African LanguagesHausa

KARYA NE! ba FUNAAB ce jami’a mafi martaba a mataki na biyu a Najeriya ba 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Abeokuta, Abeokuta (FUNAAB) Ita ce jami’a mafi kyau a mataki na biyu a Najeriya.

KARYA NE! ba FUNAAB ce jami'a mafi martaba a mataki na biyu a Najeriya ba 

Sakamakon bincike: Karya. Wani rahoton bayanan da Times ta wallafa kan makarantun jami’ar da su ka fi inganci a duniya ya nuna cewa wannan da’awar ba gaskiya ba ce.

Cikakken bayani

Ba sabon abu ba ne a ga mutane suna alfahari da irin cigaban da jami’o’in da suka je suke samu. Mahawara ce yawanci wadda ta kan ki ci ta ki cinyewa muddin aka fara ta dangane da ko wace jami’a ce ta fi inganci.

Wani mau amfani da shafi X Millennium.py (@the_millenium1), ya yi ikirarin cewa jami’ar FUNAAB ce mafi inganci a Najeriya a mataki na biyu.

“Tarihin FUNAAB. Daukakar zamaninmu, Jami’ar da ta fi inganci a Najeriya a mataki na biyu,” mai amfani da shafin ya rubuta.

Ya zuwa ranar da muka fara yin wannan labarin, 14 ga watan Nuwmanab 2023, Mutane 4,644 suka karanta labarin, 48 suka sake wallafawa, mutun uku suka ambaci batun yayin da wasu 170 suka latsa alamar Like.

Duk da cewa akwai wadanda ba su gamus da labarin ba, da yawa sun yi gaggawar amicewa.

While some X users doubted the claim’s authenticity, others quickly believed it.

“A ina kuka sami wannan labarin na jami’ar da ta fi inganci a mataki na biyu? In ji 

Enigma.eth (@enigma137x)

“Wannan ya yi kyau.” Lexzee (@devlexzee) ta ce.

To sai dai ganin irin sarkakiyar da batun ke tattare da shi, ya sa muka yanke shawarar tantance gaskiyar labarin.

Tantancewa

Da muka yi amfani da manhajar google dan gudanar da binciken mahimman kalmomi, mun gano wani rahoton da jaridar Punch ta wallafa, wanda ke dauke da jerin sunayen jami’o’i da martabarsu. Wannan rahoton ya sa jami’ar Ibadan a mataki na biyu.

Rahoton na Punch ta ce an sami wannan sakamakon ne bayan da aka yi amfani da salon auna martabar jami’o’i na World University Ranking wato WUR 3.0, wanda ke amfani da wasu mahimman abubuwa wajen tantance ingancin jami’a irinsu – koyarwa, yanayin bincike, ingancin bincike, fasahohi da himma, da kuma gogayya ko la’akari da matakin kasa da kasa.

Premium Times ma ta wallafa rahoto makamancin wannan.

Dan haka muka duba rahoton da aka samu daga Times Higher Education, wata kungiya mai zaman kansa wanda aka sani da wallafa batutuwa dangane da martabar jami’o’i tun shekarar 2004.

A nan ne muka gano cewa kungiyar ta sa Jami’ar Ibadan a bayan Jami’ar Covenant a shekarar 2024

Da muka cigaba da binciken mun ga cewa jami’ar ta FUNAAB ta na mataki na takwas ne tare da jami’ar Afe Babalola, Jami’ar Benin, Jami’ar Ladoke Akintola, da jamiar Legas da jami’ar Nnamdi Azikiwe da ta Obafemi Awolowo da kuma jami’ar Port Harcourt.

Ranking Web, wanda kuma shi ne shafin yanar gizo-gizo mafi girma wajen auna jami’o’i ya kan yio amfani da shafukansu na intanet da abubuwan da suke sanyawa a shafukan, da kuma irin kasidun da ake wallafawa daga cibiyoyin ilimin.

Bisa bayanann da shafin na Ranking Web ya wallafa a wannan shekarar ta 2023, Jami’ar Covenantce a mataki na biyu wadda ta zo a mataki na 1354 a dunita yayin da Jami’ar Ibadan ta zo na farko a mataki na 1207 a duniya.

A wannan jerin sunayen jam’i’o’in FUNAAB ta zo na 30 kuma a na duniya ta na mataki na 4,139.

DUBAWA ta kuma tuntubi masu wallafa shafin da ke tantance martabar jami’o’i na cikin gida wanda ake kira UniversityGuru dan samun karin bayani. Sai dai duk cewa sun goyi bayan wanda Times Higher Education ya fitar sun ce su ba su bayyana abun da suke amafani da shi su tantance martaba ko ingancin jami’a.

A karshe

Wannan batun ba gaskiya ba ne. Binciken Times Higher Education da Ranking Web sun karyata hakan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button