African LanguagesHausaMainstream

Gizo-Gizon da ake kira Cyclocosmia a turance ba shi da lahani ga dan adam kamar yadda ake zargi

Zargi: Wani mai amfani da Facebook na zargin wai gizo-gizon Cycloscomia na da dafi kuma yana iya hallaka dan adam cikin minti biyar da zarar ya yarbe shi da dafin

Gizo-Gizon da ake kira Cyclocosmia a turance ba shi da lahani ga dan adam kamar yadda ake zargi

Ainihin wanda ya dauki hoton a shekarar 2020 ya fito da kansa ya karyata zargin cewa gizo-gizon na da hadarin gaske ga dan adam, kuma ba safai ake ma ganin irin shi a Najeriya ba.

Cikakken labari

Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya na da kwari da dabbobi masu dafin gaske. Bisa bayanann wani rahoton da jaridar Premium Times ta yi a shekarar 2017, ‘yan Najeriya 250 suka hallaka a sanadiyyar sarar miciji cikin makonni uku kacal.

A shekarar 2021, jaridar ta Premium Times ta sake yin wani rahoton da ya ce mutane 2,000 a Najeriya ke mutuwa ta daga sarar miciji kowace shekara abin da ta danganta da furucin mataimakin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora.

Cutar Malariya ma ta kasance matsala a Afirka inda a shekarar 2021 kawai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutane 600,000 sun mutu bayan da suka kamu da masassarar, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito. Sakamakon irin wadannan hadurran, ‘yan Najeriya kan mayar da hankali kwarai kan abubuwan da ke kewaye da su a muhallinsu.

A yanzu haka gizo-gizo ne abin da ke damun masu amfani da shafukan sada zumunta na soshiyal mediya kamar yadda aka gani a shafin wani mai suna Lawrence Ukwu mai amfani da Facebook wanda ya wallafa wani tsokaci da ke gargadin masu zuwa bakin ruwa da su guji wani gizo-gizo mai dafi wanda zai iya hallaka mutun cikin minti biyar. Marubucin ya hada tsokacin shi da hoto.

Ya ce: “Ga wadanda ke son zuwa bakin ruwa, ku yi hankali da wannan (yana nufin gizo-gizon da ke cikin hoton) . Ka da ku yi kokarin dauka kuna tunanin wani abun wasa ne. Gizo-gizo ne mai dafin gaske. Idan har ya harbe ka cikin minti 5 kana iya hallaka,” a cewar mai amfani da shafin na Facebook.

Daga cikin wadanda suka yi sharhi a karkashin tsokacin,  Komolafe Sunday ya yi godiya ne da samun bayanin a yayin da wani Kyaptin Johnerro ya nuna rashin yardar sa da tambayar cewa, “yaya gaskiyar wannan batun?”

Irin wadannan zarge-zargen na iya tsoratar da jama’a musamman a irin yankunan da ake samun irin wannan gizo-gizon dan haka ne DUBAWA ke so ta tantance gaskiyar wannan zargi. 

Tantancewa

DUBAWA ta fara da binciken hoton gizo-gizon da aka yi amfani da shi a cikin shafin bincike na google. Sakamakon binciken da aka samu daga shafin tantance kwari  ya nuna cewa ana kiran gizo-gizon cork-lid trapdoor da turanci, abin da ke nufin kyauren da ke kama da marfin kwalbar inabi. 

Shafin tantance kwarin ya nuna cewa ana iya samun gizo-gizon a a kasashen Amurka, Mexico da Canada. Wannan kan shi ya nuna cewa ba safai ne ake samun shi a Najeriya ba abin da saba da zargin marubucin wanda ke gargadin masu zuwa bakin teku. 

Baya ga haka wani sakon tiwita wanda ainihin mutumin da ya dauki hoton gizo-gizon, Nick Bay (@singaporemacro) ya dauka a shekarar 2020 shi ma ya bayyan hakan

“Wannan gizo-gizon cyclocosmia ne wanda dangin gizo-gizon da ake kira cork-lid trapdoor ne domin yadda cikin shi ke daga bayan shi kamar zumbutu,” ya rubuta a tiwita

The photographer did not mention whether or not the venom of the spider is poisonous to humans as alleged by the claimant. He also never mentions that it can kill anyone within five minutes. In Fact, he debunked the claim, stating clearly that the spider is NOT dangerous to humans.

“Gizo-gizo ne da ba ya komai kuma guban da ya ke da shi ba ya wa dan adam komai,” ya fayyace.

DUBAWA ta kuma gano wata hira da masu binciken gaskiyar Check Your Fact su ka yi da wani kwararre kan gizo-gizo mai suna  Sebastian Echeverri dan sanin ko abin da mai daukar hoton ya fada gaskiya ne inda kwararren ya tabbatar da cewa: “Guban ba ya wa dan adam komai tunda ba su da bukatar cin dan adam.” 

Mun kara da gudanar da binciken mahimman kalmomi dan ganin ko akwai gizo-gizon da ke kashe dan adam amma bincikenmu bai gano komai ba.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna cewa gizo-gizo ba shi da wani lahani. Wanda ya dauki hoton gizo-gizon da aka yi amfani da shi wajen yin sharhin, kwararre kan gizo-gizo da binciken da mu ka yi da kan mu duk sun bayyana mana cewa dafin gizo-gizo ba ya kashe dan adam.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button