African LanguagesHausa

Karya; har yanzu mazauna garin Oye-Ekiti na fama da rashin wutar lantarki

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Ba’a taba dauke wuta a garin Oye-Ekiti

Karya; har yanzu mazauna garin Oye-Ekiti na fama da rashin wutar lantarki

Sakamakon bincike: Karya. Duk da cewa akwai cigaba wajen samar da wutar lantarki a Oye-Ekiti kwanan nan, ba gaskiya ne cewa suna samun wutar dare da rana ba kamar yadda ake zargi.

Cikakken bayani

Oye-Ekiti, garin da Jami’ar Tarayya ta FUOYE ta ke a jihar Ekiti, ta yi fama sosai da rashin wutar lantarki. A shekarar 2019, mazauna garin wadanda galibinsu daliban jama’a ne sun bayyana damuwarsu ta hanyar zanga-zanga wadda ta tabarbare ta kai ga tashin hankalin da ya yi sanadin rayukan dalibai biyu.

A sanarwar da aka yi kwananan nan a shafin, “FUOYE Campus Connectna X sun yi tsokaci dangane da sauyin da aka samu a fannin wutar lantarki a Oye-Ekiti, inda ma suke zargin cewa yanzu ana samun wutar lantarki babu kakkautawa, dare da rana.

“Wow! Wutar lantarki yanzu ko da yaushe a Oye-Ekiti. Lamarin wutar lantarki yanzu ya gyaru a Oye-Ekiti. Idan har ba ku riga kun dawo makaranta ba saboda matsalar wutar lantarki kuna iya dawowa yanzu. Muna samun wutar lantarki ko da yaushe kuma ba’a daukewa, Abun da muke bukatu yanzu daga wurin gwamnati shi ne ta gyara mana hanyoyinmu,” a cewar bayanin da aka wallafa.

Bisa la’akari da abun takaicin da ya faru a shekarar 2019 da kuma shakkun da wasu suka nuna cikin wurin da ake tsokaci dangane da batun, DUBAWA ta ga cewa ya na da mahimmanci ta tantance sahihancin wannan da’awar.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da yin hira da mazauna da ma’aikata a manyan yankunan garin guda shida ta wayar tarho. Yankunan sun hada da School Road, School Junction, Irona, Mini Campus da Idofin. Wadanda aka yi hirar da su kuma sun hada da masu kananan sana’o’i, da dalibai wadanda duk suka amince cewa lamarin wutar ya gyaru amma dukkansu suka ce ba’a samun shi dare da rana.

Da ya ke karin bayani dangane da batun, Precious Samuel wani dalibi wanda ke mataki na hudu a jami’ar ta FUOYE ya ce duk da cewa ana samun wutar fiye da aka rika samu a baya, ba gaskiya ne wai ana samu dare da rana ba tare da an dauke ba.

“Abun shi ne, idan har da ma ba’a samun abu yadda ya kamata, da zarar aka dan gyara, sai a ga kamar wata gagarumar sauyi aka samu, abun da ke faruwa ke nan a Oye yanzu,” ya bayyana.

“Akan sami wuta a wasu ranakun. Ko jiya an sami wuta amma bai dade ba kuma ma bai zo da karfi ba.”

Mr Samuel, mazaunn Idofin, shi ma ya tabbatar da karancin wutar lantarkin da ake samu a Oye-Ekiti. Ya ce cigabar da ake samu yanzu mataki ne da zai iya kaiwa ga lokacin da za’a sami wutar lantarkin ba tare da an dauke ba, wanda ya nuna cewa an fara samun sauyi a irin abubuwan da aka rika gani a baya.

“Ba na ji an taba kawo wutar da ta tsaya har ta kai sa’o’i 24 ko ma ta kai rabin hakan,” ya byyana.

Okeke Salvation ya na kula da wani wurin da ake zuwa cajin wayoyi ne a School Road, amma yana zama a Mini Campus. Ya watsi da batun ya ce wannan ba gaskiya ba ne, ya ma kara da cewa cigaban da aka samu bai ma kai inda ya ke zama ba wato can mini campus.

“Waye ke da lahakin yayata wannan shaci fadin?” ya tambaya.

“Watakila nan gaba. Jiya muna da wuta, amma can a Ile Jesu Oseun sun cigaba da fama da duhun kamar dai yadda aka saba.

Sai dai a cewar Silas Ayeni, shi ma dalibi a aji uku wanda ke zaune a yankin Irona,  ya ce lallai ana cigaba da dauke wutar a kai-a kai amma kuma akwai ranakun da wutar ke dorewa. Ya ce wutar ta ma taba yin sa’o’i 12 ba’a dauke ba. Ko da shi ke ya bayyana damuwar cewa mafi yawan lokutan wutar ba ta da karfi sosai.

“Mun rika samun wutar sosai a ‘yan kwanakin nan duk da cewa an rika dauke wa a wasu lokutan. Wutar kan wuce sa’o’i 12 wasu lokuta. Sai dai kawai wata sa’a wutar ba ta da karfi. Amma idan har aka kwatanta da yadda lamarin ya ke a baya a gaskiya an sami cigaba,” Mr Ayeni ya fadawa DUBAWA.

Da ta ke goyon bayan abin da Ayeni ya fada, wata dalibar ita ma Oluwadarasimi Agboola, ta bayyana cigabar da aka samu a fannin wutar lantarki a Irare, inda ta ke zama. Ta ce tsawon lokacin da akan dauka babu wuta ya ragu kuma yanzu a kan samu a dore lokaci zuwa lokaci, abun da ta kwatanta da “wuni daya da wuta, wuni daya babu.”

Haka nan kuma, Aisha Adeoye, wata mai sayar da lemun kwalba a tashar makaranta, wato School Junction, ita ma ta ce an sami cigabar.

“Sai dai ba su cika kawo wa da rana ba sadda muka fi bukata,” ta yi korafi.

Ranar 20 ga watan Nuwamban 2023, mai gudanar da wannan binciken ya ziyarci Oye-Ekiti da kansa, inda ya tabbatar da bayanan da wadanda ya yi hira da su suka yi sadda ya yi sa’o’i 24 a garin.

Duk da cewa yankuna irins School Junction, da School Road, da Faalex duk sun sami wutar lantarki amma na tsawon sa’o’i uku daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe goma. Bacin haka, yayin da aka kasance da wutar a duka sauran yankunan, a Mini Campus wutar ko daya ba ta da karfi.

Ko da shi ke, mazauna a wannan al’ummar sun bayyana gamsuwarsu da gyarar da aka samu inda suka rika tunawa da lokutan da aka yi fama da rashin wutar baki daya wata sa’a har ma a wuce makwanni biyu babu wutar.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa duk da cewa an sami cigaba wajen samar da wutar lantarkin a Oye-Ekiti, har yanzu ana dauke wutar a kai- a kai. Haka nan kuma wasu yankuna na fama da rashin wuta mai karfi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button