na haihuwa, wadanda ke dauke da wadansu cututtuka da kuma wadanda ke shan taba sigari. 

Shin Ciwon Huhun Yara Kadai Ya Ke Shafa?

Ra’ayin Kwararru

Babban likita kuma shugaban sashen yara a asibitin Garki da ke Abuja, Dr. Kayode Alabi ya ce ba sanyi ba ne ke janyo ciwon huhu

A cewar Dr. Alabi kwayoyin cuta ne ke janyo ciwon.

“Ba sanyi ne ke janyo ciwon huhu ba, na san wadansu za su ce shi ne makasudin cutar amma ba haka ba ne.”

Dangantakar da sanyi ke da shi da ciwon huhu shi ne kwayoyin cutar da ke janyo ciwon sun fi samun walwala a lokacin sanyi dan haka sai su kara asassa tari, majina da atishawa.”

Dokta Jeremiah Agim,  likitan mata kuma babban likita a National Hospital Abuja ya ce ya yarda da bayanin Dr. Alabi. Ya bayyana cewa ciwon huhu kwayar cuta ce da ke shiga ta yi lahani a huhu.

“Kwayoyin cuta ne ke janyo ciwon huhu. Wadanda ke fiskantar hatsarin kamuwa da cutar sun hada da wadanda ke dauke da cututtukan da suka riga suka rage karfin garkuwar jikinsu ta yadda ba kowane kwayar cutar ne jikinsu zai iya yaka ba ( kamar su HIV, daji, dashen gabobi, masu shan magunguna masu karfi da kuma ciwon suga) da wadanda suka manyanta da kuma wadanda ba su riga sun gama kwari ko girma ba.” Ya ce. 

A Karshe

Bincikenmu da kwararrun da muka tattauna da su, sun nuna cewa a kan kamu da ciwon huhu daga kwayoyin cuta ne wadanda suka fi aiki a lokacin sanyi saboda a lokacin ne suka fi samun walwalar yin lahani ga jikin dan adam.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »