African LanguagesHausa

Bincike kan Da’awar Nuhu Ribadu Game Da Matsalar Tsaro a Najeriya Sadda Ya Kai Ziyara Sokoto

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken Bayani

Matsalar tsaro a Najeriya ta jima tana ci wa gwamnati tuwo a kwarya, shugabannin da suka gabata duk sun yi kokarin su amma har yanzu an kasa magance wannan matsalar, musamman a yankin arewacin kasar inda ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane ke gallazawa jama’a.

Satar mutane da ‘yan bindigar ke yi na ci gaba da sauya salo inda suka daina dauki dai-dai zuwa daukar jama’a masu yawa ko kuma satar daliban makaranta.

Tun kafin zuwan wannan gwamnatin, an sace yan makaranta da dama kama daga dalibai a makarantar Chibok a jihar Borno da na makarantar Dapchi a Yobe wadanda Boko Haram suka sace.

Sai kuma dalibban da yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace da suka hada da na makarantar kimiyya ta maza dake Kankara jihar Katsina, da na makarantar Jangebe jihar Zamfara, sai daliban makarantar Kagara dake jihar Neja da na kwalejin tarayya dake Mando da jami’ar Greenfield duk a jihar Kaduna da daliban Islamiyyar Tegina a jihar Neja da kuma daliban kwalejin tarayya ta Yauri kazalika da daliban sakandiren Kuriga dake jihar Kaduna.

Gwamnati ta samu nasarar ceto wasu daga cikin daliban a hannun yan bindigar yayinda wasu daga ciki iyayen su ne suka yi fadi tashi na ganin an sako su ta hanyar biyan kudin fansa. Sai dai wasu daga cikin daliban babu su babu labarin su.

A ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, 2024 ne aka ji Malam Nuhu Ribadu,  mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro yayi wasu maganganu a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, inda ya gabatar da wata makala akan sha’anin tsaro albarkacin bukin yaye dalibbai na Jami’ar Usman Danfodio. 

A cikin kalaman nasa, ya bayyana cewa an ceto dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ba, haka kuma yace tun bayan da aka gwamnatin Tinubu ta hau mulki yan ta’adda basu kai hari a muhimman wurare ba kamar yadda suka saba. 

Kalaman  sun janyo martani daga al’umma ganin cewa sun fito ne a bakin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, wannan ne yasa Dubawa yin bincike don sanin gaskiyar wasu daga cikin kalaman da yayi. 

Da’awa 1: An sako duk wadanda masu garkuwa da mutane suka tsare a arewacin Najeriya. 

Tantancewa

A yan makonnin da suka gabata hukumomin tsaro sun samu nasarar hallaka wasu shugabannin ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane irin su Sani Dangote da Lamo Saude da dai sauran su. Hakama hedikwatar tsaro tace daga watan Janairu zuwa Fabrairun 2024, sun kashe ‘yan ta’adda akalla 2,352, sun kama 2,308 tare da kubutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar.

Hedikwatar tsaron kuma ta ce sojoji sun kubutar da mutane 465 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Afrilun 2024. Haka kuma an ceto dalibai da aka yi garkuwa da suka hada na kauyen Kuriga dake jihar Kaduna, da daliban islamiyya a jihar Sakkwato ba tare da biyan kudin fansa ba, sai dai yadda kubutar da daliban ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Wani kwararre akan sha’anin tsaro Kabiru Adamu, a firar sa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka ya bayyana shakku akan kubutar da daliban ba tare da anyi musayar wani abu da yan bindigar ba, “ba dole sai kudi ba, zasu iya bukatar ayi musaya fursunoni ko su bukaci wata kulawa da dai sauran su.”

Duk da cewa sha’anin rashin tsaro abu ne dake sauyawa saboda yawan kai hare-hare da satar mutane a kowace rana da yan ta’adda ke yi, wata kididdiga daga kamfanin kan sha’anin tsaro a Najeriya SBM Intelligence ya ce ya samu rahoton mutane 4,777 da aka sace tun lokacin da Tinubu ya hau mulki a watan Mayun bara.

Ko a daren ranar 18 ga watan Afrilu wato 17 ga wata sai da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da wasu gwamman mutane a “kauyen Angwar Danko dake mazabar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a yayin wani hari da suka kaiwa wadannan al’ummar.

Kuma a wannan makon ne aka cika shekaru 10 da sace dalibai a makarantar sakandiren ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, kuma har yanzu akwai sauran matan kusan 100 da ke tsare a hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su.

Hukunci: Kalaman mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro cewa an sako duk wadanda masu garkuwa da mutane suka tsare a arewacin Najeriya Yaudara ce!

Da’awa 2: Tun hawan gwamnatin Tinubu ‘yan ta’adda masu tsatstsauran ra’ayi basu kai hari ga muhimman wurare ba. 

Tantancewa

Najeriya na fama da tashe-tashen hankali daban-daban da suka shafi matsalar tsaro, daga satar mutane domin neman kudin fansa zuwa ayyukan masu ‘yan tawaye da kuma aikata miyagun laifuka da kusan daukacin kasar ke fama da shi.

A mafi yawan lokuta wadannan ‘yan ta’addan na kai hare-hare ga ofisoshin gwamnati domin yin barna ko karbe iko da shi. Game da kalaman Malam Nuhu Ribado cewa Yan ta’adda masu tsatsaruan ra’ayi basu kai hari ga muhimman wurare ba tun hawan wannan gwamnati, kamar yadda suka yi a kan jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna da fasa gidan yari da kuma wuraren ibadu. Bincike ya nuna cewa Yawanci gaskiya ne.

Domin kuwa a ranar 18 ga watan Fabrairun 2024 wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke garin Zurmi hedikwatar karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, inda suka hallaka a kalla mutum bakwai har da wani jami’i daya.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2024 ma, rahotanni sun nuna cewa, jami’an tsaro sun kama akalla mutane 18 da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutikar kafa Yarbawa ne da suka yi yunkurin kwace iko a Majalisar Dokokin Jihar Oyo wadda bata da nisa zuwa Sakatariyar Gwamnatin Jihar Oyo.

Sai dai har yanzu ba a samu wasu manyan hare-hare ba kamar yadda yan ta’addar ke yi a baya.

Hukunci: Da’awar cewa tun hawan gwamnatin Tinubu ‘yan ta’adda basu kai hari ga muhimman wurare ba Yawanci Gaskiya ne!

Da’awa 3: An daina saka dokar zaman gida a yankin kudu maso gabas Najeriya.

Tantancewa

Tun bayan lokacin da aka kamo Nnamdi Kanu daga Kasar Kenya, kungiyar IPOB ta gudanar da zanga-zanga daban-daban da daukar haramtattun matakai ciki har da aiwatar da dokar zama a gida a duk ranakun Litinin har sai an sako Nnamdi Kanu.

Bincike ya nuna cewa tun bayan hawan wannan gwamnatin, jami’an tsaro na samun nasara akan masu fafutikar kafa kasar Biyafra dake tada kayar baya, inda Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya ke lalata sansanin ‘yan kungiyar awaren IPOB da takwararta ta ESN a Jihohin Ebonyi da Abiya da kuma Delta.

A watan Maris na 2024, Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce a ranar 10 ga wata sojojin sun kai samame tare da lalata masana’antar kera bindigogi ta IPOB da ke yankin Ekoli Edda da Amagwu Ohafia a Jihar Ebonyi da Jihar Abiya.

A ranar litinin 8 Afrilun 2024, Rundunar ‘yan sandan jihar Imo tayi nasarar kama wani da ake zargin dan IPOB ne, mai suna Chidebere Nwuzor kuma yana daya daga cikin masu aikin tursasa bin dokar zaman gida da kungiyar ke sa wa.

A yanzu dai za’a iya cewa umurnin zaman gida da kungiyar ke bayarwa bai yin wani tasiri, kasancewar ko da sun fito domin tursasa al’umma rufe masana’antu da wurin kasuwanci, suna fuskantar fushin jami’an tsaro da na yan sa kai, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito a watan Fabrairun 2024.

To sai dai kuma ana cikin fargaba a yanzu, bayan da wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar zaman gida domin girmamawa da sojojin Biyafra da suka rasa rayukansu a yakin basasar 1967-1970 da aka yi a Najeriya.

Hukunci: Da’awar Nuhu Ribado cewa an daina saka dokar zaman gida a yankin kudu maso gabas Najeriya Gaskiya ce!

A Karshe

Kalaman mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro cewa an sako duk wadanda masu garkuwa da mutane suka tsare a arewacin Najeriya Yaudara ce! Babu wata shaida dake tabbatar da hakan.

Da’awar cewa tun hawan gwamnatin Tinubu ‘yan ta’adda masu tsatstsauran ra’ayi basu kai hari ga muhimman wurare ba Yawanci Gaskiya ne! Bincike ya nuna cewa mayakan ISWAP da yan bindiga sun kai hari a ofishin yan sanda, kuma masu fafutikar ballewa daga Najeriya sun yi yunkurin kwace iko a Majalisar Dokokin Jihar Oyo.

Da’awar Nuhu Ribado cewa an daina saka dokar zaman gida a yankin kudu maso gabas Najeriya Gaskiya ce! Mun gano cewa jami’an tsaron Najeriya na samun nasarar fatattakar mayakan IPOB, dalilin da ya sa ko sun sanya dokar bata tasiri.

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »