African LanguagesHausa

KARYA! Annie Idibia na cikin koshin lafiya ba ta da cutar daji

Claim: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai mai dakin mawaki Tuface na addu’a wa matarsa wadda ke fama da cutar daji ko kuma Cancer.

Sakamakon Bincike: KARYA! Hoton da aka yi amfani da shi tsohon hoto ne wanda ta dauka a shekarar 2015 lokacin wani gangami na fadakar da jama’a dangane da cutar daji.

Cikakken bayani

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, cutar daji ita ce sanadin mutuwa a mataki na biyu a duniya baki daya inda ake kiyasin akalla mutane miliyan 9.6 suka hallaka daga cutar kawo yanzu.

Wani mai amfani da shafin Facebook, LoveDoctor Daniels, ya wallafa hoton Annie Idibia, matar Innocent Idibia, wanda aka fi sani da TuFace, ya ce tana fama da cutar daji. A labarin, Mr Daniels ya kuma kara da cewa TuFace na kira ga ‘yan Najeriya da su taya shi addu’a saboda matarsa na fama da cutar daji. Ya kuma kara da cewa dama Annie Idibia ta dade tana fama da rashin lafiya. Sa’annan labarin na dauke da adireshin wani shafi mai suna, “cancer.facebook.com”.

Mutane 580,000 suka latsa alamar “Like” a jikin hoton Annie inda ta yi kama da mara lafiya sosai, wasu 16,000 suka yi tsokaci a karkashin labarin, yayin da was kuma suka sake raba labarin har sau 41.

Yadda labarin ya dauki hankali ya kuma sa mutane cikin wani yanayi na tausayi, da sarkakiyar da irin wannan batun ke da shi, da ma dai taurarin da ake magana a kai ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan batun.

Tantancewa

Dan tantance hoton da aka yi amfani da shi, mun yi nazarin shi a manhajar google inda muka ga cewa hoto ne aka dauka dan fadakarwa dangane da hadarin cutar daji na mama a shekarar 2015 wanda aka yi wa taken “against all odds” wato “ko ta halin kaka.” Burin hotunan shi ne su fadakar da jama’a kan mahimmancin binciken mama a matsayin kariya daga illolin cutar domin ta yin irin binciken ne kadai ake iya ganewa a kan kari dan a magance ta. Binciken ita ce kariya.

Mun kuma bi adireshin da aka wallafa tare da hoton, wanda ya kai mu wani shafin caca. Wannan ya tabbatar mana cewa an yi haka ne dan jan hankalin jama’a zuwa shafin cacar.

Bugu da kari babu wani bayani a shafin TuFace dangane da rashin lafiyar mai dakin nasa da ake zargi. Sa’annan ita da kanta Madam Idibia ta karyata zargin da jita-jitar ta fara yaduwa a shekarar 2020. 

A karshe

Labarin da ke zargin wai Annie Idibia na da kansa ba gaskiya ba ne. Babu wani bayani daga TuFace wanda ke bukatar wasu addu’o’i wa matarsa kamar yadda ake zargi. Hoton da aka yi amfani da shi kuma na wani gangami ne dan fadakar da jama’a dangane da mahimmancin gudanar da bincike a kan mama dan kariya daga illolin cutar kansar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button