Getting your Trinity Audio player ready...
|
Claim: Lauya mai rajin kare hakkin dan adam na da’awar daukar cikin wata wato surrugacy abu ne da aka haramta a Najeriya.
Hukunci: Yaudara ce. Kwararru sun ce babu wata dokar da ta fayyace cewa an haramta mata daukar cikin wasu matan, wanda aka fi sani da surrogacy da turanci.
Cikakken bayani
Surrogacy wani salo ne haihuwa inda mace wadda ake kira surrogate da turanci, (ta na iya yiwuwa mai alaka ta dangi ko mara alakabfvf da iyayen da sha’awar haihuwar) za ta dauki cikin mata da miji, wadanda ke sha’awar samun haihuwa amma watakila saboda wasu dalilai na lafiya matar ba za ta ita daukar cikin ba. Yadda ake amfani da wannan salon shi ne idan har mata da miji sun yi kokarin samun juna biyu na wani tsawon lokaci kuma ba su samu ba, sai a dauki kwan na namijin da na namcen a hada su har sai sun hadu kamar dai yadda irin wannan halittar ke faruwa a cikin dan adama. Sai a dauki wannan kwan a dasa shi a cikin wata macen dan ita ta dauki cikin har zuwa watanni taran da ya kamata.
Wannan salon haihuwar ya fara daukar hankali a Najeriya musamman wajen wadanda suke ta kokarin samun haihuwa amma sun gaza duk kuwa da irin kokarin da suke yi.
Kafar yada labarai ta Sahara Reporters, a shafinta na Instagram, ta wallafa wata hira da aka yi da tashar Arise Television wadda ta janyo takaddama domin lauya mai rajin kare hakkin dan adam Sonnie Ekwowusi ya ce surrogacy haramun ne a Najeriya.
Da ya ke bayani cikin wani bidiyo, Mr Ekwowusi ya bayyana cewa wannan salo ne da ya sabawa dokokin halitta ya kuma kira “hayar mahaifa”
“Matar da ke daukar yaron a ciki na tsawon watanni tara ta zama kamar wata mallaka, wannan ba adalci ba ne. Surrogacy babban cin mutunci ne ga mata,” ya ce.
Tun bayan da aka wallafa labarin 24 ga watan Afrilun 2024, bidiyon ya sami likes 338, da tsokaci 95 sa’annan an raba shi har sau 124.
Ana iya ganin labarin a shafin Facebook wadannan shafukan: Nan, nan, nan, da nan.
Wannan batun na da sarkakiyya sosai, kuma abu ne da ya dauki hankali sosai shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyi tantancewa.
Tantacewa
A cikin mujallar dokokin da suka shafi hakkin dan adam, wani malama a jami’ar Amurkar da ke Najeriya, Olanike Adelakun, ta ce ba’a haramta surrogacy a Najeriya ba, amma kuma ba’a riga an yi la’akari da shi a hukumance ba. Dan haka idan har mutun ya shiga yarjejeniyar surrogacy a Najeriya bai karya doka ko aikata laifi ba.
Yadda ba a bin dokokin da ke sanya ido kan surrogacy a Najeriya, yawancin irin asibitocin da ke taimakwa wadanda kan fuskanci kalubalen haihuwa na amfani da
Hukumar kula da dokokin Najeriya ta bayar da shawarar cewa duk dan da mace ta haifa ta hanyar dashen kwai sadda ta ke gidan aure, mijin ne mahaifin yarin a hukumance.
Haka nan kuma hukumar ta kara bayar da shawarar cewa duk da ko ‘yar da aka haifa ta yin amfani da yarjejeniyar surrogacy, bayan haihuwar dole ne iyayen su dauki yaron a hukumance ko da kuwa yaron na su ne bisa dangantakar da suke da shi na jini.
Ra’ayin kwararru
Mun yi magana da Achille Elizabeth, wata lauyar Najeriya wadda ta fada mana cewa surrogacy ba su da wasu dokoki a bayyane haka.
“Dokokinmu ba su ce komai dangane da shi ba. Abin da mutane kan fada idan ana tattauna batun duk abubuwa ne da ke nasaba da addini, al’ada, da’a da kuma ra’ayoyinsu na kansu. Idan da Surrogacy laifi ne, da an rufe asibitoci da yawa.
“Surrogacy hanya ce ta tallafawa mutane da haihuwa, inda za ka sami mutane su na bayar da tallafin kwai, kuma taimakawa wani ya fadada zuri’arsa ba laifi ba ne a Najeriya. A shekarar 2017, an fitar da wani kudurin dokar da ke da nufin kwaskware dokar lafiya ta kasa wati National Health Act da turanci, dan a kara har da amfani da sabbin fasahohin haihuwa sai dai bai wuce karatu na biyu ba. Dan haka ko dan wannan kuna iya ganin cewa babu wasu dokoki a fayyace dangane da surrogacy,” ta kammala.
Christiana Longe, wata lauyar Najeriyar ita ma, ta bayyana cewa sashi na 30 na dokokin Najeriyar da aka bayyana cikin bidiyon ba shi da wata dangantaka da surrogacy.
“Rashin kasancewar abu a cikin doka ba ya na nufin idan an yi shi zai zama laifi ba ne,” ta kuma bayyana cewa duk wanda ke son amfani da wannan salon haihuwar dole ya rubuta yarjejeniya da kwantiragi, kowa ya sa hannu kafin a aiwatar da shi.
Ta kuma kammala da shawarar cewa kowani bangare ya tabbatar ya dauki lauyoyin da za su sa ido kan yadda komai zai gudana daga farko har karshe.
A Karshe
Da’awar cewa an haramta surrogacy a Najeriya yaudara ce. Sashi na 30 na dokokin Yara wato Child Rights Act da aka yi amfani da shi a bidiyon ba shi da alaka da bayanin da aka yi. Lauyoyin da DUBAWA ta tattauna da su su ma sun tantance cewa babu wasu dokoki a bayyane da suka haramta wannan salon a Najeriya.