African LanguagesHausa

Mazambata a Facebook na amfani da ‘auren bisa’ da nufin samun nagartattun zama dan kasa a Canada wajen yaudarar mutane

Getting your Trinity Audio player ready...

Rikicin tattalin arzikin da ya janyo wa Najeriya asarar nera triliyan 20, a cewar cibiyar da ke tallafawa wajen habbaka ‘yan kasuwa masu zaman kansu CPPE, shi ne turar da ya kai Omotoke (ba sunanta na gaskiya ba) bango, wadda ta fara tunanin barin kasar ta je kasar waje a wani mataki na dindindin. A cewarta koma ina ne za ta je, “Idan dai har ba Najeriya ba ce za ni saboda na gaji.”

Kamar Facebook ya ji tunaninta, nan da nan sai ta fara ganin tallace-tallace kan yadda za ta iya zuwa kasar Canada da matakan da ya kamata ta dauka. Daya daga cikin tallace-tallacen cewa ya yi mutun na iya aure ma ya sami takardun bisar nan take. Da ta ga haka sai ta bi tallar wadda ta kai ta ga shafin wani wanda ma yanzu ba za ta iya tunawa da sunansa ba. Hawaye ya riga ya fara cika idanunta yanzu.

“Na biya dalar Amurka $1,750 (N1,298,500 ko kuma N742/$ a kasuwannin kudin ranar 18 ga watan Afrilun 2023) zuwa ga wannan mutumin dan ya yi mun hanya. Bai karbi kudin baki daya a tashi daya ba; kadan-kadan na rika biya. Mun ja abun daga watan Janairu har zuwa 18 ga watan Afrilu kafin na fahimci cewa na zama mi shi banki ne kawai. Daga nan sai ya kulle ni daga shafinsa. Duk maganganun da muka yi ta Facebook ne domin bai so ya bani lambobinsa ba.”

‘Yan Najeriya da yawa suna barin kasar ko kuma ‘Japa’ kamar yadda ake kira yanzu — wadda wata kalma ce a harshen yarbanci da ke nufin “kubucewa” – sakamakon mawuyacin halin da kasar ke ciki da ma rikicin tattalin arziki da tsadar rayuwa. Tsakanin zabin da ake da shi cikin kasashen da mutane ke zuwa, Canada ce ta fi samun karbuwa wajen jama’a.

Bisa bayanan Hukumar Kula da masu gudun hijira da ‘yan kasa na Canada (IRCC) ‘Yan Najeriya 5,755 suka sami izinin zama na dindindin daga farkon shekara ta 2023 kadai, wanda ke zaman kari na kashi 32.5 cikin 100 idan aka kwatanta da wadanda suka sami izinin zaman a bara waro 5,345. ‘Yan Najerita akalla 15,595 suka koma Canada da zama a shekarar 2021. A shekarar 2022 wannan adadin ya karu da kashi 41.9 cikin 100 zuwa mutane 22,130.

A wani binciken da aka yi a shekarar 2020 a karkashin jagorancin Cibiyar Kidayar Afirka API daga cikin mutane 772 wadanda suka amsa tambayoyin binciken, wadanda suka riga suka bar kasashensu (120 or 15.5%) da ma wadanda ke tunanin yin hakan (652 or 84.7%), kashi 75 cikin 100 sun ce neman rayuwa mai inganci ne dalilinsu yayin da kashi 55 cikin 100 kuma suka ce suna neman kyakyawar makoma ne wa yaransu.

Kasar Canadar dai ta kasance wurin da mutane ke sha’awar zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ya fitar da shirin da ta kira Express Entry wanda ya fara aiki a shekarar 2015 dan rage yawan tsoffin da ke kasar na yankin arewacin Amurka. Shirin ya saukake wa baki hanyar shiga su zama sami matsayin ‘yan kasa na dindindin musamman idan har suna da kwarewar da za ta basu damar samun matsayin. Bisa bayanan Worldometer (shafin da ke tattara bayanan jama’a), matsakaicin shekaru na haihuwa a Canada yanzu shi ne 40.6 daga watan Oktoban Oct. 2023. Sabanin yadda a Najeriya yanzu matsakain shekaru na haihuwa shi ne 17.2.

Tayi mai kyalkyali

Mazambata a Facebook na amfani da ‘auren bisa’ da nufin samun nagartattun zama dan kasa a Canada wajen yaudarar mutane

Domin shawo kan tsarin Facebook ta yadda ba zai yi tasiri sosai a kan bincikenmu ba DUBAWA ta fara da binciken hanyoyin neman bisar Canada. Mun gano da yawa kamar nan da nan.

To sai dai kuma irin wadannan tallace-tallacen da ma sun sabawa dokokin talla na kamfanin Meta a abun da suka kira salon kasuwancin da ba su dace ba, ko kuma “Unacceptable Business Practices.” Bayanin da aka yi dangane da burin manufar ya nuna cewa”Masu talla ba su da hurumin yin tallar kayayyakin da aka san cewa za su yaudari jama’a ne kawai a rude su a karbe musu kudi ko kuma bayanansu na kansu. Muna yin haka ne dan mu kare wadanda ba su ji ba su gani ba daga hannun wadanda za su so su zambace su.”

Daga nan sai muka karanta irin tsokace-tsokacen da aka yi a karkashin tallar muka ga inda wasu masu amfani da shafin suka ce duk wanda ke da sha’awa ya tura musu sako kai tsaye. Daga cikin irin mutanen akawai Sam Charles da Barbs Opez Awolowo.

DUBAWA ta tura musu sakonni kai tsaya, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Barbs Opez Awolowo ne kadai ya amsa sakon

Tattaunawar da muka yi da shi ya kasance kai tsaye, nan da nan ya fadawa DUBAWA cewa kafin a fara, za’a bukaci $500 (N575,000, wanda ke zaman N1150/$ ranar 19 ga watan Oktoban 2023).

Bayan nan kuma ya fada mana cewa akwai wata tsohuwa wadda da ma ta ke da sha’awar irin auren.

Kamar dai yadda mazambata suka saba, sai ya fara kokarin gagguta abun ya na so mu biya da sauri, ya ma ba mu tabbacin cewa daga mun biya wannan kudin ba za mu sake biyan wani kudin ba, ya ma mance cewa shi ya ce kudin farkon zai bude mana hanyar zuwa matakin gaba ne, wanda ake sa ran zai ma fi matakin farkon tsada.

Bayan da muka roke shi muka ce ya ji tausayinmu saboda matsalar tattalin arzikin da muke fama da shi yanzu, sai ya yarda muka yi ciniki kan cewa a tsaya a kan $500 wanda 

Kafin sa’o’i 48 DUBAWA ta sake tuntubarsa ta ce ta sami $300 ko kuma N30,000 na fam din da za’a cika. Sai ya ce a tura kudin zuwa manajan sa ya ba mu lambar asusun wato 8066183676 on Opay mobile bank. Da muka duba bayanan asusun bankin sai muka ga cewa sunansa na ainihi shi ne Opeyemi Peter Babalola. Sunan ya yi kama da wanda ya sanya a Facebook: Opez (Opeyemi) da Barbs (Babalola).

Masu amfani da Opay sun tabbatar mana cewa lambar wayarsu akan maida ya zama lambar asusun bankinsu da zarar aka cire sifilin da ke gaba. Wannan na nufin lambar wayarsa ita ce  08066183676  tunda lambar wayar ce lambar asusun. 

Mun tabbatar masa cewa za mu biya kudin a mako mai zuwa.

Tun daga sannan ba mu sake tuntubarsa ba, ko da shi ke ya tura mana sakonnin tunatar da mu har sau biyu. Na karshe ranar biyu ga watan Nuwamba.

Da DUBAWA ta duba lambar a Truecaller (inda ake gano ainihi sunayen da aka yi wa lambobin waya rajista da su), tunda lambar da aka yi amfani da shi a bankin Opay din ke nan, sunan da ya bayyana shi ne “Ope Ope” tare da adireshin email kamar haka “Opeople381@gmail.com.” Wani abu guda da muka gano a wannan binciken shi ne yadda a ko da yaushe sunan “Ope” ya rika bayyana, kuma dama an saba gajarta sunan“Opeyemi” ne zuwa “Ope” .

Mazambata a Facebook na amfani da ‘auren bisa’ da nufin samun nagartattun zama dan kasa a Canada wajen yaudarar mutane
Hotonsa a shafin shi na Facebook
Mazambata a Facebook na amfani da ‘auren bisa’ da nufin samun nagartattun zama dan kasa a Canada wajen yaudarar mutane

Alamun zamba

Da DUBAWA ta fari bin diddigin wannan shirin, mun gano wadansu abubuwan da za su iya taimakawa wajen ganowa ko shafuka na mazambata ne. Yawanci tallar da akan yi su kan yo alkawarin bayar da damar sada mutun da abu (Kamar wata kila suna so su yi wani abun da ya wuce abin da suke talla, wata kila jima’i ko wata dangantaka) wa wadanda basu ji ba su gani ba.

Sai da tallar yawanci ba su da hanyar gano wadanda ke da sha’awa cikin sirri. A maimakon haka sai a kai mutun wasu shafuka na daban wadanda ke bayani kan yadda ake samun takardun zama dan kasa a Canada.

Bacin haka, mutun ba zai iya samun tallar haka nan kawai a cikin facebook ba, sai dai idan an wallafa shi a wani shafi. Dan haka tallar za ta iya kai mutun shafin da aka riga aka sa ne kawai kuma in ban da facebook din ba za’a iya samun shi a wasu dandalolin ba. Ba za’a iya amfani da tallar daga an latsa adireshin da aka hada sakon da shi ba.

Bacin haka, idan mutun ya yi kokarin tura sako ta kai tsaye, zai ta samun sakonnin da aka riga aka shirya har sai ya gaji.

Dan haka duk mai sha’awa ba shi da wani zabi tunda ba zai iya samun masu tallar kai tsaye ba, illa ya bi wadanda suka rubuta sako a karkashin tallar suna bukatar da a tuntube su kai tsaye.

Shin irin wannan auren ya halatta?

Ko da mutun wani jinsi ne, ana kulla yarjejeniyar aure tsakanin namiji ne da namce wadanda suke da izinin zama ‘yan kasa a kasar, da nufin samun bisa a matsayin baki ko bakon haure.

Sai dai an haramta yin hakan kuma ana iya hukunta mutun bisa tanadin dokar hukunta miyagun laifuka a sashi na 292 (R.S.C., 1985, c. C-46) domin an kwatanta shi a matsayin “auren zamba”. Wato karya, zamba, da boye gaskiyar auren ko yanayin zaman auren da gangar duk dalilai ne da za su sa gwamnatin Canada ta soke takardun izinin zama dan kasar – wani dogon mataki wanda ministan IRCC ya kaddamar.

Misali a shekarar 2019, sadda gwamnatin Canada ta karbe bisar karbe bisar  Yan Yang, wani dan asalin China wanda ya ke da izinin zama dan kasa tun shekarar 2010 bayan da ta gano cewa ya sami izinin ne sakamakon auren karyar da ya yi da Lisa Marie Mills.

Wasu karin mutanen da abun ya shafa

Biola* (Ita ma ba sunanta na gaskiya ba) Ita ma ta bi hanyar da a tunaninta ya fi dacewa ta nemi kudin tallafi dan ya taimaka mata. Sai dai ko ita ma ba yi sa’a ba, haka ta fada hannun masu zambar wadanda suka dade suna amfani da wannan salon a shekarar 2021 saboda ta yi “tunanin cewa wannan hanyar zai fi mata sauri.”

“Takardun makaranta na da kyau sosai, kuma a tunani na lokacin wannan hanyar za ta fiye mun a maimakon neman izinin zama ‘yar kasa kai tsaye. Har yau bana so mahaifi na ya san cewa na ya fada hannun masu yaudara domin ban san abun da zai faru ba.”

Chinonso* (shi ma ba sunan gaskiya ba) ya fi su karfin hali. Bayan da ya fada hannun masu yaudaran a 2021 sai ya sake. Wannan karon wani abokin shi ya taimake shi da wata mata ‘yar asalin India wadda ta yarda ta yi yarjejeniyar auren da shi.

“Idan da ba dan abokina ya shirya mun ba, da na sake yin kasada. Amma kudin da na yi asara ya jefa ni cikin bashi. Dole sai da na bar gida, ana ta mun dariya a gida saboda na yi asara garin yin garaje ina neman sauki.”

‘Ku tabbatar kun yi bincike’- Gargadin kwararre

Olufemiloye Ajiboye (Olu of Canada wato wani wanda ake wa lakabi da basaraken Canada), wanda ke bayar da shawara kan shige da ficce ya bukaci duk wadanda ke son zuwa Canada daga Najeriya su gudanar da bincike sosai kafin su sa kai domin su guji fadawa hannun mazambatan da makircinsu.

Ya ce samun izinin zaman kasa ta aure ya halatta, amma dole a bi kaida da sauran sharuddan da aka gindaya idan ba haka, duk wadanda abun ya shafa “za su sami hukuncin doka idan har aka gano cewa sun yi kokarin yin magudi.”

Ya ce, “Daya daga cikin hanyoyin da Canada ke yaki da irin wannan auren wanda aka san zamba ce cikin aminci, shi ne amfani da dokoki da manufofi masu tsaurin da suka fitar. Idan har wanda ka aura na dogaro da kai ne, dole ka cigaba da kula da shi/ita na tsawon shekaru uku ba tare da ya/ta yi aiki ba har zuwa sadda za su sami izinin kasancewa ‘yan kasa.”

Ya kuma ce hukuncin da kundin tsarin mulkin Canada ya tanadar wanda kuma IRCC ke aiwatarwa ya kunshi haramta bisa na tsawon shekaru biyar da kuma tasa keyar duk wanda/wadda aka kama da laifi a fitar da su daga Canada.

Domin kaucewa daga shiga hannun irin wadannan muiyagun, ya shawarci ‘yan Najerita da su yi bitar duk wani bayani daga suka samu musamman a soshiyal mediya, su tabbatar cewa kafafen da suke samun bayanan su masu sahihanci ne. Akwai dandaloli da dama a soshiyal mediya wadanda ke bayar da bayanai masu nagarta dangane da hanyoyin da ya kamata a bi cikin mutunci da aminci. Haka nan kuma duk wanda ke so ya shiga Canadar ya tabbatar ya yi amfani da jami’an da ke da lasisin yin hakan su kuma karanta manufofin shige da ficen kasar a shafukan  kasar.

Bayanin Edita: Mun sakaya sunayen wadanda abin ya shafa bisa dalilai na tsaro.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button