Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe rassan bankin UBA guda shida

Hukunci: Yaudara ce! Gwamnatin ta karyata wannan da’awar a cewarta babban ofishin ne aka rufe ba shida kamar yadda ake yadawa ba dan haka yaudara ce kawai.
Cikakken bayani
Kadan daga cikin labarin da muka tsakuro daga shafin DCL Hausa na cewa:
Hukumar tattara kudaden haraji na cikin gida wato KADRIS wadda aka fi sani Kaduna State Internal Revenue Service da turanci, ta rufe rassan bankin UBA guda shida da ke Kaduna ne bayan hukumar gudanarwar bankin ya gaza biyan harajin da ake bin su, duk da takardun tunatarwar da hukumar ta aika masu lokuta daban-daban.
Sakataren Majalisar Gudanarwar kuma mai bada shawara kan shari’a ta Kaduna State Internal Revenue Service (KADRIS), Barista Aysha Muhammad da rakiyar jami’an tsaro ta jagoranci rufe rassan bankin.
A cewarta, hukumar ta dauki matakin da nufin karbo bashin kudaden haraji Naira 14,367,344.20k da suke bin bankin daga shekarar 2018 zuwa 2021, kamar yadda dokar hukumar ta tanadar.
Ganin yadda wannan labarin zai iya tayar da hankalin jama’a ya haddasa husumi ne ya sa DUBAWA ta ga ya dace a tantance gaskiyar wannan labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken da’awar a cikin manhajar tantance labarai da hotuna. Sakamakon binciken ya nuna cewa an wallafa wannan da’awar a ranan 24 ga watar Afrilu 2024 a shafukan Facebook da Instagram. Inda DUBAWA ta gano da cewar jaridun DCL Hausa, da Legit Hausa ne kadai suka wallafa labarin a shafukansu na facebook sauran manyan shafukan yada labarai ba su wallafa wannan labarin ba, illa wata shafin mai suna Ajeeborters_family a instagram.
Daga nan, DUBAWA ta kuma tattauna da wasu ma’aikatan bankin UBA a nan jihar Kaduna, wadanda kr aiki a babban ofishin UBA na jihar, sun tabbatar da cewar karya ne ba’a kulle rassa shida na banki ba, babban ofishin wato hedikwatar bankin a Kaduna ne kadai aka rufe a ranar Laraba 24 ga watan Afrilu 2024. Sun shaida wa DUBAWA cewar lallai an rufe babban ofishin da safe amma shi kansa an dawo an bude ba dadewa bayan an rufe ba, wato da misalin karfe goma na safe.
Hakazuluka DUBAWA ta kara garzayawa rassan banki da ke yankin kudancin jihar dan gani da ido, a nan ma ma’aikatan sun kara tabbatar mana da cewa babban ofishin su ne kadai aka rufe da safe amma an bude shi ba da daddewa a safen.
Duk da haka domin samo karin bayani, DUBAWA ta sami jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KADRIS Jamil Zakari ta tattauna da shi, inda ya shaida mana lallai da gaske sun rufe rassan UBA shida a jihar kuma sun yi bisa ka’idar kotu domin akwai yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsu dangane da wa’adin da aka basu na biyan kudin da ake binsu, amma a cewar Zakari har ranar ta zo ta wuce ba su biya ba.
Da muka tambaye shi sunayen bankunan da aka rufe ranar 24 ga watan Afrilun, bai ba mu ba, sai dai ya dauki hoton dokar da kotu ta basu wadda suka yi amfani da ita wajen rufe bankunan.
Sai dai da muka tambaye shi ko bankin ta biya abun da ake bin ta kafin aka sake budewa cikin sa’o’i biyu zuwa uku da kullewa, ya ce wata matsayar ce aka cimma shi ya sa aka bude bankin amma ba wai sun biya kudaden ba.
Karshe
A karshe, DUBAWA ta gane cewar lallai labarin da aka yayata ya ce KADRIS ta yi da’awar rufe rassa shida na bankin UBA a dalilin rashin biyan bashin miliyan goma sha hudu da jihar Kaduna ke bin ta. Sai dai da DUBAWA ta je rassan bankunan ta duba, dukansu na bude, illa dai da suka ce mata an rufe hedikwatar bankin a jihar na wasu ‘yan sa’o’i kalilan. Dan haka bayanan bangarorin biyu sun saba wa juna, sai dai abun da ya tabbata a zahiri shi ne KADRIS ta yi da’awar rufe rassa amma ofishi daya ta rufe daga karshe wanda shi ma daga baya an dawo an bude, sa’annan da muka tuntubi jami’in hulda da jama’an KADRIS bai bayyana sunayen rassan bankin da aka kulle ba amma shi ma ya tabbatar cewa an rufe hedikwatar kafin aka dawo aka bude daga baya dan haka babu cikakken gaskiya a cikin labarin yaudara ce kawai.