Hausa

Shin da gaske ne Kano na shirin saka dokar hana mata tukin mota?

Zargi: Wani sakon da ake yadawa a kafofin sadarwar internet na rade-radin wai jihar Kano na shirin hana mata tuka motocinsu a jihar.

Cikkaken Bayanni

Jihar Kano da wasu jihohi 11 da ke yankin arewacin Najeriya na amfani da tsarin dokar shari’ar musulunci wanda aka aka kafa tun a shekarar 2000.

Wannan dokar ta haramta shan giya, zina, luwadi da ma zance tsakanin na miji da na mace a cikin bainar jama’a domin hakan alama ce ta fitsari ko rashin tarbiya. Duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin kamar yadda shari’ar musulunci ta gindaya.

A Kwananakin nan kafofin yada labarai sun sake samun labari makamancin wannan, wanda ke zargin gwamnatin Kanon da aiki kan wata doka cikin sirri, inda ake zargi dokar za ta hana mata tuka motoci a jihar Kano.

Labarin wanda aka fara wallafawa a shafin The Reflector na zargin cewa shawarar wani shirin boye ne tsakanin gwamnati da majalisar Ulaman jihar.

“Bayan sun dakile ko wace kafa ta samun wani mataki na bazata dangane da abin da suke yi, gwamantin jihar Kano tare da majalisar ulamanta na shirin zartar da dokar ta za ta haramtawa mata tuka mota a jihar. Dokar za ta shafi mata har da wadanda ba musulmi ba,” a cewar labarin.

“Hakan ya biyo bayan taron sirrin da aka yi a ma’akatar shari’a lokacin hutun sallah tsakanin Kwamishanan kula da harkokin addinai Dr Mohammed Tahir (Baba Impossible) da kungiyar malamai/ulama a karkashin jagorancin Sheikh Abdulwahab Abdallah BUK”

Rahoton ya kuma kara da cewa ana aiki a kan kudurin wannan dokar a ma’aikatar shari’a kuma nan ba da dadewa ba za’a gabatar da shi a gaban Majalisar dokokin jiha domin ta amince da shi ta zamar da shi doka.

Wannan kira na haramtawa mata tuki na karkashin jagorancin Sheikh Abdallah Usman Umar Gadon Kaya wanda ya ce kyale mata su na tuki a jihar na zaman lokaci mai duhu ga musulmi. Labarin ya kuma cigaba da cewa: A gudunmawarsa Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce kamata ya yi a ce Kano ta yi koyi da Saudiyya wadda a cewarsa, al’umma ce da ke aiki da dokokin shari’a. Shi kuma a nasa ra’ayin Sheikh Abdallah Pakistan cewa ya yi yanzu ne ya kamata a zartar da wannan doka, babu lokacin da ya fi wannan ganin cewa jihar na fiskantar wani yanayi na fadakarwar musulunci a karkashin Ganduje.

“Daga farkon taron, kwamishanan kula da harkokin addini, Baba Impossible ya tabbatarwa mahalarta taron cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da kai wajen wanke Kano daga duk munanan halaye na zamantakewa.

“A matsayin mabiyi addinin musulunci gwamna Ganduje zai yi duk abin da zai iya wajen sanya kano bisa turbar gaskiya da irin tarbiyar da ke girke a addinin Islam,” ya ce.

Mahalarta taron sirrin a cewar rahoton sun hada da “Sheikh Abdallah Usman Umar Gadon Kaya, Sheikh Abdallah Pakistan, Sheikh Abdulwahab Abdallah BUK, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, Farfesa Salisu Shehu, Dr Aliyu Umar Al-Furqaan da wasu wadanda ba’a fayyace ba.

Idan har kudurin ya zama doka, dokar za ta haramtawa mata tuki a jihar ko da kuwa matan ba mabiya addinin musulunci ba ne.

Mutane fiye da 5,000 sun ga wannan labarin. Bayan haka, an raba shi a soshiyal mediya inda wasu karin jama’a suka yi ma’amala da shi.

Tantancewa

Dubawa ta fara da neman mahimman kalmomi inda ta gano cewa ban da shafin The Refelections babu wata sahihiyar kafar yada labaran da ta yi amfani da labarin a kasar baki daya. Sa’annan kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mohammed Garba ya karyata wannan zargin a wata sanarwar da ya fitar ranar talata, Malam Garba ya kwatanta rahoton a matsayin karyar ba ta da tushe.

Wanann labarin ba shi da sahihanci shi ya sa ba’a iya tantance majiyoyin labarin,” ya ce.

Malam Garba ya ce gwamnatin jihar ba zata gudanar da wani “taron sirri” domin ta yanke shawara kan batun da ya shafi dimbin jama’ar jihar ba, ya kuma kara da cewa ko ita kanta Saudiyya wadda jagora ce a addinin musulunci, ta cire dokar da ta hana mata tuki a kasar a 2018.

Rahoton ya ambato daya daga cikin malaman addinin da suka kasance a taron na cewa ya dace Kano ta yi koyi da Saudiyya tunda “al’umma ce mai amfani da dokokin sharia.”

Sai dai bincike ya nuna cewa mata sun yi shekaru uku suna tuki yanzu a Saudiyya.

A 2018, gwamnatin Saudiyya ta cire dokar da ta hana mata tuki. Yerima mai jiran gado Mohammed bin Salman wanda aka fi sani da inkiyarsa MBS ne ya jagoranci hambarar da dokar a matsayin daya daga cikin matakan habaka tattalin arzikin kasar ta yadda ba za ta rika dogaro da man fetur kadai ba.

Wannan mataki ya nemi ya bude al’ummar Saudiyya ga sauran kasashen duniya domin ta janyo masu zuba jari. Shugabanin kasar sun yabawa yeriman kuma sauran kasashen duniya na mi shi kallon mai rajin kare hakkin mata.

Ko da shi ke, haramta mata tukin da aka yi a Saudiyya, abu ne da ya shafi al’ada ba kamar yadda dokokin da aka sanya a yankin arewacin Najeriya suka shafi addini ba.

Kwamishinan ya kuma nuna farincikinsa da cewa yawancin malaman da aka ambato a rahoton sun riga sun nisanta kansu daga labarin.

Daya daga cikinsu Sheikh Abdullah Kaya ya ce labarin karya ne wato “Fake News”

“Ni Abdullah Usman Umar Gadon Kaya, na fada da kakkausar murya wannan labari fake news ne. Bani da hannu a ciki. Wannan harka ce ta makiya, wadanda suke so su tayar da zaune tsaya a jihar Kano da Najeriya baki daya,” malamin ya rubuta a shafin shin a Facebook.

Dubawa ta kuma tuntubi shugaban kungiyar kiristocin Najeriya wato CAN a jihar Kano, reverend Samuel Adeoulu Adeyemo da Sheikh Ibrahim Khali shugaban kungiyar malamai/Ulamas. Su biyun sun ce labarin ba shi da tusheballantana asali.

A karshe

Batun cewa gwamnatin jihar Kano na shirin saka dokar haramtawa mata tuka mota a jihar karya ne. Babu wata sahihiyar kafar yada labarai da ta buga irin wannan labarin a kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button