African LanguagesHausa

Sanarwar CBN dangane da manufofin kasuwannin musayar kudaden ketare, daga shekarar 2017 

Zargi: Ranar Laraba 14 ga watan Yuni, masu amfani da soshiyal mediya suka fara yada wata sanarwar da aka sabunta ake kuma zargin ta fito ne daga babban bankin Najeriya wato CBN mai taken “Sabbin ayyukan manufofi a kasuwannin musayar kudaden ketare.” 

<strong>Sanarwar CBN dangane da manufofin kasuwannin musayar kudaden ketare, daga shekarar 2017 </strong>

Sakamakon Bincike: Karya! Duk da cewa sanarwar ta fito ne daga babban bankin, a shekarar 2017 aka fitar da ita ba sabuwa ba ce kamar yadda ake so a dauka.

Cikakken bayani

Ranar Laraba 14 ga watan Yunin 2023, aka yi rahoton da ke cewa bankin kolin na Najeriya ya umurci bankunan kasuwanci da su yi cinikin kudaden ketare a kowane  farashin canji.

Wannan ya zo ne ‘yan makwanni kalilan bayan da sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ya kama aiki. A jawabin da ya yi a ranar da ya yi rantsuwar kama aiki, shugaban ya yi  alkawarin daidaita yawan kudin ruwa a kasar. Wasu daga cikin nazarin  da aka yi sun nuna cewa matakin da CBN ya dauka zai bai wa bankuna dama su sayar da kudaden ketare a kan farashin da kasuwanni suka amince da su, abun da ke nufin cewa yanzu Najeriya na amfani da farashin da ake amfani da shi ko’ina cikin walwala.

Yayin da rahoton ya ambato majiyoyi daga CBN, duk sun ce ba’a riga an sami tabbaci daga Babban Bankin ba amma ana sa ran samu kafin karshen ranar.

Wadansu masu amfani da soshiyal mediya sun riga sun fara yada sanarwar da ake zargi ta fito daga CBN din ne.

Bisa bayanan sanarwar, CBN “ zai karawa bankunan kudade domin su cimma bukatun ‘yan Najeriya wadanda ke so su yi tafiya dan kansu ko dan kasuwanci, bukau na magunguna da na kudin makaranta, nan da nan.”

Sanarwar na kuma dauke da sa hannun darektan kula da sadarwa tsakanin Kamfanoni, Isaac Okoroafor wanda kuma ya kara baiwa sanarwar nagarta

Tantancewa 

Mun yi amfani da mahimman kalmomi wajen gudanar da bincike a shafin CBN dan gano ko bankin kolin ya fitar da sanarwar da aka ce ya fitar, sai dai wadda muka gani na dauke da bayanai daban da abun da ake yadawa.

Sabuwar sanarwar na dauke da taken “se titled “Canje-canjen aiki ga kasuwar musayar kudaden ketare” kuma Angela Sere-Ejembi, darektar kasuwannin kudi ta sanya hannu ranar 14 ga watan Yunin 2023.

A waje guda kuma, da muka ziyarci shafin CBN mun ga cewa sanarwar da ake yadawa ma na kan shafi amma an wallafa ta ne ranar 20 ga watan Fabrairun 2017.   Sanarwar mai taken “Sabbin ayyukan manufofi a kasuwannin musayar kudaden ketare.” na dauke da lamba mai kamar haka: CCD/GEN/PR/200217.

A lokacin da aka fitar da sanarwar, CBN ya ce zai bai wa bankuna wasu karin kudade domin su cimma bukatun jama’a, sana’o’i, bukatun asibiti da na makarantun ‘yan Najeriya.

Wannan sakamakon irin matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta wajen samun takardun kudin ketare dan gudanar da cinikayyar da suka saba. Dan haka ne CBN ya dauki wannan matakin dan ragewa jama’a wahala.

A Karshe

Yayin da cewa sanarwar ta fito daga CBN din ne, tun watan Fabrairun 2017 ya fito, sadda tsohon shugaba Muhammadu Buhari ke mulki. Sanarwar ba sabuwa ba ce. CBN ya fitar da sabuwar sanarwa mai tsokaci kan wannan batun.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button