Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani hoton da ke nuna ginin da ya fadi kwanan nan a Jos.

Hukunci : Yaudara ce! Bincikenmu ya nuna mana cewa an dauko hoton ne daga wani abin da ya faru a jihar Kaduna a shekarar 2013.
Cikakken bayani
A ‘yan shekarun da suka gabata, gidaje da dama sun fadi a Najeriya, amma babu wanda ya zo da matukar takaici kamar wanda ya afku kwanan nan a birnin Jos wanda ya yi sanadin rayukan dalibai da malamansu a jihar Filato.
Yayin da take jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa cikin bayanin da ta wallafa, Prosperous Oluchi, wata mai amfani da Facebook ta wallafa wani hoton da ke bayyana wurin da abun ya faru. A bayanin da ta yi ta ce: “Kia! Babbar makaranta a Jos ta fadi jiya kuma kananan yara da yawa sun rasa rayukansu. Iyaye sun rasa yara. Wata mata ta rasa yaranta hudu, kuma tana jin labarin ta bi su, yayin da a nan, Allah ya kare ni da ku da yaranmu …. Me ya sa ba za ku yabawa Ubangiji da suna mai dadi ba. I ina kiransa mai kare ni”
Ms Oluchi na daga cikin wadanda suka yada hotuna da bidiyoyi daga wannan hatsarin. Sai dai hotonta ya banbanta daga wadanda aka rika wallafawa wanda ma har ya sa wasu suka fara tambayar sahihancin hoton.
Hoton da Ms Oluchi ta wallafa a Facebook. Asalin hoton: Facebook.
DUBAWA ta lura da cewa a duk lokutan da abubuwa irin wannan suka faru, masu amfani da soshiyal media su kan sa hotunan da ke yaudarar mutane, wata sa’a ma labaran karya kawai a soshiyal mediya. Shi ya sa muka dauki nauyin tantance gaskiya.
Tantancewa
Mun fara da tantance hoton cokin manhajar gano asalin hoto da sadda aka fara amfani da shi, a nan ne muka gano cewa hoton na cikin yanar gizo-gizo tun shekarar 2013. Gidan talibijin na Channels ne ya fara wallafa hoton kuma na wani gini ne da ya fadi a jihar kaduna ranar 31 ga watan Yulin 2013.
Ko da shike, kafofi da dama sun yi amfani da hoton dan bayyana faduwar gine-gine da dama kamar yadda za ku iya gani a nan, nan, nan, da nan.
A Karshe
Wannan hoton da Ms Oluchi ta wallafa ba shi da wani alaka da ginin da ya fadi a Jos. Dan haka wannan bayanin na yaudarar jama’a ne kawai.