African LanguagesHausa

Nasboi mai yin bidiyoyi a tiktok bai mutu ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Tiktok ya ce wai mai yin bidiyoyin tiktok din nan kuma mawaki Nasiru Bolaji, wanda aka fi sani da nasboi ya riga mu gidan gaskiya.

<strong>Nasboi mai yin bidiyoyi a tiktok bai mutu ba</strong>

Sakamakon binciken: Karya! Mawakin ya sanya kadan daga cikin sabuwar wakarsa a shafi Instagram sa’o’i kadan bayan da aka yi labarin mutuwarsa, kuma tun lokacin bai daina wallafa abubuwa a shafin ba.

Cikakken bayani

A ‘yan shekarun nan, a kasashen duniya mun ga yadda aka rika samun bayanan karya dangane da mutuwar wadansu taurari musamman jaruman fina-finai da sauransu. Shafukan soshiyal mediya ne suka taimaka wajen habbaka wannan yayin da ya bulla. A yawancin lokuta, da yawa wadanda ba su ji ba su gani ba sukan yadda da irin wadannan labaran kafin daga baya su kula cewa karya ce kawai.

Wannan batun ya zama abun damuwa sosai ga masu ruwa da tsaki da wadanda ke irin ayyukan da kan sa su a labarai ko da yaushe, wadanda su ne yawanci akan yi zargin sun mutu.

A shekarar 2023, alal misali, DUBAWA ta yi nazarin wasu daga cikin irin wadannan taurarin da abin ya shafa.

Ana danganta wannan da abubuwa da yawa, kamar yaudarar jama’a, neman suna da kuma daukar hankalin jama’a.

Kimanin makwanni biyun da suka gabata, jaruman fina-finan Nollywod, Ngozi Ezeonu, ta zama daya daga cikin irin wadanda wannan abun ya shafa. Rahotanni daga wasu shafukan soshiyal mediya kawai suka fara bulla na cewa mai shekaru 58 din ta riga mu gidan gaskiya kuma har dan ta ya tabbatar da hakan.

Sai dai a shafinta na Instagram, jarumar ta karyata zargin ta kuma yi gargadi ga “wadanda ke yayata mutuwarta ba tare da hujja mai kwari ba.”

Kwanan nan kuma wani mai amfani da TikTok @speed_akpi ya yi zargin cewa mai kirkiro bidiyoyi ya wallafa a soshiyal mediya Nasboi ya mutu. ya kuma danganta mutuwarsa da damuwa.

“ Labari da dumi-dumi: Nasboi ya mutu yau da safe sakamakon damuwa. OMG Na kasa yadda, Jesus,” abun da ya rubuta ke nan karkashin wani bidiyon da ya wallafa a shafin TikTok.

Na farko dai DUBAWA ta gano cewa shafin na da mabiya 60 ne kawai, kuma ya na kwaikwayon shafin Speed Darlington, mawakin Najeriya, mai barkwanci kuma influncer na soshiyal mediya.

Mai amfani da shafin na da’awar wai shafin na Darlington ne. Wani mai amfani da shafin X ne ya ga bidiyon, ya sake  wallafawa ya nemi a tantance masa sahihancin bidiyon.

Bisa la’akari da mutanen da aka ambata da kuma yiwuwar labarin ya yadu ta yadda zai zama da lahani ga al’umma ne ya sa DUBAWA ta ce za ta tantance labarin.

Tantancewa

Da DUBAWA ta duba shafin na Instagram na Nasboi, sai ta kula cewa ya wallafa bidiyo wuni gida bayan da aka yi zargin mutuwarsa. Ranar 15 ga watan Janairun 2024 aka yi zargin kuma bayan nan ya wallafa wasu karin bidiyoyin a shafinsa na kansa. Kamar yadda muka gani a wadannan shafukan, nan, nan, da nan

Nasboi ya yi suna sosai tun bayan da ya yi wakar ‘Umbrella,’ wanda ya yi tare da mawakin najeriya shi ma,  wanda aka fi sani da Wande Coal. 

Ya kaddamar da abun da ya kira kalubalen umbrella, ko kuma  #umbrellaopenversechallenge kamar yadda aka fi sani a duniyar soshiyal mediyan dan wakar ta sami karbuwa, inda ya gayyaci ‘yan Najeriya ya ce su nuna irin fasahar da suke da shi wajen amfani da kalamai da kidin wakar su yi bidiyo.

Nasboi ya yi kokari sosai wajen wallafa yawancin bidiyoyin da ya samu daga wannan kalubalen.,

Ranar 17 ga watan Janairu– wuni biyu bayan da aka ce wai ya mutu – mawakin ya shiga shafin X ya na kira ga ma’abotansa da su bayyana ra’ayoyinsu dangane da shirin da ya ke so ya gabatar. Har ila yau, babu wani bayani mai cewa haka a manyan kafofin yada labarai wadanda aka san suna da sahihanci, da ma dai sauran taskokin blog na masu rubuce-rubuce a kasar.

A Karshe

Zargin cewa nasboi ya mutu karya ne kawai. Mawakin ya na nan yana tallar wakarsa mai suna “Umbrella” da ma abun da ya ke shiryawa a Soshiyal mediya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button