Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani hoto da aka kirkira ya nuna yadda tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello yayi shigar mata ya bazu a shafin WhatsApp. Masu amfani da wannan kafa na zargin tsohon gwamnan da yunkurin tserewa kamun Hukumar da ke Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC
Hukunci: YAUDARA CE. Bincike ya gano cewa hoton tsohon gwamnan Yahaya Bello da aka dora shi da shigar mata asalin hoton na matar Ken Nnamani tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya ce da ta rasu
Cikakken Sakon
Hukumar da ke Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC na tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi da aikata zamba ta makudaden kudade da yawansu ya kai miliyan dubu 84. Hukumar ta EFCC na zargin Yahaya Bello da karkatar da kudaden da yawansu ya kai miliyan dubu 80 a watan Satimbar 2015, watanni hudu kafin ya shuga ofishinsa a watan Janairu 2016.
Hukumar ta EFCC ta gurfanar da Mista Bello a gaban Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun shari’a da ke Maitama Abuja bisa zargin karkatar da kudade.
A ranar 17 ga watan Afrilu 2024 hukumar ta EFCC ta yi yunkurin kama Mista Bello a gidansa residence da ke Wuse Abuja sai dai Mista Bello ya kaucewa kamen hukumar bayan samun tallafin Gwamnan na Kogi mai ci Usman Ododo.
Daga bisani kuma a ranar 18 ga watan Afrilu, 2024 hukumar ta EFCC ta ayyana tsohon gwamnan Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo wanted.
A ranar 23 ga watan Afrilu,2024, hukumar ta kuma nemi babbar kotun Federal High Court Abuja da wasu fannoni da su taimaka wajen nemo inda Mista Bello ke a boye.
Tun lokacin da aka ayyana shi a matsayin wanda ake mnema ruwa a jallo wannan hoto da aka yi masa siddabaru aka canza ke ta kara kaina a shafin na WhatsApp inda wasu ke zargin cewa Mista Bello yayi shigar mata a yunkurinsa na ficewa daga kasar don kada hukumar ta EFCCta kama shi.
Image Source: Screenshot of the WhatsApp post
Yadda wannan hoto ya bazu a shafin na WhatsApp a ranar 24 ga watan Afrilu,2024 ya sanya DUBAWA gudanar da bincike a kansa.
Tantancewa
Mun gudanar da bincike kan hoton ta hanyar amfani da hanyar gano asalin hoto ta (Google Reverse Image Search) Si muka gano cewa, asalin hoton na Jane Nnamani ce wato matar tsohon shugaban majaliosar dattawan Najeriya da ta rasu , an kuma wallafa hoton nata ne a wani shafi na Nigerianewsleader a ranar 7 ga watan Mayu, 2023.
Image Source: NigeriaNewsleader
Mun kuma gano irin wannan hoto da aka wallafa a Qed. ng kan rasuwar ta Misis Nnamani a Mayun 2023. A cewar shafin da ke wallafa labaransa a kafar ta intanet an yi amfani da hoton ne don bayyana shirin binne matar ta Ken Nnamani.
Kammalawa
Bincikenmu ya gano cewa anyi amfani da hoton ne aka makala fuskar Mista Bello bayan wasu dabaru da aka yi a asalin hotom ma Misis Nnamani mai rasuwa, don haka hoton da akae yadawa a shafin na WhatsApp YAUDARA CE.
Wanda yayi wannan aikin bincike yayi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Olufisoye Adenitan, FRCN positive fm Akure jihar Ondo, Najeriya, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar