Hausa

Jami’ar jihar Sokoto ba ta tallata daukar sabbin ma’aikata ba

Cikakken Bayanni

A Kwanakin nan an yi ta yada sako a kafofin sadarwa na soshiya midiya da WhatsApp dake cewa wai jami’ar jihar sokoto na daukar mutane aiki, sakon ya kuma kara da yin kira ga jama’a da su yada sakon ya kai ko ina saboda wadanda suka cancanta su nema.

Sakon ya ce jami’ar na neman malamai da kwararru a fannin ilimin da za su cike gurabe a matakai na koyarwa da wadanda ba na koyarwa ba, mukaman dai sun hada da: Babban lakcara, farfesa, mataimakin lakcara da lactara na daya da na biyu, da Reader ko kuma wanda ke gaba da babban lakcara, da suaransu. Masu sha’awa in ji sakon na da wa’adin nan da 18 ga watan Oktoba 2021.

Jihar sokoto na daya daga cikin jihohi 36 da ke Najeriya. Ta na yankin arewa maso yammacin kasar a kan iyakar da Najeriyar ke da shi da Jamhuriyar Nijar. Domin yawan masu son samun damar karatu a jihar, tsohon gwamnan jihar gwamna Aliyu Wamakko ya yanke shawarar kirkiro jami’a mallakin jihar sannan ya kafa kwamiti.

Tantancewa

Dubawa ta fara bincike ta zuwa shafin yanar gizon da aka danganta ta sakon. Shafin yana saka daukar sabbin ma’aikata a jami’o’i daban-daban a Najeriya ciki har da jami’ar jihar Sokoto. Shafin ya nuna kansa a matsayin mai tallar guraben ayyuka da samun tallafi a gida da waje.

Dangane da ayyukan da aka talata, shafin ya ce albashi da sharuddan aikin da aka gindaya sun zo dai-dai da na takwarorinsu na sauran Jami’o’in Najeriya.

Karin bincike a shafin jami’ar jihar Sokoton ya nuna cewa babu wadannan guraben aikin da ake fadi kuma ma akwai gargadin da aka wallafa tun ranar 18 ga watan Agustan 2021, mai dauki da sa hanun rajistrar makarantar Amins Yusuf Garba, dake cewa akwai tallar da ke yawo a kafofin sadarwa na internet wanda ke cewa makarantar na daukar ma’aikata.

A cikin gargadin, jami’ar ta sanar wa jama’a cewa makarantar ba ta daukar ma’aikata kuma ta shawarci jama’a da su yi hattara cewa jami’ar bata tallata neman ma’aikata ba. Ya yi gargadin mutane su kula matuka.

Ya kara da cewa idan mutane na bukatar sanin duk wani abu game da jami’ar su garzaya shafin jami’ar a www.ssu.edu.ng da kuma kuma wadanda suke kafofin yada labarai.

A Karshe

A karshe dai bisa ga hujjojin da suka bayyana karara, babu irin wannan talla da jami’ar ta saka, ba gaskiya bane wanda ke yawo.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »