African LanguagesHausa

Kwararru sun tattauna dabarun inganta hanyoyin samar da bayanai ga jama’a dangane da kafafen yada labarai a Afirka

Getting your Trinity Audio player ready...

Domin karrama zagayiwar ranar kafafen yada labarai da karatu, DUBAWA, shirin tantance gaskiya ta Cibiyar Aikin Jarida Sabbin Dabaru da Cigaba wato Centre for Journalism Innovation and Development (CJID), ta tara kwararru a kan shafin X ranar 26 ga watan Oktoban 2023 dan tattauna batutuwan da suka shafi kafofin yada labaran Afirka da bayanai dangane da karatu.

A karkashin jagorancin Silas Jonathan, mai gudanar da bincike a DUBAWA, tattaunawar ta kunshi shahararru irin su Chidoh Onumah, dan jaridar kuma mai koyar da aikin jarida, Aurelia Ayisi, babbar malama a sashen nazarin sadarwa da ke Jami’ar Ghana, Akintunde Babatunde, shugaban shirye-shirye na CJID da Prscilla Amoah wadda ta kammala karatu a Jami’ar Kafafen Yada Labarai, Fasaha da Sadarwa (tsohuwar cibiuyar nazarin aikin jarida ta Ghana)

Mutane fiye da 600 suka shiga taron yayin da masu gabatarwar suka musayar ilimi suka kuma duba batutuwa kamar karatun da ya danganci hanyoyin amfani da intanet, tantance gaskiyar bayanai da ma dabaru inganta aikin jarida mai sahihanci.

Yaki da bayanan karya

Ms Aurelia ta yi bayani dangane da banbancin da ke tsakanin lakantar hanyoyin amfani da yanar gizo-gizo, kafofin yada labarai da kuma sanin bayanai. Ta bayyana cewa “Iya amfani da yanar gizo-gizo ko kuma digital literacy shi ne amfani da fasahohin yanar gizo yayin da fahimtar kafofin yada labarai kuma ke nufin nazari da tantance sakonnin da ake sanyawa a kafofin yada labarai. Haka nan kuma bayanai na nufin mayar da hankali wajen ganowa, nazari da kuma samo bayanai. Fahimtar Kafofin yada labarai da bayanai shi ne abun da za’a iya amfani da shi wajen kwatanta wadannan batutuwan.”

Mr Babatunde shi kuma ya duba dangantakar da ke tsakanin fahimtar kafofin yada labarai da tabbatar da cigaba mai dorewa. “Samun bayanai na taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama wajen samar da cigaba mai dorewa, ksmst kiwon lafiya, ilimi, noma, da ma damammaki na inganta karfin tattalin arziki. Bacin haka, ya na da mahimmanci wajen bai wa mutane irin makaman aikin da suke bukata wajen tantance duk wani bayani da suka samu,” ya bayyana.

Ms Amoah ta bayyana na ta ra’ayin dangane da yadda matasa suke da kwarewa wajen kafofin yada labarai da bayanai musamman a harkokin sabbin fasahohin zamani na yanar gizo. “Babu wanda ya yi shiri a harkar fahimtar harkokin yada labarai , musamman idan ya zo batun sadarwa,” ta bayyana. “Aikin ‘yan jarida ne su tabbatar da sahihancin duk wani bayani da za su gabatar.”

Gudunmawar nazari wajen inganta fahimtar bayanai da kafofin yada labarai 

A tattaunawar da aka yi dangane da kafofin yada labaraiu da fahimtar bayanai, an mayar da hankali kan irin gudunmawa da nazari mai zurfi zai iya bayarwa wajen inganta wannan fannin mai mahimmancin gaske.

“Ya kamata masu karantarwa su yi amfani da hanyoyin koyarwa da fahimtarwa daban-daban su kuma yi kokaro su saje da irin sauye-sauyen da ake samu idan ya zo batun bayanan da kafofin yada labarai ko kuma na sadarwa,” Ms Aurelia ta battana. “Koyo ta hanyar gwada abubuwa kai tsaye, wanda ya kunshi fahimtar abubuwa ta hanyar aiki da su ta kai tsaye shi ne mafi mahimmanci. Tilas ne masu karantarwa su zama wadanda ke shirye a kowani lokaci su dauki matakan da za su saje da sauyin da ake samu akai-akai su kuma zama wadanda ke inganta saninsu a ko da yaushe.”

Mr Onumah shi kuma ya jaddada mahimmancin dabarun shawo kan bayanan karya. A cewarsa, “Gwamnati na da rayawa takawa wajen inganta kafofin yada labarai da fahimtar bayanai. Gina dakunan karatu zai iya kowa bayanai kusa da al’umma. Dole mu kirkiro abun da zai kalubalanci kafafen yada labarai, ya yaki bayanan karya ya kuma hada bayanan kafofin yada labarai da irin wadanda ake koyarwa a makarantu dan inganta ilimin matasa.” ya kuma bayyana mahimmancin da ya ke da shi a ce gwamnati ta taimaka wajen gina manyana dakunan karatu da ma dai duk wadansu matakan da al’umma ke dauka dan gina dakunan karatun da hama’a za su iya amfani da shi su sami bayanai a tafin hannunsu.

Yayin da ya ke bayyana shirye-shiryen CJID masu yawan gaske wadanda suka taka rawar gani a wannan gannin a Afirka baki daya, Mr Akintunde ya yi kira da a zuba jari wajen tabbatar da cigaba sa’annan kuma a samar da hadin gwiwa tsakanin duk masu ruwa da tsaki.

Ya ce, “muna banbanta tsakanin masu rubuce-rubuce a taskokun Blogs da influencers na soshiyal mediya da ‘yan jarida. Baya ga kafofin yada labarai da bayanai, ya kamata mu yi la’akari da dalilin da ya kan tura mutane su nemi bayanai. Idan za mu yi haka, dole mu yi binciken da zai bayyana mana inda masu ruwa da tsaki su ke, mu tattauna da masu karfin fada a ji da influencers a kowani mataki, hatta shuwagabannin addini. A ko da yaushe muna zuba jari kan rahotannin da ke gudanar da bincike da dandalolin da ke kan yanar gizo-gizo ta yadda za mu inganta hanyoyin samun bayanai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button