Zargi: Wani mai amfani da Facebook na zargin wai shahararren dan wasan nan mai fina-finai a Hollywood Tom Hanks ya goyi bayan takarar Peter Obi
Babu wani bayanin da ya nuna cewa Tom Hanks ya goyi bayan takarar Peter Obi ko ma ya taba ambatar wani abu da ya danganci takarar bare Peter Obin kansa.
Cikakken labari
Samun goyon bayan ‘yan siyasa, malaman addini da ma sauran masu ruwa da tsaki kan kasance babban alfanu ga ‘yan siyasa musamman saboda yadda sauran magoya bayan su za su rika takama da shi.
Ba da dadewan nan ba wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa hoton wani shafin da ya dauka yana zargin wai shahararren dan wasan Hollywood, Thomas Jeffery Hanks, wanda aka fi sani da Tom Hanks ya ce yana goyon bayan takarar Peter Obi, abin da ya dauki hankali sosai har aka yi ta yadawa.
“Idan da Peter Obi Ba-Amurke ne ko da ma bakin fatan Amurkan ne da an ba shi damar kasancewa shugaban kasa ba tare da an yi zabe ba,” wani bangarin labarin ya bayyana.
Ganin yadda wani zargin ya bi ko’ina ne mu ke so mu fayyace gaskiyar.
Tantancewa
Domin gano ainihin labarin da ya yi wannan batun wanda mu ke kyautata zaton ya yi mafari ne daga Facebook, mun fara da binciken mahimman kalmomi wanda ya kai mu ga labaran da aka wallafa a shafukan Best News Network, Readitt da ma wasu shafukan na Facebook wadanda duk suka danganta labarin da wani mai suna Philip Ojealao.
Daga nan DUBAWA sai ta karkata binciken zuwa gano irin labaran da Philip Ojealao ya wallafa a shafin Facebook. A nan ne ta gano wannan labarin wanda ya wallafa ranar Lahadi 17 ga watan Yulin 2022.
BInciken sai ya koma kan shafukan Tom Hanks, inda DUBAWA ta duba shafukan shi na Instagram da Tiwita. A shafin shi na Instagram (@tomhanks) babu wani bayani dangane da Peter Obi. A shafin Tiwita kuma mun lura cewa rabon da ya wallafa wani labari tun watan Mayun 2022. Binciken da muka yi a google shi kuma ya nuna mana cewa bai taba yin wani furucin da ya danganci Peter Obi ba.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa Tom Hanks bai wallafa wani abu makamancin wannan a shafin ba kuma bai fitar da wata sanarwar da ke da alaka da wannan batun ba dan haka wannan labarin karya ne.