Zargi: A wani sakon Whatsapp da ya bi gari, an yi sanarwar cewa VC din jami’ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE) a umurci duk daliban da ke jami’arsa da su fara shirin jarabawa yayin da ASUU ke yajin aiki.
Ranar daya ga watan Afrilu, wata sanarwa ta bayyana a manhajar WhatsApp wadda ke cewa wai VC din jami’ar tarayya ta Oye-Ekiti, Farfesa Abayomi Fasina ya “gargadi” duk dalibai da su yi shirin jarabawa-
An rubuta sakon ne a shigen labari iri na jarida ko kafofin yada labarai da taken:
“Ku yi shiri gabannin jarabawa, VCn FUOYE ya gargadi daliban jami’arsa.”
Zuwan sanarwar a daidai lokacin da kungiyar ASUU ke yajin aiki ya haifar da martani daga daliban jami’ar wadanda ke fargabar cewa mai yiwuwa da zarar aka kammala yajin aikin mallaman za su fara da jarabawa ne ba tare da an yi darussa ba.
Da aka tambayi wani wanda ya raba labarin a Whatsapp ko ya san ainihin tushen labarin, ya bayyana shakkun shi dangane da sahihancin bayanin amma ya ce ya raba ne kawai dan nishadi.
Sai dai matsalar ita ce mutumin ya raba adireshin labarin da ya yi kama da wannan ba tare da majiya ko kuma ma kadan daga cikin kalaman da VCn ya yi sadda aka yi hira da shi ba, ta yadda za’a gane ko labarin na da irin nagartar da ake bukata.
Daya (1) ga watan Afrilu rana ce da ta yi suna dan wasannin barkwancin da ake yi dan a yaudari abokai, abin da ake dangantawa da “April Fool”. Dama can kowace ranar daya ga watan Afrilu abokai kan tsokani juna a cikin wasa ko ba’a albarkacin ranar ta April Fool a yanayi na anashuwa. Sai dai kuma idan ba’a yi hankali ba irin wadannan wasanni kan janyo lahani abin da ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tabbatar da gaskiyar wannan zargin.
Tantancewa
Da DUBAWA ta latsa adireshin yanar gizon da aka bayar tare da wannan labarin sai ya kai ta wani shafi mai suna “Prank Mania.” “shafi ne da ke taimakawa mutane su kirkiro sakonnin barkwanci da ba’a wanda za’a iya yadawa a WhatsApp, Facebook, Tiwita da dai sauran shafukan sada zumunta na soshiyal mediya.”
Daga cikin kanun labaran karyar da aka riga aka kirkiro da wannan shafin, labarin jarabawar ta jami’ar Oye-Ekiti ta bullo tare da wani jerin umurnin da ke gayyatar DUBAWA ita ma ta shirga na ta labarin “CREATE YOUR RANK OR SHARE THIS PRANK.”
Duk da cewa shafin ya yi gargadi masu amfani da shi su guji daukar abubuwan da suka gani a shafin da gaske, lahanin da ya riga ya yi ga al’umma ya wuce gona da iri.
Wannan ya kasance haka ne domin masu amfani da soshiyal mediya yawanci ba sai sun karanta labari suke yarda da shi ba, daga sun ga kanun shi ke nan ya isa.
Domin sake tantance wannan labarin DUBAWA ta tuntubi shi kan shi VC din na Jami’ar Tarayyar ta OYe-Ekiti Farfesa Abayomi Fasina wanda da kansa ya karyata zargin:
Mr. Wole Balogun mai baiwa VCn shawara kan batutuwan da suka shafi kafofin yada labarai, ne ya yi magana a madadin shugaban jami’ar, ta wayar tarho inda ya ce:
“wannan ba gaskiya ba ne. Kasancewarmu cibiya a tarayyar kasar, ba zamu iya yin wani abu ba idan har ASUU na yajin aiki.”
A Karshe
Baya ga karyata zargin da shugaban jami’ar ya yi, an kirkiro labarin ne a shafin “Prank Mania,” shafin da ke barin mutane su shirya labaran karya. Dan haka labarin ba gaskiya ba ne.