African LanguagesHausa

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

A shekarar 2023 an samu bazuwar bayanai na karya a shafukan sada zumunta, wadanda suka yi tasiri a muhimman fannoni kamar na lafiya da harkokin kudade da ilimi da harkoki na nishadantarwa.

Jami’oin Najeriya ma ba a bar su a baya ba, an shafa masu irin wadannan labarai na gangan. A wannan makala DUBAWA ta zabo irin wadannan labarai na karya guda shida wadanda suka shafi makarantun don nazarin yadda irin wadannan bayanai ke tasiri a harkokin cibiyoyin na ilimi.

1. Tsarin samar da abinci kyauta a jami’ar jihar Kogi

Wani shafin Facebook yayi da’awar cewa a jami’ar jihar Kogi (KSU) ana ba wa dalibai “fufu da sabulu” kafin fara daukar darasi da safe.

Sai dai bayan gudanar da bincike daliban da masu gudanar da jami’ar sun karyata wadannan jawabai wadanda suka bayyana da zama na karya. Ana iya nazari kan irin wadannan bayanai a anan (here.)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Hoto: Jami’ar jihar Kogi. Hoton an dauko shi: Jaridar Premium Times.

1.  Turancin Borokin (Pidgin) a yanzu ya zama wajibi a jami’ar jihar Delta

Ba da jimawa ba bayan da ya wallafa labarin ba da abinci kyauta, sai kuma ya wallafa labarin “Amfani da Turancin Brokin (Pidgin) ya zama darasi na wajibi a jami’ar jihar Delta.”

DUBAWA bayan da ya tuntubi mahukuntan makarantar sun karyata bayanin. Ana iya nazari kan abin da aka binciko anan (here.)

Bayan bin kwakkwafin labarin, aka kuma wallafa abin da aka gano, sai mai shafin ya cire jawaban da ya wallafa dama wasu labaran a shafukan na Facebook. Ana iya ganin abin da aka cire a shafin a nan (here.)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Jami’ar jihar Delta, Abraka (DELSU). Inda aka dauko hoton: DELSU on Facebook.

1. Shirin daukar dalibai a Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti 2023/2024

A baya-bayan nan Adetunmobi Jibola, wani mai amfani da shafin Facebook, ya bayyana cewa ana ci gaba da daukar dalibai a shekarar karatu ta 2023/2024 a Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE). Inda ya nuna cewa yana da hanyar sama wa mutane gurbin karatu, ya kuma ba wa mutane tabbaci suna iya tuntubarsa.

Bincike kan wannan bayani ya gano cewa karya ne, kasancewar tuni aka rufe samar da guraben karatu ta hanyar UTME. Wadanda za su iya samun gurbin karatu da yayi saura dalibai ne masu nema kai tsaye kawai. Ana iya samun cikakken rahoto anan (here)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Jami’ar Tarayya  Oye-Ekiti. Asalin hoton: FUOYE Facebook page.

1.  Ranar dawowa karatu a Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti

Har yanzu dai akan Jami’ar ta FUOYE. Gyara a kalandar tsarin karatu na shekara, wannan aka yada a manhajar WhatsApp wanda ya nuna cewa za a koma harkokin karatu a ranar 3 ga watan Oktoba, 2023. Wannan na zuwa ne bayan da aka tafi wani hutu na sai baba-ta-gani, bayan da aka samu labarin kisan gillar wata daliba a makarantar.

Mahukunta a makarantar sun tabbatar da cewa babu wani shiri na komawa makaranta sabanin yadda wani ya kirkiri labarin, baya ga wannan kagaggen labarin aka kuma kirkiri kalandar tsarin karatu ta shekarar dalibai don a kara wa labarin zuma wanda duk karya ne. Ana iya kara nazari a nan (here.)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Jami’ar Tarayya ta  Oye-Ekiti. Inda aka samo hoton: Guardian.

1. Damar samun aiki a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Offa

A watan Satumba wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Kabiru Ibrahim ya wallafa da yada labarin cewa Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Offa na fadada ayyukanta inda ta bude kofar samar da guraben ayyuka na malamin kwaleji na 1 dana 2 da mai binciken kudi da masanin kwamfuta da mai kula da dakin karatu.

Shugaban kwalejin ya karyata wannan da’awa, inda ya ba da tabbacin cewa babu wani batu na daukar aiki a kwalejin. Ana iya kara nazari anan (here.)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Federal Polytechnic Offa. Inda aka samo hoton: Punch.

1. Jami’ar OAU ta tilasta tafiya hutu saboda Wasannin Kasashen Afurka ta Yamma na 2023

Labarai ne da yawa da suka bayyana ta manhajar WhatsApp da da’awar cewa Jami’ar  Obafemi Awolowo University (OAU) ta ayyana tafiya hutu daga ranar 15, Disamba 2023, zuwa 8 ga watan Janairu, 2024. Wannan hutu na da nasaba da daukar bakuncin wasannin kasashen Afurka ta Yamma (WAUG) na wannan shekara.

Sai dai a tattaunawa da jami’ai na makarantar sun karyata da’awar inda suka ce labarin ba shi da tushe. Ana iya neman karin bayani kan wannan batu anan ( here.)

Bayanai shida na karya kan jami’oin Najeriya

Obafemi Awolowo University. Inda aka samo hoton: OAU.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button