Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: DDL Hausa tayi da’awar cewa, shugabannin Jam’iyyar APC na Mazabar Kawo Sun Dakatar da Dan Gidan Malam Nasiru El-Rufa’i Hon. Bello El-Rufai na Tsawon Watanni Uku Bisa Dalilan Nuna Rashin Da’a, Rashin Biyayya da kuma Rashin Mutunta Majalisar Dokokin Jihar da ma Kakakin Majalisar.
Hukunci: Karya ne! Bincike ya tabbatar cewar babu wani zancen dakatar da dan tsohon gwamnar Kaduna Hon. Bello El-Rufai da aka yi, kuma ma shi dan majalisar wakilai ne dan haka ba majalisar jiha ce ke da hurumin hukunta shi ba ko da ya yi laifi
Cikakkayen Bayani
A wani labari da DDL Hausa ta wallafa, tayi da’awar cewa Shugabannin Jam’iyyar APC na Mazabar Kawo Sun Dakatar da Dan Gidan Malam Nasiru El-Rufa’i Hon. Bello El-Rufai na Tsawon Watanni Uku Bisa Dalilan Nuna Rashin Da’a, Rashin Biyayya, Rashin Mutunta Majalisar Dokokin Jihar da Kuma Kakakin Majalisar.
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ce ba za ta lamunci kalaman ”rashin ɗa’a” daga wajen Bello El-Rufai, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa ba, a kan dambarwar da ake yi da ta shafi binciken gwamnatin mahaifinsa, tsohon gwamna Nasir El-Rufai.
A sanarwar da majalisar ta wallafa a shafinta na X, ta ce tun bayan da ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai binciki al’amuran da suka shafi kashe kuɗaɗe da karɓar basussuka daga shekarar 2015 zuwa 2023 a Jihar Kaduna, “sai Bello ya wallafa wasu kalamai a X na neman faɗa.”
Sai dai sanarwar mai ɗauke da sa hannun Suraj Bamalli, mai taimaka wa Shugaban Majalisar kan harkokin sadarwa, ta ce duk da cewa tuni Bello, ya goge saƙonnin, sun kasance “na raini ga kafatanin ɓangaren dokoki na jihar.” Kamar yadda muka gani a cikin wannan labarin da trtafrika ta wallafa a shafinta wanda muka tsakura da yin karin bayani dangane da abin da ya faru.
Ko bayan da DDL ta wallafa batun a shafinta da yawa sun yi tsokaci kamar haka: Muhammd Uwaisu Khaleefa ya ce “Allah ya sa mu dace, ku kuke kidan ku ku ke rawar ku, Allah ya kara farraka a tsakaninku.” Yayin da Muhammad Auwal kuma ya ce “Abin da ya yi ya yi daidai.” Bacin haka akwai da yawa kuma da suka rika danganta batun da halayyar Bellon da mahaifinsa a maimakon tsokaci kadai a kan batun da ke da nasaba da siyasa.
Ganin yadda dai wannan batun da ma ke tattare sarkakiya kuma ya na iya ruda jama’a ne ya DUBAWA ta dauki nauyin gudanar da wannan binciken na tabbaar da gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Dan haka, DUBAWA ta fara da binciken zagin da ake zargi Hon. Bello El-Rufai ya yi wa gwamnatin jihar Kaduna, sai dai ba ta gani ba a shafinshi, bisa dukkan alamu dai ya goge sakon da gaske kuma buba shaidar zagin ko barazanar da ake cewa ya yi.
Daga nan sai DUBAWA ta yi binciken tabbatar da wannan da’awar a manharajar Google ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomin da za su nuna labarai dangane da batun ko kuma ma dai masu alaka da batun. Sakamakon binciken ya nuna da cewar babu wata kafar yada labarai sahihiya a Najeriya baki daya da ta bada wannan rahoto illa DDL Hausa.
Duk da haka DUBAWA ta kara bincika kafafen yada labarai daban-daban tunda da yawa sun dauki labarin badakalar Bello El Rufa’in tun bayan da ya shiga shafin X ya na kare mahaifin nasa.
Sai dai ta ga duk babu rahoto akan wannan batun dakatar da Hon.Bello El-Rufai illa shafin DDL Hausa in da DUBAWA ta ga labarin. In ban da binciken da ake wa mahaifinsa tsohon gwamnar Kaduna Mal. Nasiru El-Rufai a kan bashin da ya ciwo wa jihar da ayyukan da aka yi da kuɗaɗen, ba bu wata maganar dakatar da dan sa Hon. Bello El-Rufai.
Ra’ayin kwararre
Domin karin bayyani, DUBAWA ta sami kwararre a harkokin siyasa mai suna Hon. Ali Kalat wanda ke wakiltar mazaɓar karamar hukumar Jema’a a a jihar Kaduna in da ya shaida mana cewa na farko basu da ‘yancin dakatar da Hon. Bello El-Rufai saboda ba mamba ba ne na jiha amma a matakin tarayya ya ke wato can a majalisar Wakilai. Dan haka majalisar dokoki na jiha ba ta isa ko kuwa bata da ikon dakatar da shi.
Ya kara bayyana mana cewa ko a matakin jiha, ba’a dakatar da mutun hakanan sai an girka kwamitin da’a wanda zai yi zama na musamman ya tantance laifukan da ake zarginsa da shi su tabbatar ko ya cancanci dakatarwa ko bai cancanta ba, kafin su kawo zancen gaban mambobin majalisa.
“Wannan kwamitin zai gudanar da bincike ne sosai, bauan ya kammala binciken ya gamsu, sai su tura mi shi wasika suna bayyana masa abubuwan da suka gano, daga nan sai su saurari amsarasa,” ya bayyana.
“Bayan wannan binciken sai su rubuta cikakken rahoto su gabatar wa majalisar su ba ta shawarar cewa su dakatar da shi idan har sun gamsu da cewa abun da ya yi ya cancanci dakatarwa.”
Ya kuma kara da cewa bayan haka ne majalisa za ta karanta rahoton sa’annan sai a yi zabe. Wadanda suka fi rinjaye ne za’a bi wato idan har mafi yawan ‘yan majalisar sun amince a dakatar da shi bisa shawarar da kwamiti ya bayar sai a dakatar da shi, idan kuma ba haka ba sai ya cigaba da mukaminsa.
Kammalawa
A karshe, binciken DUBAWA ya tabbatar da cewa babu gaskiya kan wannan da’awar msi cewa an dakatar da Hon. Bello El-Rufai na Tsawon Watanni Uku bisa dalilan nuna rashin da’a;rashin biyayya, rashin mutunta majalisar dokokin jihar Kaduna, da kuma kakakin majalisar. Don haka da’awar Karya ce!
An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar, Deborah Majingina Habu, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.