African LanguagesHausa

Jirgin kasar da ke yawo a cikin garin Legas shi ne na biyu irinsa a yankin Yammacin Afirka

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa cewa layin jirgin da aka kaddamar kwanan nan a jihar Legas shi ne na biyu irinsa da ke aiki a Yankin Yammacin Afirka bayan jirgin kasar Abuja na Abuja Rail Mass Transit.

<strong>Jirgin kasar da ke yawo a cikin garin Legas shi ne na biyu irinsa a yankin Yammacin Afirka</strong>

Sakamakon Bincike: Da gaske ne! Layin jirgin da aka kaddamar a Legas shi ne jirgin sufuri na kudi na biyu a yankin yammacin Afirka. Wanda aka yi a Abuja shi ne na farko a yankin.

Cikakken bayani

Matsalar cunkoson motoci na daya daga cikin matsalolin muhalli a birane sakamakon yawan ayyukan mutane na yau da kullun. A manyan biranen da ke da cigaban tattalin arziki, matsalar ma ta fi kamari.

Domin shawo kan wannan matsalar a Legas, gwamnan Babajide Sanwoolu ya kammala layin jirgin da aka fi sani da Blue Line Rail mai tsawon kilometa 27, shekaru 40 bayan da aka fara. Matakin farko zai rika bi  daga Marina zuwa Mile 2, yayin da na biyun kuma zai hada daga Mile 2 zuwa Okokomaiko. Da ma can an yi amfani da launuka daban-daban dan banbanta sassa hudun da za’a sanya wa jiragen tun lokacin da aka fara kaddamar da shirin a shekarar 2003 lokacin a karkashin jagrancin gwamnan jihar Bola Tinubu, wanda yanzu shi ne shugaban kasar Najeriya.

Wani mai amfani da shafin Facebook Okodoro Oro kwanan nan ya yi zargin cewa layin jirgin shi ne na biyu irinsa da ke aiki a yankin yammacin Afirka.

A cewarsa, “Lagos Blueline rail ya fara aiki yau a birnin Legas Najeriya. Wannan ne layin jirgi na biyu irinsa a yankin yammacin afirka bayan layin Abuja Rail Mass Transit.”

Daga biyar ga watan Satumba, masu amfani da shafin su su 85 sun mayar da martani kan batun yayin da mutane shida kuma suka raba labarin. Da DUBAWA ta kara bincike sai ta cewa akwai kafofin yada labaran da suka wallafa wadanda su ma mutane da yawa sun yi tsokaci a kai. Misali Anambra Current News ta sami tsokaci 101 mutane 261 sun yi ma’amala da labarin kuma wasu 21 sun sake rabawa. A shafin Beautiful Nigeria kuma an yi ma’amala da batun sau  487 tsokaci 36 an kuma sake rabawa sau 31

Wannan ne ya sa DUBAWA za ta tantance batun

Tantancewa

Mun sami bayanai da dama dangane da jirgin kasan Abuja da muka yi amfani da mahimman kalmomi a karon farko. Mun gano cewa an kaddamar  da shi ne ranar 12 ga watan Yulin 2018, kuma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci bukin. Babu kasar yankin yammacin Afirka da take da wannan abun more rayuwar kafin wannan lokacin.

To sai dai shirin wanda ya ci dalar Amurka miliyan 824 ya tsaya bayan da COVID-19 ya sa aka dakatar da sufurin fasinjoji. Har yanzu ba’a sake amfani da jiragen ba shekaru uku bayan tafiyar COVID-19.

A wannan lokacin, shekarar 2019, gwamnatin Ivory Coast ta sanya hannu kan yarjejeniya da  hadakar Kamfanonin jiragen kasar Abidjan. A lokacin ta na karkashin jagorancin Bouygues Travaux Publics, kuma yarjejeniyar ta bukaci gina layin dogo mai tsawon kilometa 37 a Abidjan babban birnin kasar ta Ivory Coast. Bacin haka, sai a watan Maris 2023 ne aka fara ginin kamar yadda muka gani a mujallar kasa da kasa ta jiragen kasa

Wasu kasashen da suka fara gina layin jirgin sun hada da Lome (Togo) da Kumasi (Ghana). Babu wata kasar yankin yammacin Afirka da ke da birni ko jihar da ke da jirgin kasa.

Wannan ne ya sa Lagos Blue Rail ya zama na biyu a yankin bayan da ya fara aiki ranar 4 ga watan Satumba. Bacin haka shi ne na farko a yankin da ke amfani da wutar lantarki.

A karshe

Duk da cewa layin jirgin ne na farko da ke amfani da wutar lantarki a yankin yammacin Afirka, shi ne na biyu idan ana irga jiragen. Abuja Rail Mass Transit ne na farko kuma wannan zargin gaskiya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button