African LanguagesHausa

Karya! Hoton da ke yawo ba dan Najeriyar da ake da’awar ya biya bashin wani mai amfani da layin MTN ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: An kama dalibin da ya biya duk bashin da ake bin wani mai amfani da layin MTN

<strong>Karya! Hoton da ke yawo ba dan Najeriyar da ake da’awar ya biya bashin wani mai amfani da layin MTN ba ne</strong>

Sakamakon bincike: KARYA. Hoton da ake amfani da shi ana zargin wai dalibin nan ne da ya biya bashin wani mai amfani da layin MTN na wani dan Najeriyan ne daban wanda ake zargi da kisan kai a Landan a shekarar 2014. Haka nan kuma, bisa bayana jaridar Punch, “bashin da ak biya” tangarda ce ta na’ura ba wai an biya bashin ba ne da gaske.

Cikakken bayani

A watan Nuwamban 2023, masu amfani da layin MTN sun yi ta farin ciki da ma bukin “soke” wasu basussukar da aka yi wa masu amfani da layin MTN a kan shirinsu na XtraTime. XtraTime na barin masu amfani da layin su karbi rancen mintoci indan har kudin su ya kare kuma suna bukatar su yi waya cikin gaggawa.

Ranar Asabar 11 ga watan Disemban 2023, wani mai amfani da shafin Facebook, Update King, ya sanar cewa wani dalibi wanda ya je koyon aiki a MTN ya kuma biya bashin duk mutanen da suka karbi rance a kan shirin Xtratime, ya shiga hannun ‘yan sandan Najeriya.

“ ‘Yan sanda sun cafke dalibin nan da ya soke basussukan masu amfani da layin MTN sadda ya je koyon aiki a MTN.” Mai amfani da shafin ya bayyana.

Tare da bayanin, ya wallaga hoton wani mutumi mai kama da wanda ke da shekaru akalla 20 da ‘yan kai a tsakiyar ‘yan sanda biyu wadanda ke rike da shi a kowani gefe.

<strong>Karya! Hoton da ke yawo ba dan Najeriyar da ake da’awar ya biya bashin wani mai amfani da layin MTN ba ne</strong>

Hoton da aka kwafo daga shafon na Facebook

Tuni dai mutane 89 suka latsa alamar like a kan labarin yayin da mutane 54 suka yi tsokaci wasu kuma suka raba labarin sau 102, daga sadda ya wallafa labarin zuwa ranar 11 ga watan Disemba kadai.

Yawancin wadanda suka yi tsokacin sun bukaci da a sake shi ya koma gida.

“Ku sake shi kawai.” Dar Ling ya bayyana. “Idan kun yarda ku sake shi.” Uquaa Edison also ya roka.   

Kawo yanzu dai batun ya shiga kusan ko’ina a shafukan sada zumunta, har da Facebook, X da  TikTok

Dan sarkakiyar da irin wannan batun ke da shi ne DUBAWA Ta ce zata bincika ta gano gaskiyar lamarin.

Tantancewa

Mun ti binciken mahimman kalmomi a shafin Google, dan samun wani abu da ke dangantaka da kama mutumin da aka yi zargin ya biya basussukan, amma ba mu ga wani rahoto mai sahihanci dangane da batun ba. Sai dai mun ga wani rahoton da jaridar Punch ta wallafa ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

A rahoton, MTN ta amince da abin da ya faru kuma ta kwatanta shi a matsayin “tangardar na’ura” kamfanin ya  tantance matsalar da aka samu ya ce “kutse ne a bangaren na’urar da ake amfani da ita.” To sai dai basussukan da ake bin mutane na nan babu abin da ya sauya.

Mun kuma yi amfani da manhajar da ke tantance hotuna a google dan yin binciken kwa-kwaf a kan hoton, wanda shi kuma ya hada mu da wani rahoton ta jaridar Premium Times ta wallaga. A wannan rahoton, ta bayar da labarin wani dan Najeriya wanda aka bayyana sa a matsayin Jefferey Okafor, mai shekaru 23 na haihuwa wanda aka tasa keyarsa daga Landan a shekarar 2014 saboda ya bayyana a shari’ar da ake zarginsa da kisa.

Da ma Mr Okafor ya tsere daga Landan ne zuwa Najeriya bayan da aka gano cewa da hannunsa a kisan wani Carl Asiedu mai shekaru 19 na haihuwa wanda ke aikin Dijay a watan Augustan 2009. Sai dai a shekarar 2014, ‘yan sandan Najeriya suka gano Mr Okafor a Asaba babban birnin jihar Delta, sa’annan sika yi shirin mayar da shi can Landan din inda zai fiskanci shari’a.

<strong>Karya! Hoton da ke yawo ba dan Najeriyar da ake da’awar ya biya bashin wani mai amfani da layin MTN ba ne</strong>

DUBAWA ta tuntubi MTN da ma ‘yan sanda ta imel amma babu wanda ya amsa sakonnin da suka tura.

A Karshe

Hoton da aka yi amfani da shi ana cewa an kama mutumin da ya biya basussukan masu amfani da MTN ne ba shi ba ne, wani dan Najeriyar ne wanda ake zargi da kisan kai a Landan a shekarar 2014. MTN ya kuma fadawa jaridar Punch cewa ba’a biya wani kudi ba, matsala ce aka samu da na’ura.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button