ECOWAS yayin zaman da Tinubu ya jagoranta. Asalin hoton: TheCable
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyo da ya shuhura a shafukan soshiyal mediya na da’awar cewa shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaba a Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).

Hukunci: Karya! Tinubu bai yi murabus daga kujerar shugabancin ECOWAS ba. Bisa bayanan wata sanarwar da ECOWAS ta fitar, wa’adinsa ya cika ne ranar tara ga watan Yulin 2024 amma an sake zabensa a wannan ranan. Kafofin yada labarai masu nagarta duk sun dauki labarin, kuma sun yi bayani makamancin wannan.
Cikakken bayani
Bola Tinubu, shi ne shugaban kasa mai ci yanzu a Najeriya, kuma shi ne ke jagorantar ECOWAS tun watan Yulin shekarar 2023, bayan da ya karbi shugabancin daga hannun shugaban kasar Jamhuriyar Guinea Bissau, Umaro Embalo.
Wani mai amfani da shafin X, @Naija_PR, ya yi da’awar cewa Tinubu ya yi murabus bayan da ya shafe shekara daya yana shugabancin kungiyar.
Ya wallafa wannan bayanin da hoton Tinubun da tsokacin da ke cewa: “Labari da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya sauka daga mukaminsa na shugaban ECOWAS.”
Ana iya ganin wannan da’aawar a shafukan X da na Facebook, a nan da nan.
Tun ranar 7 ga watan Yulin 2024 aka wallafa labarin kuma an kalla sau 131,000, an sake wallafawa a wasu shafukan sau 180 sa’annan ya sami alamar like 1,000.
Bisa la’akari da shuhurar da wannan batun ya yi da ma yadda zai iya tasiri, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya a matsayin gangamin da ta take yi na yaki da bayanan karya a yankin Yammacin Afirka.
Tantancewaa
DUBAWA ta fara da gudanar da binciken mahimman kalmomi. Sakamakon ya nuna mana cewa an zabi Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS din ne ranar tara ga watan Yulin 2023.
Dan tantance tsawon wa’adin da mukamin ke da shi, mun duba babban shafin ECOWAS, (ECOWAS’s official website) inda muka gano wani sakin layin da ke bayanin cewa “Mukamin shugaban kungiyar na yawo ne tsakanin kasashe mambobi kuma ana gudanar da zaben ne bayan kowace shekara.”
Dan haka, tsawon lokacin da kowani zababben shugaba ke yi a kan kujerar mulkin ba ya taba wuce shekara daya. Bisa la’akari da haka, ya kamata a ce da Mr Tinubu ya kammala wa’adinsa ranar tara ga watan Yulin 2024 — sadda ya cika shekara daya a mukamin.
DUBAWA ta sake gano wata sanarwar da ECOWAS ta fitar da kanta ta na sanar da cewa ta sake zaben Mr Tinubu dan ya yi tazarce a mukamin na wani karin shekara dayan.
Wannan ya faru ne sadda suka gudanar da babban taron shugabannim kasashe da gwamnatocin ECOWAS karo na 65 wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa a ABuja.
Bacin haka, kafofin yada labarai masu nagarta irin su Channels da Punch duk sun dauki labarin.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa Tinubu bai yi murabus daga mukaminsa na shugaban ECOWAS ba. Ya kamata a ce ya kammala wa’adinsa ne ranar tara ga watan Yulin 2024, kafin aka sake zaben shi.
