African LanguagesHausa

Hotunan labaran da aka gyara ana zargin wai za’a rage albashin masu yi wa kasa hidima na NYSC, da abun da ke tashe a WhatsApp

Zargi: Hotuna da yawa da mutane suka yi amfani da shi a shafukansu na WhatsApp na zargin wai shugaba Bola Tinubu na shirin rage albashin wata-wata na masu yi wa kasa hidima. 

Sakamakon Bincike: Wannan bayanin karya ne. Sabon shugaban da aka rantsar bai yi wannan furucin ba. 

Cikakken bayani

Watanni bayan nasarar da ya yi a zaben watan Fabrairun 2023, an rantsar da shugaba Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya ranar 29 ga watan Mayu a matsayin wanda ya karba daga hannun Muhammadu Buhari, sa’annan ya kuma zama zababben shugaba na biyar bisa tsarin mulkin dimokiradiyyar da kasar ta koma tun shekarar 1999.

Sai dai kasar na fama da rikicin tattalin arziki a fannoni daban-daban sakamakon wasu daga cikin manufofin da Buhari ya aiwatar lokacin da ya ke mulki, inda ya bar kasar cikin irin kangin bashin da ba a taba gani ba a tarihin kasar.

Domin shawo kan wannan matsalar, daya daga cikin abubuwan da ya sanar a matsayinsa na sabon shugaba shi ne cire tallafin man fetir, abun da ya tsunduma ‘yan kasa cikin wani yanayi na rudani, sa’o’i kadan da kammala rantsuwar kama aikin na sa.

Wata kila wannan ne ya yi tasiri kan tunanin mutane a kan cewa zai rage kudin alawus din da ake bai wa masu yi wa kasa hidima daga N33,000 bisa karin da aka yi a shekarar 2020 zuwa N25,000.

Sai dai,  da muka kasa kunne sosai a jawabin da Tinubu ya yi a bukin rantsarwar ba mu ji wani abu game da batin kudin alawus din ba. Domin tabbatar da hakan ne ya sa muke so mu gano mafarin wadannnan hotunan da ake amfani da su da ma jita-jitar da ke so ya tayar da husumi a cikin kasa.

Tantancewa

Bayan da muka yi nazarin hotunan, mun gano abu daya, akwai wani rubutu da aka yi amfani da shi kan duka hotunan wadanda sai an sa ido sosai ake gani. Rubutun na cewa “breakyourownnews.com” wanda ke nufin an yi amfani da wannan shafin ne inda kowa ma na iya zuwa ya rubuta labarin da ya ke so ko da kuwa shakiyanci ne kawai.

DUBAWA ta kuma sake yin bincike na mahimman kalamai da wadannan kalmomin da ke rubuce kamar adireshin yanar gizo, wanda ya kai mu ga wani rahoto na tantance gaskiya kan wani batu da bisa dukkan alamu shi ma an kirkiro shi da wannan shafin.

Haka nan kuma, mun sami kwafi na jawabin Tinubu kuma ba mu komai dangane da wannan batun ba. Kuma kafofin yada labarai masu nagarta a kasar su ma ba su dauki labarin ba, sa’annan su kan su kafofin sada zumunta na soshiyal mediya da sauran maus ruwa da tsaki a kasar ba su wallafa labarin ba.

A Karshe

Shugaba Tinubu bai bayar da wani bayani kan shirin rage alawus din ma su yi wa kasa hidima ba. Dan haka wannan zargin karya ne kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button