African LanguagesHausa

Kungiyoyin hadin gwiwa na binciken gaskiya sun samar da tallafin dala miliyan daya dan yaki da bayanan karya

Getting your Trinity Audio player ready...

Dan yaki da yaduwar bayanan karya a duniya baki daua, Kungiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa kan binciken gaskiya IFCN  da ke cibiyar Poynter ta sanar cewa ta bayar da tallafin dalar Amurka daya ga mutane 20 da suka cancanci samu a matsayin wani bangare na kudin da aka ajiye ($12million)  dan aikin da ya shafi tantance bayanai a duniya baki daya, wanda kuma aka tara da kudaden da aka samu daga Google da YouTube.

Poynter,  wadda ke zaman sananniyar cibiyar aikin jarida ta bayyana wadanda suka yi nasara a mataki na biyu wanda aka kira GROW ranar 13 ga watan Nuwamban 2023, Wadannan kudaden ana bayar da su ne dan tabbatar da habaka kwarewa, da gogayya da dorewar yunkurin da ake yi a matakin yankuna da kananan hukumomi.

Idan ba ku manta ba, DUBAWA na daha cikin wadanda suka fara samun kudaden a watan Oktoban 2022, sadda kungiyar hadin gwiwar ta IFCN ta fara bai wa kungiyoyi 10 daga kasashe takwas kimanin $450,000 a matsayin tallafi.

Bisa bayanan Angie Drobnic Holan, darektar IFCN, kudaden na da mahimmanci wajen inganta kawancen kungiyotin da ke bincike. Holan ta ce “Muna matukar farin ciki da bambance-bambancen da muke da shi a tsakanin mambobinmu da sabbin dabarun shirye-shiryen da dakunan labaran suka gabatar wadanda zasu fadada mana aikinmu su kuma kara tasirin aikin.”

Shirye-shiryen da aka baiwa kudin sun hada da abubuwa daban-daban daga kasashen duniya. Rappler wata kafar watsa labarai a Philippine wadda ke karkashin jogarancin wada ta sami lambar yabo na Nobel Maria Ressa, za ta yi amfani da kudin. Haka nan kuma ita ma jaridar USA Today za ta yi amfani da shi wajen yaki da bayanan karya a harshen Spanianci. Deutsche Presse-Agentur daga Jamus ita ma za ta horas da masu aikin binciken gaskiya a kafofin yada labaran kasashen Jamus, Austria, da Switzerland a kan AI ko kuma manhajar da ke kwaiwayon dabi’un dan adam.

Juyin mulkin da aka yi a Myanmar a shekarar 2021 ya sa Mizzima samar da sashen binciken gaskiya su ma dan yaki da bayanan karya, da kuma kudin da zai sa shirin ya dore a kungiyar domin shirin su ya ma kunshi ilimantar da ‘yan kasar dangane da mahimmanci da ma yadda ya dace a rika amfani da kafofin yada labarai.

Kudin na GROW ba ya zuwa da wasu bukatu masu tsauri, dan haka duk kungiyoyin da suka sami kudin za su iya amfani da shi wajen daukar ma’aikata, fadada shirin, kirkiro sabbin shirye-shiryen da za su haskakak aikinsu, horaswa, samun kudi, amfani da makaman aikin da kan taimaka wajen nazari, da habaka hanyoyin samun kudaden shiga da kuma shiga kawance da irin hadakar da za su kawo cigaba.

Kungiyoyin da suka karbi kudin GROW sun hada da Africa Check (Afirka ta Kudu) Asocciacion de Periodismo de Investigacion Ojo Publico (Peru), Belarusian Investigative Centre (Belarus), BOOM (India), Demagog.cz (Czech Republic), FastCheck Lab (Hong Kong), Fountain ARIJ International (Jordan), Krik (Serbia), La Diaria (Uruguay), Laksmusz.hu (Hungary), and Les Surligneurs (France). 

Sauran sun hada da Gidauniyar Maharat (Lebanon), Newtral (Spain), The Self-Investigation (the Netherlands), Vera Files (the Philippines), da Verify-Sy (Turkey).

Wannan sanarwar ta biyo bayan matakin farko da aka dauka na BUILD wanda ya bayar da tallafi ga wadanda suka sanya hannun amincewa da amfani da ka’idojin IFCN. Wannan matakin na GROW ya sake fadada matakan cancanta zuwa ga kungiyoyin da ba su sanya hannu ba, muddin suna da goyon bayan kungiyoyin da suka riga suka sanya hannu, kuma shirin da suke so su gabatar zai kawo cigaba mai ma’ana ne ga shirye-shiryen da ke da alaka da binciken gaskiya.

Yanzu da ake shirin zuwa mataki na uku wanda shi kuma ake kira shirin ENGAGE, kungiyar za ta fara karbar takardun nuna sha’awa daga daya ga watan Disemba zuwa 8 ga watan Janairu, kuma wannan zai mayar da hankali ne a kan samun gudunmawar al’umma. IFCN na shirin gudanar da wani shirin da zai kunshi tambayoyi da amsoshi ranar 13 ga watan Disemba domin shawon kan duk matsaloli da ma tambayoyin da jama’a ke da shi a kan kudaden da za’a bayar a matakin ENGAGE.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »