African LanguagesHausa

KARYA! INEC ba ta sake sauya wa ma’aikatanta a Abuja wajen aiki ba

Zargi: INEC ta sake tura ma’aikatanta dake aiki a sashen bayanai, sadarwa da fasaha na ICT zuwa wani wurin da ke wajen Abuja inda za’a sake gudanar da zabe

Sakamakon Bincike: KARYA. Babu wani bayani da ke alaka da wannan zargin a shafin INEC. A watan Agustan 2022 ne hukumar ta sake tura ma’aikatanta wasu wurare kuma ma tiransifa kawai ba dan zabe ba.

Cikakken bayani

Wani mai amfani da Facebook, John Nwaokorie, ya wallafa batun cewa  Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC)  za ta tura wasu daga cikin ma’aikatanta da keaiki a a sashen ICT gabannin sabon zaben da ake shirin gudanarwa.

“Watakila za’a sake gudanar da zaben shugaban kasa saboda sun fara tura ma’aikatan da ke aiki a sashen ICT a Abuja, da wadanda suka fito daga wani yanki, wuraren da suke tunani jam’iyyar LP na da magoyabaya,” wani bangare na abun da ya wallafa ya bayyana.

Mai zargin ya kuma kara da cewa sakamakon wannan sauyin wurin aikin, zuwa wani yankin da bai bayyana bam ma’aikatan da suka rage a sashen na ICT yanzu yawancin sun fito ne daga yankin arewa da na kudu maso yammacin kasar.

Kafin a bayyana hukunci karshe a shari’ar da aka yi dangane da zaben shugaban kasa (PEPT) of the Presidential Election Petition Tribunal (PEPT), wanda aka kammala ranar 6 ga watan Satumban 2023, an rika yin rade-radin cewa za’a sake gudanar da zaben shigaban kasa. Sai dai zaben ya danganci hukuncin da kwamitin da ke sauraron kararrakin zaben ya yanke.

Labarin bai dauki hankali sosai ba tunda a ranar Larabar 6 ga watan Satumba alamar Like 21 ne kawai sa’annan kuma akwai tsokaci 12. Sai dai wasu daga cikin masu tsokacin sun bayyana shakkarsu ne dangane da batun baki daya.

“Ko za ka iya sada ne da wanda ya yi maka wannan zanen? Ya yi aiki mai kyau wajen kokari yaudarar jama’a,” Michael Olajide ya bayyana.

“Mun sa idanunmu a kan dukkansu(.)” a cewar Martin Luther Agweye.

Saboda sarkakiyar da irin wannan zargin ke da shi ne ya sa muka yanke shawarar tantancewa.

Tantancewa

Mun fara da duba shafin  INEC amma da mu ga wani labari dangane da tura ma’aikata wani yanki ba a fannin labaran shafin.

Mun gano cewa sadda hukumar ta tura wasu manyan jami’anta wani wuri a ciki har da kwamishinoni da darektoci watan Agustan 2022 ne. Kafofin yada labarai irin su Punch, This Day, Daily Post, da The Sun duk sun dauki labarin.

Abun da ya fi mahimmanci kuma shi ne a cikin duka ma’aikatan da aka tura babu wanda ke aiki a ICT, duk daga wasu sassa na daban ne a huumar. Bacin haka, sauyin wajen aikin ko kum tiransfa ya shafi ma’aika ta yankunan arewa da kumakudu maso yammacin kasar ne sabanin zargin da mai shafin na Facebook ya so ya yi.

A halin da ake ciki dai yanzu INEC na shirin gudanar da zaben gwamna dana majalisar dokokin jiha a jihohin Bayelsa, Imo, da Kogi ne kadar kamar yadda ta baayyana a shafinta. Ba’asanar cewa za’a sake gudanar da wani zabe ba.

Mun kuma kira kwanishanan INEC da shugaban sashe bayanai da shugabana kwamitin bayanai da ilimantar da masu zabem Festus okoye dan neman karin bayani amma bai riga ya ba mu amsa ba.

A Karshe

Wannan batun karya ne. Babu wani bayani dangane da wannan zargin a shafin INEC. Haka nan kuma bisa bayanann kafafen yada labarai, a watan Agustan 2022 ne INEC ta yi wani abu makamancin wannan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button