African LanguagesHausa

Yaudara! Najeriya ba ta ayyana goyon bayanta ga Iran, Falasdinu a rikicin Isra’ila da Gaza ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X (Twitter) ya wallafa hoton tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, yayin da ya ke shan hannu da shugaban jamhuriyar Islamar Iran, Hassan Rouhani, tare da da’awar cewa gwamnatin Najeriya na goyon bayan Iran da Falasdinu a rikicin Isra’ila da Gaza.

Hukunci: Yaudara ce! Wannan hoton da ake dangantawa da da’awar, tsoho ne domin tun a shekarar 2015 aka dauki shi a wani taron sadarwa a hukumance daga wakilan gwamnatin Najeriya wajen samar da maslaha ta diflomasiyya ga rikicin ba bayyana goyon baya ga wani daga cikin bangarorin da ke rikicin ba

Cikakken bayani

Rikicin Isra’ila da Gaza, babban matsala ce a lamuran da suka shafi siyasa irin ta yanki, kuma ya dade ya na fama da lokutan da ake samun rashin jituwa da tashin hankali tsakanin Isra’ila da yankunan Gaza da ke West Bank.

Rikicin ya kara ta’azara ne ranar bakwai ga watan Oktoban 2023, Sadda kungiyar Hamas ta kaddamar da irin harin da bata taba kaiwa kan Isra’ila ba, inda ‘yan binciga da yawa suka samu suka shiga kananan al’ummomin da ke kusa da zirin Gaza.

Wannan harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,200,  tare daw wasu 250 wadanda ke rike a hannun Hamas din bisa kiyasin Isra’ila. A matsayin martani, Isra’ila ta umurci dakarunta su kai hari ta sama, wanda shi kuma ya yi sanadin mutuwar mutane 33,000 bisa bayana ma’aikatar lafiya ta Gaza.

A waje guda kuma ranar 13 ga watan Afrilun 2024, wani mai amfani da shafin X Sir. Engr. A.Y (@A_Y_Rafindadi) ya ya wallafa wani labari a shafinsa da zargin cewa gwamnatin Najeriya na mika goyon bayanta ga Iran da Falasdinu yayin da ake cikin rikicin na Isra’ila da Gaza.

Labarin ya bayyana ne tare da hoton Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasar Najeriya ya na shan hannu da Hassan Rouhani, tsohon shugaban Jamhuriyar Islamar Iran. Sa’annan a cikin bayanin an rubuta cewa Najeriya yayin da take muba’i’a ga Iran da Falasdinu a abin da yanzu ake kira “yakin duniya na uku.”

Yaudara! Najeriya ba ta ayyana goyon bayanta ga Iran, Falasdinu a rikicin Isra’ila da Gaza ba

Wannan hoton ya dauki hankalin jama’a sosai inda kusan mutane miliyan 1.3 suka kalla, ya sami alamar Like 2,400. Amma mafi mahimmanci a gare mu shi ne daga tsokace-tsokacen da wadanda suka yi ma’amala da labarin suka yi, sun yi imanin cewa labarin gaskiya ne, wasu ma har sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta guji goyon bayan kowani bangare a rikicin.

Northern Pearl (@kadunasAyomide) cewa ya yi “Wace Najeriyar? A madadin ‘yan Najeriya ku fita sha’aninmu. Wutar lantarkin Nepa kadai mu ke bukata.”

Wasu karin mutanen su ma sun bayyana shakkarsu, inda suka ma sanya alamar tambaya a kan ko a matsayinsa na tsohon shugaban kasa, shi Buharin ma ya na da ‘yancin zuwa ya bayyana goyon baya ga kasar da ke yaki, ya kuma ce ya yi hakan ne a madadin Najeriya. De’Otunba GCFRN1( @de_generalnoni) shi ma kusan hakan ya bayyana: “Tinubu ne shugaban kasa ba Buhari ba. Dan haka abin da Tinubu ya ce ne Najeriya za ta yi!”

Wannan da’awar ta zo ne daura da harin da Iran ta kai kan Isra’ila a matsayin ramakon harin da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran din da ke birnin Damascus na kasar Siriya, inda jami’anta da dama suka rasa rayukansu.

Tantancewa

Binciken da DUBAWA ta gudanar ta bayyana cewa wannan da’awar yaudata ce kawai, domin shi kan shi hoton da ake amfani da shi, tun kafin ma a san za’a yi rikicin aka dauke shi. Da muka yi amfani da manhajar binciken hotuna na TinEye da Google Lens Search mun gano daidai sadda aka dauki hoton, kuma a taron koli ne karo na uku na kasashen da ke fitar da iskar Gas(GECF)  wanda ya gudana a shekarar 2015.

Bugu da kari, DUBAWA ta kwatanta da’awar da sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar a hukumance ranar 14 ga watan Afrilun 2024, wanda mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya Francisca K. Omayuli ta rattabawa hannu, ta na kira da a nemi maslaha ta diflomasiyya tsakanin Iran da Isra’ila

Sanarwar ta jaddada cewa duk bangarorin biyu ne ya kamata su nemi hanhoyin sulhu dan tabbatar da daidaiton kasashen duniya baki daya. Binciken da muka kuma yi da mahimman kalmomi ya nuna cewa kafofin yada labarai masu nagarta duk sun yi amfani da sanarawar. Kafofi irin su Channels Television, ait.live, da Arise News su ma sun yi bayani dangane da wannan matsayar ta gwamnati tarayya dangane da rikicin na Iran da Isra’ila.

Sanarwar da aka fitar a hukumace na dauke da taken “NAJERIYA NA KIRA DA A KAMA KAI, BIYO BAYAN TASHIN HANKALIN DA YA AFKU KWANAN NAN TSAKANIN ISRA’ILA DA IRAN,” ta na kira ga bangarorin biyu da su yi amfani da matakan diflomasiyya wajen samun maslaha.

A Karshe

Duk da cewa da’awar da ke cewa Najeriya na goyon bayan Iran da Falasdinu kan rikicin Isra’ila da Gaza ya dauki hankali, bincike mai zurfi da DUBAWA ta yi ya nuna cewa yaudara ce kawai. Shi kan shi hoton da aka yi amfani da shi a sunan hujja tsoho ne, tunda mun gano cewa tun ma kafin a fara rikicin aka dauki hoton. Ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya ta fitar da sanarwar da ke kira ga bangarorin biyu da su nemi maslaha ta diflomasiyya ba tare da nuna goyon bayanta go kowani bangare ba.

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Bridge Radio 98.7FM, Asaba, , domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button