Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Omoyele Sowore, dan fafutuka a Najeriya ya je taro a Amurka inda ya tada hargitsi (disrupt a town hall meeting) a taron da ke zama na magoya bayan gwamnati inda ya nuna adawa da kisan masu zanga-zanga a Najeriya.

Hukunci: Yaudara ce! Ko da yake Mista Sowere na nuna fishinsa a lokutan tarukan ‘yan Najeriya a Amurka, bidiyon da ake nunawa an dora shi a intanet shekaru 12 da suka gabata ba shi da wata alaka da zanga-zangar tsadar rayuwar ta #EndBadGovernance.
Cikakken Sako
Zanga-zangar Tsadar Rayuwa #EndBadGovernance protest, da aka tsara kawo karshenta a 10.08 ta tada kura a sassa daban-daban na Najeriya, Zanga-zangar da ta samo asali saboda tsadar rayuwa a fadin kasar ta samu martani kala-kala.
Shugaba Bola Tinubu yayi wa ‘yan Najeriya bayani a baya-bayan nan, inda ya nemi da su dakatar da zanga-zangar da ta dauki lokaci ana yinta. Ya ba su tabbaci cewa yana aiki tukuru wajen ganin an shawo kan matsalolin tattalin arziki da ya addabi kasar.
Har ila yau gwamnoni a jihohin kasar sun yi kira ga al’ummominsu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum inda suka yi masu alkawari na samar da shugabanci nagari.
Mista Sowore ya kasance daya daga cikin manyan muryoyi da aka rika saurara wadanda suke goyon bayan zanga-zangar inda ma ya sha alwashi (vowed) ba gudu ba ja da baya har sai ranar 10 ga watan na Agusta a zanga-zangar da aka sa gaba.
A ranar 6 ga watan na Agusta an nuna wani hoton bidiyo yadda Mista Sowore da wasu mutane da dama suka tada hargitsi a yayin wani taro a Amurka.
A bidiyon an nuna yadda Mista Sowore ke cewa an kashe mutane 20 yayin gudanar da zanga-zangar lumana a Najeriya makon jiya.’ Ya kalubalanci wadanda suke halartar taron a Amurka “kasar kare hakki.”
Bayyana cewa an kashe masu zanga-zangar lumanar a ‘makon jiya’ ba zai rasa nasaba ba da ganin rahotanni wadanda ke cewa an kashe mutane da dama a jihohin Najeriya tun bayan da aka shiga zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar ta #Endbadgovernance protest kwanaki kadan bayan fara zanga-zangar.
Ko da yake wannan bidiyo tsoho ne, ana kafa hujja da shi duba da yadda ake ta samun rahotannin kafafan yada labarai wadanda ke cewa an kashe mutane da dama a yayin zanga-zangar lumanar ta #EndBadGovernance protests.
Wannan ya sanya wasu ‘yan Najeriyar suka rika sake yada wannan bidiyo bisa zaton sabo ne.Kamar yadda aka gani anan here da nan here, Ganin yadda bidiyon ya yadu hakan ya sanya DUBAWA gudanar da bincike a kansa.
Tantancewa
DUBAWA bayan duba na tsanaki kan bidiyon ya gano cewa bidiyon an masa gyare-gyare ne ta yadda za a ga kamar sabo ne. Bincike ya gano cewa ba sabo ba ne an yi shi tun a shekarar 2012.
A shekarar 2012 Mista Sowore da wasu magoya bayansa a lokacin gangamin #OccupyNigeria sun tada hargitsi (disrupted) a otel din Grand Hyatt hotel a New York, taron da ministar harkokin wajen Najeriya Viola Onwuliri, ke hakarta.
Ministar ta hada taron ne a kokarin yin bayani kan shirin cire tallafin manfetir inda ana tsaka da bayani sai Sowere da magoya bayansa suka tada hargitsi a wajen taron tare da neman gwamnatin Najeriya ta dena kisan masu zanga-zangar lumana ba gaira.
Karshe
Mista Sowore bai tada hargitsi ba a Amurka saboda kiran a dena kisan masu zanga-zanga a Najeriya ana tsaka da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance protests. Bidiyon da ke yawo a intanet tsohon bidiyo ne da aka yi shi a 2012.