Zargi: Bola Tinubu na bayar da N25,000 a matsayin kudaden zaben shugaban kasa, kamar yadda wani sakon WhatsApp ke zargi.
Sakamakon Bincike: Karya. Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu ya kira sakon “labarin bogi”
Cikakken bayani
Bayan da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta ce Bola Ahmed Tinubu na APC ne ya lashe zaben shugaban kasa ne wani sako ya bayyana a WhatsApp yana zargin wai Tinubun na raba wani N25,000.
Wannan sakon ya bayyana ne a shafukan sada zumunta na Laberiya, abun da sanya DUBAWA tunanin ko har ‘yan Laberiya za su iya samun kudin ko kuwa dai na ‘yan Najeriyar da ke rayuwa a Laberiyar ne.
Daga nan ne DUBAWA ta bi diddigin sakon na WhatsApp, dan ganin ko zata gano mafarin shi
Tantancewa
DUBAWA ta tuntubi kwamitin da ke kula da yakin neman zaben Mr. Tinubu, wato PCC wanda ya karyata zargin.
Hope Obeten, wanda ke zaman mamba na PCCn ya ce “Ku ne mutane na uku da ke jan gankali na ga wannan batun kuma zargin da wanann shafin ke yi karya ne.
DUBAWA ta latsa wannan adireshin na zuwa shafin da ake yadawa a sakon na WhatsApp sai dai kamar shafin ba ya aiki kuma ba ya ma kai ka zuwa wani shafin na daban.
A Karshe
Dan haka wannan labarin da ke cewa Mr. Tinubu ya bayar da N25, 000 ba gaskiya ba ne!