|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Hoton VeryDarkMan a hannun EFCC ya yadu inda yake nuna irin tuhumar da ake masa.

Hukunci: Karya ce. Binciken da muka yi ya gano cewa hoton da ke nuna kama shi kwaskwarima ce aka yi.
Cikakken Sako
Wani hoto a shafukan sada zumunta da ya yadu a ranar 2 ga watan Mayu,2025 ya muma yadda hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta kama mai fafutukar kare hakkin bil Adaman nan Martins Otse wanda aka fi saninsa da sunan VeryDarkMan (VDM), a bankin Guarantee Trust Bank (GTB) da ke Abuja Fadar Gwamnatin Najeriya.
Bayan kama shi ne sai wasu masu fafutuka a shafukan sada zumunta kamar Jerry Wife TV (archived here) da Ochuole Updates suka shiga yada hotunan na VDM dauke da allo da ke nuna irin tuhumar da ake masa. Allon dai ya nuna sunansa da irin tuhumar da ake masa da kwanan wata, inda ya nunar da cewa an kama shi bisa “zargin amfani da intanet wajen muzgunawa wani.(Alleged case of cyberstalking and ML.”)”
Har ila yau wannan hoto ya bayyana a shafin X kamar yadda za a iya gani a wadannan wurare. here (archived here).
Wannan hoto ya haifar da kace-na-ce kamar yadda aka ga wani mai amfani da shafin mai suna Chigozie Ike na cewa VDM ya fara fuskantar kalubale “karma” a fafutukar da yake yi.
Sai dai kuma wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Adeniyi Awoniyi, ya kalubalanci sahihancin hoton ne.
A wurin da aka tanada don yin tsokaci Adeniyi ya rubuta cewa “Kowa ya zama mai fafutuka ana yada bayanai marasa ingancxi ana yada labaran karya. Idan kuma aka kama su sai su fara neman magoya baya wadanda za su yi zanga-zangar neman ganin an sake su ’Ka kula da abin da kake wallafawa.”
Hoton tuhumar da ya yadu a shafukan sada zumunta. Inda aka zakulo hoton: Facebook.
DUBAWA ta gunar da bincike ganin yadda ake ta cece-ku-ce a dangane da kama VDM.
Tantancewa
DUBAWA ta lura da wasu alamu na tambayoyi ga misali an ga VDM na fara’a a maimakon ganin yana daure fuska da aka saba ganin masu laifi na yi idan aka tsare su tsawon wasu kwanaki. Sannan kuma an rubuta sunansa akan allon cikin kuskure inda aka rubuta “Martin Vicent Otse” maimakon “Martins Vincent Otse.”
Sannan hoton bai fita da kyau ba, daya daga cikin alamu na farko da ake gane hoto da aka sassauya, yawancin hotuna da aka yiwa kwaskwarima za a ga kyansu ya ragu .
Baya ga wannan kuma da aka leka shafin sada zumunta na EFCC babu inda wannan hukuma ta wallafa wannan hoto.
Mun tura hoton ga manhajar gano asalin hoto Fake Image Detector, sai ta nuna cewa ko dai an yi amfani da fasaha a aka kirkiri hoton ko kuma an jirkita shi.
Sakamako da aka samu daga Fake Image Detector
Mun kuma gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a Google kuma sakamakon da muka gano ya nunar da hoton VDM a bayansa da wata taga ko window a wani shafin facebook da aka kirkira parody profile.
Ta hanyar amfani da wannan sakamako an sake bin diddigin hoton sai ya kaimu ga shafin Instagram na VDM, anan aka gano asalin hoton original version of the photo, tare da wani bidiyo da aka wallafa a ranar 26 ga watan Disamba, 2023.
Asalin hoton da aka yada. An samo shi daga shafin VDM na Instagram.
A sako (statement) da hukumar EFCC ta wallafa a ranar 6 ga watan Mayu,2025, hukumar ta EFCC ta bayyana cewa a baya ta gayyaci VDM a bisa tuhume-tuhume daban-daban kan “zargin almundahnar kudade” sai dai baya amsa gayyatar da ake masa.Ta kara da cewa a wannan karo an kama shi ne bisa tsarin doka kuma ana tsare da shi.
“A kyale EFCC ta gudanar da aikinta ba sani ba sabo, da zarar an kammala bincike za a gabatar da tuhumar da ake masa,” abin da wani bangare na jawabin ya nunar kenan.
Hoton bayani daga shafin X na EFCC
A Karshe
Bincikenmu ya gano cewa hoton VDM da ke yawo a shafukan sada zumunta an yi kwaskwarima ne aka hada shi don kawai a yada labarin karya.




