Getting your Trinity Audio player ready...
|
Juyin mulkin Jamhuriyar Nijar ya janyo sabani tsakanin kasar da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Yammacin Afirka wato ECOWAS. Juyin mulkin wanda ya yi sanadin hambarar da shugaban kasar da aka zaba bisa turbar dimokiradiyya, Mohammed Bazoum, ya yi sandin takunkumi daga kungiyar inda ta umurce duk kasashen kungiyar su rufe iyakokinsu da Nijar.
Daga baya an koka aka kuma roki ECOWAS ta dakatar da takunkumin da ta sanya, sai dai wannan ya zo ne bayan da kasashen Mali da Burkina Faso suka janye daga kungiyar baki daya suka kuma girka wata kungiyar ta daban wadda ta kunshi kasashen da ke karkashin jagorancin sojojin da suka yi juyin mulki a kasashensu.
Dakatar da takunkumin da aka yi, ya sa Najeriya bude iyakarta da Nijar, to sai dai ita Nijar din ba ta bude na ta iyakar ba har sai da aka shafe mako daya bayan Najeriya ta bude na ta.
Wannan matakin na Nijar ya haifar da mahawarori dangane da yadda kasar za ta rayu idan har babu hanyar shigar da kayayyaki tunda ba ta gabar ruwa.
Dan nuna cewa kasar za ta iya rayuwa ba tare da kayayyakin da ke shigowa daga Najeriya ba, wani mai amfani da shafin X, Sy Marcus Herve Traore, ya wallafa a shafinsa na X din ranar 19 ga watan Maris cewa ana gyara madatsar ruwan Kadandaji a Jamhuriyar Nijar.
Masu mana bincike sun yanke shawarar tantance gaskiyar wannan batun ne dan yaki da bayanai marasa gaskiya da wadanda ke yaudarar jama’a.
Da’awa 1: Mai amfani da shafin X (@marcus_herve), Sy Marcus Herve Traore, ya yi amfani da wani hoto na madatsar ruwan Kandadji da ke jamhuriyar Nijar ya na ikirarin cewa an kammala gina ta.
Hukunci: Karya ce. Da muka bincike shafin samun hotuna na kyauta mai suna Shutterstock mun gano cewa hoton madatsar ruwan Gariep ne a Afirka ta Kudu ba Kandadji ba.
Takaitaccen bayani kan madatsar ruwan Kandadji
Wani rahoto daga HumAngle ya bayyana cewa madatsar ruwan na kusa garin da ake kira Kandadji a yankin Tillaberi da ke jamhuriyar Nijar.
Shirin ya sami tallafi ne daga Bankin Duniya, Bankin Bunkasa Afirka, the Hukumar Cigaba ta Faransa da Bankin Islama kuma an kashe euro biliyan 1.1.
An fara gina madatsar ruwan ne a shekarar 2008 a zamanin Mamadou Tandja. Wani kamfanin Rasha mai suna Zaroubegevodstroï (ZVS) aka bai wa kwangilar, amma daga baya wani kamfanin China mai suna Gezhouba Group Company Limited, ya fara ginawa.
An dade ana kara wa’adin kammala madatsar ruwan, amma a yanzu ana sa ran kammalawa a shekarar 2025 sakamakon tsaikon da aka samu sadda aka yi fama da cutar COVID-19.
An sake dakatar da ginin sakamakon juyin mulki da ma takunkumin tattalin arzikin da ECOWAS ta dora wa kasar.
Daga 28 ga watan Maris 2024, mutane sun kalli labarin sau 692,600 sa’annan akwai tsokaci 410 an sake rabawa sau 1,300 rda kuma alamar like 3,100.
“Kuna ganin wannan? Wannan ita ce madatsar ruwan kandadji wadda ake aiki a kai. Zan fadawa ‘yan Najeriya masu yawan surutu kuma wadanda ba su san komai ba sai fadin rai suna bata lokacinsu a yanar gizo suna cewa Najeriya da ECOWAS duk ba su karuwa da Nijar…,” ya bayyana a cikin sakon.
Tantancewa
Mun sa hoton a manhajar tantance hotuna ta Reverse image search muna amfani da Tineye, sakamako 44 suka bayyana har wanda ya fito daga manhajar hotunan kyauta na wani kamfanin Amurka mai suna Shutterstock.
Sakamkon kuma ya bayyana mana cewa an fara ganin hoton ne a shafin hotunan kyautan na Shutterstock. Bincikenmu ya nuna mana taken da aka yi wa hoton wato “Dam Wall.” Michael Potter11 ya dauki hoton wanda aka wallafa ranar 24 ga watan Satumba 2012.
Duk da cewa wannan shafin bai bayyana ainihin inda madatsar ruwan ya ke ba, da muka sake bincike a Google mun gano cewa madatsar ruwan Gariep ne da ke Afirka ta Kudu.
Hotunan na Griep wadanda aka sa a shafin X na gwamnatin Afirka ta Kudu, da Flickr, da Alamy duk sun yi kama da wanda muka gano a shafin Shutterstock.
Sauran sakamakon da muka gani sun nuna cewa ana yawaon amfani da hoton a shafukan intanet inda ake danganta shi da labarai daban-daban masu alaka da madatsun ruwa kamar yadda muka gani a nan, nan da nan. ,
A Karshe (Da’awar farko)
Wannan hoton ba madatsar ruwan kandadji ba ne, wani hoto ne aka dauko daga shafin hotunan kyauta na Shutterstock. Wannan madatsar an riga an gama ta, Kandadji ko har yanzu ba’a kai ga kammalawa ba.
Da’awa 2: Shin Najeriya ta sa hannu kan wata yarjejeniya da Nijar dan ta hana ta gina madatsar kan kogin Neja a sheakarar 2020
Hukunci: Yaudara.
Ciakken bayani
A matsayin wani bangare na labarin da ya wallafam Traore ya yi da’awar cewa a shekarar 2020, Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar da ta hana ta gina madatsar a kn kogin Neje.
“A watan Yulin 2020, a karkashin gwamnati a karkashin jagorancin @MBuhari ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta hana ta gina madatsar ruwa a kogin nNeja. To me ya faru? Sun sa hannu kan yarjejeniya shi ya sa yanzu Najeriya ke bai wa Nijar wutar lantarki,” ya rubuta.
Tantancewa
Mun fara da binciken mahimman kalmomi a google inda muka yi amfani da “Nigeria signed an agreement with Niger not to dam river Niger.” wato “Najeriya da Nijar sun sanya hannu kan yarjejenita dan kada Nijar ta yi dan a kogin Neja” daga nan labarai biyu suka fito, daya a shafin Daily Trust wani kuma Vanguard.
A watan Yulin 2020 jaridun biyu suka wallafa labarin, kuma duka biyu sun ambaci wani furucin Malam Garba Shehu ne wanda ya kasance, mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ya na fayyace batun bashin wutar lantarkin da Najeriya ke bin kasashen Nijar, Togo da Benin.
Malam Shehu a cikin sanarwar cewa ya yi Najeriya na kai wutar lantarkin zuwa kasashen ne a matsayin wata yarjejeniyar hadin gwiwa tsakaninsu dan kada su gina madatsa a kan kogin Neja domin daga nan ne ake samun lantarkin da ke samar da wuta a madatsun Kainji, Shiroro da Jebba.
Ya ce an sake yin bitar yarjejeniyar a shekarar 2019.
Yayin da ba’a iya tantance sadda Najeriya ta sa hannu kan wannan yarjejeniyar da Nijar kan sa madatsa a kogin ba, kasashen biyu na kokarin shawo kan rikicin da ka iya tasowa ta Niger Basin Authority ko kuma kungiyar kasa da kasa da ke sa ido kan yadda kasashen yankin ke amfani da ma’adinansu dan inganta rayuwar al’ummominsu da tallafawa juna. Yarjejeniyar farko da suka kulla a shekarar 1963 ne, inda daga nan suka cigaba da yin wasu a shekaru 1964, 1980 da 2008.
A Karshe (Da’awa ta biyu)
Da’awar cewa Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakaninta da Nijar dangane da gina madatsa kan kogin Neja a shekarar 2020 yaudara ce kawai. Yarjejeniyar farko sun sanya sannu ne a shekarar 1963 kuma an shafe shekaru ana bitarsu, na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2019.
An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA 2024 a karkashin shirin Kwame Karikari, tare da hadin gwiwar jaridar Daily Trust, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.