African LanguagesHausa

Shin gaskiya ne timatiri da tafarnuwa na iya wanke al’aurar namiji?

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi:  Wani shafin facebook na zargin cewa ana iya amfani da timatiri da tafarnuwa a wanke bangaren al’aurar namijin da ake kira prostate da turanci, kuma yin hakan zai iya kare shi daga kamuwa da cututtuka musamman sankara.

<strong>Shin gaskiya ne timatiri da tafarnuwa na iya wanke al’aurar namiji?</strong>

Sakamakon Bincike: Babu hujjoji masu gamsarwa. Yayin da akawai binciken da ke nuna yadda timatiri da tafarnuwa ke dauke da sinadaran da ke inganta lafiyar alaura su kuma kare ta daga cututtuka, babu binciken da ke nuna cewa ana iya amfani da kayayyakin abinci a tare dan a “wanke al’aura.”

Cikakken bayani

Bangaren al’aurar namijin da ake kira prostate da turanci, gaba ce ‘yar karama wadda ta ke taimakawa namiji wajen haihuwa. Prostate na da siffa shigen gurjiya. Ana iya ganinta a cikin kugun namiji, a karkashin mafitsara a daidai gaban dubura. Prostate ya kan taimaka wajen sarrafa maniyi, shi ne ke samar da sinadarin nan mai kama da madara wanda ke daukar maniyi daga lunsayi (wasu kan kira shi gwaiwa) zuwa al-zakari inda ya kan fito bayan namiji ya kawo.

Alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa sankarar prostate shi ne nau’in cutar daji na biyu a cikin nau’o’in cutar da ke kasancewa ajalin maza bayan sankarar huhu. Wannan ne ya sa mutane da yawa suke gabatar da ra’ayoyinsu da dama dangane da yadda suke ganin ya kamata mutane su kaucewa kamuwa da cutar da ma hanyoyin da suke zargi ana iya amfani da su wajen wanke prostate din.

Wata mai amfani da Facebook, Eerifeoluwasimi, ta wallafa wani guntun bidiyo a shafinta kan yadda shan nikakken timatiri da tafarnuwa a kai-a kai zai iya wanke prostate.

A bidiyon mai tsawon minti daya da dakiku 46, an jiyo wani mutumi yana bayanin yadda ya ke da mahimmanci wa wadanda shekarunsu na haihuwa ya haura 40 su rika wanke prostate din su kuma san yadda ake nika timatiri da tafarnuwa. Ya ce a sa sala biyu na tafarnuwa da timatiri daya da mililita 500 na ruwa, ya ce kuma ba prsotate kadai ba ma wannan hadin na iya rage kumburi a cikin jiki ya kuma kare mutun daga kamuwa da cututtuka. 

Bidiyon wanda yanzu ya shiga kusa ko’ina ya sami alamar Like 990, an tsokaci 21 a karkashin labarin kuma an raba shi sau 709 daga ranan 5 ga watan Agusta sadda mu ka ga labarin.

Yawon da batun ya yi da mahimmancin batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ne ya sa muke so mu gudanar da bincike dangane da wannan batun.

Tantancewa 

Bisa sakamakon binciken da shafin Better Nutrition ya gudanar, timatiri na da sinadirai da yawa wadanda suke da kyau wajen inganta lafiyar prostate. Wannan haka ne sabida ya kunshi wani sinadarin da ake kira lycopene, wani sinadarin da ketaimakawa wajen kare mutun daga kamuwa da cutar sankarar prostate. Bacin haka ana danganta yawan cin timariri da raguwa a hadarin kamuwa da cutar sankara kuma sauran binciken da aka yi ma duk sun nuna cewa shi wannan sinadarin na lycopene zai iya jinkirta cigaban cutar BHP wanda kumburi ne a gwaiwa kuma ba shi da wata alaka da sankara.

Wani binciken da mujallar Pubmed ta yi ya nuna cewa mazan da suka fi cin abubuwa kamar albasa, tafarnuwa da albasa mai lawashi hadarin kamuwa da cutar sankarar ba shi da yawa.

Haka nan kuma, wani binciken da babban dakin karatu na Likitoci na kasa ya nuna cewa Tafarnuwa ya na da sinadaran da ke rage kumburi, rage hadarin kamuwa da sankara da kuma sinadaran da ke kashe cututtutuka ko hana su yaduwa yadda za su yi wa jikin mutun lahani. Haka ne ma ya sa na tsawon shekaru da dama yanzu, ake amfani da tafarnuwa wajen jinyar wadanda ke da cutar sankara na prostate da alamun BPH (kumburin gwaiwa) Sai dai wajibi ne a kara binciken da zai gano yadda aka yi tafanuwar ke yakar sankara da rage kumburi. 

Ra’ayoyin kwararru

Mun yi magana da Abiola Ayanbukola, wata likita a asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo wadd ta bayyana mana cewa ana yawan bai wa mai sankarar perostate shawarar cin timatiri da tafarnuwa, sai dai babu wani binciken da ya nuna cewa saboda “wanke prostate” din ne.

“Ina iya tabbatar mu ku cewa timatiri da tafarnuwa suna da tasiri mai kyau a kan kiwon lafiya har da na prostate, amma ba zan iya cewa komai dangane da wanke prostate ba domin ni ban taba ganin wanda ya ce ya yi hakan kuma ya yi masa aiki ba,” ta bayyana.

Doctor Busola Adebesin, ita ma likita a kasar Gambia ta goyi bayan cewa timatiri na dauke da lycopene, dan haka yana da sinadaran da kan yaki kwayoyin sankara. Ta kuma kara da cewa daya daga cikin hanyoyin kaucewa kamuwa da cututtuka irnín sankara shi ne gyara yadda ake cin abinci, a fi mayar da hankali kan abubuwa masu gina jiki.

Ga wadanda suke son shan giya da cin jar nama ya na da mahimmanci su koma ga cin ‘ya’yan itace da kayayyakin lambu. Timatiri, tafarnuwa, da wake duk abubuwa ne da ke inganta lafiya musamman na prostate kuma ana yawan bayar da shawarar cewa a rika amfani da su wajen yin abinci.

A Karshe

Yayin da timatiri ke dauke da sinadarin lycopene, wanda kan tare kwayoyin sankara, dole sai an kara yin bincike kafin a tabbatar cewa hada timatiri da tafarnuwa zai iya wanke prostate

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button