Getting your Trinity Audio player ready...
|
Dapo Olorunyomi, mawallafin jaridar Premium Times, ya soki shawarar da kamfanin Meta ya yanke na hana kwararrun masu bincike tantance bayanan da ke shafukansu tare da maye gurbin da tsarin da ya ce zai kasance karkashin jagorancin al’umma, wanda ke daya daga cikin matakan kwaskware ayyukan shafin da kamfanin ke aiwatarwa.
Mark Zuckerberg babban darektan kamfanin na dandalolin Meta wanda aka fi sani da Meta Platforms Inc, wanda shafukan Facebook da Instagram ke karkashi, ya sanar da wannan cigaban ranar bakwai ga watan Janairun 2025, inda ya kare shawarar da cewa martani ne ga sukar da ake wa kamfanin na cewa ya na nuna son kai a fagen siyasa wanda ke tasiri kan jam’iyyu da bangarorin da ke da ra’ayin mazan jiya musamman a tsarin da wasu kafofin yada labarai ke amfani da shi wajen tantance sahihancin bayanai a Amurka.
Da ya ke mayar da martani Olorunyomi ya ce kungiyoyin da ke tantance sahihancin bayanai a kasashe masu tasowa ne za su fi yin rauni daga wannan matakin saboda yawancinsu na dogaro da dangantakar da suke da shi da kafofin sada zumunta na soshiyal mediya irin su Meta ne dan samun kudaden shiga.
“Yawancin kungiyoyin tantance sahihancin bayanai a kasashe masu tasowa na dogaro da shafukan ne wajen samu kashi 80 zuwa 100 — wata sa’a ma kudinsu baki daya – daga kawancensu da irin wadannan kamfanonin ne,” ya ce.
Darektan ya bayyana cewa wannan matakin na bazata na sanya damuwa kan makomar tantance sahihancin bayanai, da sanin ya kamata a fannin kafofin yada labarai da kamfanonin fasaha.
Ya ma nuna rashin gamsuwarsa da yadda kamfanin ya bayyanawa Hadakar Kungiyoyin tantance sahihancin bayanai na kasa da kasa wato IFCN mintoci 30 kadai kafin sanar da shawarar a hukumance ga duniya baki daya.
Olorunyomi ya ce tasirin da Elon Musk ke da shi kan kafofin yada labaran Amurka na kara kasancewa karfen kafa ga gwagwarmayar da ake yi wajen tabbatar da gaskiya da mulkin dimokiradiyya mai sahihanci, inda ya ce a ra’ayinsa wannan matakai irin wannan ne suke kara lalata dangantakar da ke tsakanin fasaha da shika-shikan mulkin dimokiradiyya.
“Ba wai matsalar na da dama a wajen Amurka ba ne. Matsalar ta yi kamari a sauran kasashen duniya irinsu Brazil da Philippines inda al’ummomin fasaha da gwamnatoci ke nuna turjiya,” ya bayyana.
“Wannan na kuma misali ne na yadda ya ke tasiri kan tsarin samun kudaden shiga na kamfanonin yada labarai, irin karfin da kamfanonin fasaha ke da shi da ma irin hadarin da wadannan fasahohin ke da shi a kan mulkin dimokiradiyya. Ba gaskiya ba ne yadda a kan ce abubuwa kan gyaru da zuwan sabbin fasahohi,” ya ce. “Wadanda ke tunanin cewa da zarar sabuwar fasaha ta zo, maslaha ta samu, yanzu suna iya ganin cewa matakin da muka dauka kan fasaha da kwarewar mu na dan adam ya fi mahimmanci.”
Olorunyomi ya yi gargadin cewa wannan zai iya kara yaduwar bayanan da ba daidai ba, domin ba lallai ne masu amfani da shafukan su kasance suna da kwarewar da suke bukata wajen sanin gaskiyar bayanai ba. Ya kuma jaddada mahimmancin gyara manhajojin ta yadda za su rage bazuwar bayanai mara gaskiya a maimakon dogaro a kan abin da masu amfani da shafukan za su/ su ka wallafa.
Ko da shi ke, ya na sa ran cewa masu ruwa da tsaki musamman wadanda su ka damu da irin tasirin da hakan zai yi kan siyasa musamman wajen huldodin siyasa da mahawarorin da wannan sanarwar za ta janyo. Ya ma bayyana cewa kungiyar hadin gwiwar ta masu tantance gaskiyar ta IFCN ta riga ta fara yunkurin shawo kan lamarin.
Bacin hakan, ya yi kira da a sami martanoni na sabbin dabarun da za su yi aiki yadda ya kamata da wannan sabon cigaban da aka samu, inda ya bukaci karin hadin gwiwa tsakanin fasaha da ilimin dan adam wajen kyautatawa da wanzar da sahihiyar dimokiradiyya.