African LanguagesHausa

Karya! Babu wata hujja cewa kanumfari da tafarnuwa na   wanke mahaifar mace

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Kanumfari da tafarnuwa na tsaftace mahaifa

<strong>Karya! Babu wata hujja cewa kanumfari da tafarnuwa na   wanke mahaifar mace</strong>

Sakamakon binciken: KARYA NE! Mujallu sahihai na lafiya da kwararrun masanan lafiya sun ce babu wata sheda da ta tabbatar da hakan.

Cikakken bayani

Ba sabon labari ba ne kokarin gano sahihancin magungunan gargajiya ba kamar na Bature ba. Wani shafin Facebook mai suna Fertility guideline group, ya wallafa cewa kanumfari da tafarnuwa na tsaftace ko wanke mahaifa.

Shafin ya yi karin bayanin da ke cewa idan aka hada kanumfari da dakakkiyar tafarnuwa aka cakuda suka jiku aka sanya a firji, ana iya dimamawa a sha da safe kafin karin kumallo. Ko da yake za a iya sha lokacin da mace ke jinin al’ada a guji sha lokacin da mace za ta iya daukar ciki. Haka nan maza da ke da cutar sanyi suma suna iya sha.

Wani mai amfani da shafin na Facebook , Tomi Adenuga, shima yayi irin wannan da’awa.

Ya zuwa ranar 8 ga Disamba, 2023 wannan wallafa ta samu masu nuna sha’awa wato (Likes) 5,900 da masu tsokaci (Comments) 78 da wadanda suka yada (shares)2,000.

Ganin yadda labari ya yadu dama irin tasirinsa a tsakanin al’umma da lafiyarsu shafin DUBAWA ya shiga aiki tukuru don yin bincike.

  Tantancewa

A cewar Healthline, kanumfari na dauke da sinadarin eugenol, da ke yakar kwayoyin cuta a jikin dan Adam. Man kanumfari mai kyau na kashe kwayoyin cutar daji a makogwaro baya ga wasu fa’idoji da yake da su. Idan aka hada kanumfari da sinadarin nigericin suna daidaita yawan suga a jiki da kwarin kashi da yaki da cutar daji da kan shafi ciki.

Masu binciken lafiya na Medical News Today sun nunar da cewa amfani da kanumfari na rage teba da ke samuwa dalilin cin abinci da ke sa teba.

Binciken nasu ya kara da cewa shedu sun tabbatar da cewa bayan da aka rika ciyar da bera da abincin da ke da sinadarin na kanumfari ya rage kiba, da girman hanta fiye da barayen da ba a ciyar da su da abincin da babu kanumfarin.

Har ila yau wasu kafofi kamar Breathe Well-being da Verywell Health da MedicineNet, da Drug.com sun nunar da irin amfanin da kanumfari ke da shi amma babu wanda ya bayyana batun na tsaftace mahaifa ko wankin mahaifa.

Shin Tafarnuwa na wanke mahaifa?

A cewar Medical News Today, tafarnuwa na taimakawa jiki wajen yaki da cutar daji ta makogwaro da kansar kwakwalwa da ciwon makogwaro da bugawar zuciya da ciwon suga da rage yawan sinadarin cholesterol da hawan jini. Sauran kafofin kamar PharmEasy da Spice World, Everyday Health, Real Simple, da Health duk sun bayyan a ra’ayoyinsu kan amfanin tafarnuwa amma babu wanda ya bayyana cewa kayan ganyen na wanke mahaifa.

Me kwararru ke cewa?

A tattaunawa da Dr Victoria Shittu, kwararriyar likita mai fafutukar wayar da kan jama’a kan abubuwan  da suka shafi kwakwalwa ta yi watsi da wannan da’awa da ta bayyana da zama mara tushe.

”Ita mahaifa ba ta bukatar a wanke ta, halittace tsaftatacciya, sai idan an samu irin wadannan mutane (ma’ana mutanen da aka bayyana a sama) su bata ta” a cewar likitar.

Kwararriyar masaniya a fannin na lafiyar kwakwalwa ta kara jaddada cewa wanke mahaifa ba dole ba ne. Idan ma ta kama za a yi akwai hanyoyi na kimiyar kwararru da ake bi idan ma an samu wasu kwayoyin halitta da suka cutar da ita.

“Mahaifa ba  aba ce da ke a bude ba ga kwayoyin cuta, ba ta bukatar wanki. Ko da masu zubar da ciki ana bin kaidoji na likitanci da amfani da wasu magunguna na kashe cuta.” a cewar Dakta Shittu.

Dr Nathaniel Adewole, wanda ke zama kwararen likitan mata a Asibitin Koyarwa na Abuja shima yayi fatali da wannan da’awa da bayyana da cewa babu ita. A cewar kwararren likitan, “Bani da masaniya kan wannan a tsawon shekaru na na aiki.” 

Ya kara da cewa babu wani batu na wankin mahaifa, a ce wasu nau’ikan abinci don wankin mahaifa babu wannan batu. “A iya sanina.” A cewar likita Dr. Adewale.

A Karshe

Wannan da’awa karya ce. Babu  wani bincike na likitoci ko kwararru a fannin lafiya da ya goyi bayan wannan da’awa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button