African LanguagesHausa

Shin da gaske ne hukumar bincike ta Amurka FBI ta samu kudade da gwala-gwale na miliyoyin dubban Dalar Amurka a gidan Buhari na New York?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta kamar a wadannan wurare (here, here da here}sun yi da’awar cewa sashin binciken manyan laifuka na Amurka FBI sun gano kudade miliyan dubu biyar na Dalar Amurka da gwala-gwalai wadanda kudinsu ya kai Dala miliyan 700 a gidan tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke birnin New York. Sun kuma yi da’awar cewa Shugaba Donald Trump ya ba da umarni a farwa gidajen ‘yansiyasa ‘yan Najeriya da ke Amurka. 

Shin da gaske ne hukumar bincike ta Amurka FBI ta samu kudade da gwala-gwale na miliyoyin dubban Dalar Amurka a gidan Buhari na New York?

Hukunci: Karya ce. Babu wata sheda da muka gano wacce ta karfafa wannan da’awa koda kuwa daga wata kafar yada labarai. 

Cikakken Sako

A ranar 31 ga watan Janairu, 2024 wani mai amfani da shafin Facebook Mazi Benjamin Madubugwu ya yada wata wallafa, da hoton tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda aka rubuta da wannan taken labarai:

“LABARI DA DUMI-DUMI: An kama kudade Dalar Amurka Miliyan dubu biyar ($5 Billion) da gwala-gwalai da kudinsu ya kai Dala miliyan 700 a gidan Buhari da ke New York, a daidai lokacin da hukumar ta FBI suka kai wani simame kan gidajen ‘yansiyasa daga Najeriya, Trump ya bukaci a tsayar da kudaden a asusu, kasancewar bai amince da shugaban Najeriyar na yanzu ba, wanda ya bayyana da cewa gara Buhari da shi.”

A wannan wallafa an nuna Buhari tare da hoton daloli na Amurka.

A ranar biyar ga watan Janairu,2025 wani shima mai amfani da shafin Instagram  alhaji_comedy, ya wallafa irin wannan da’awa wacce aka yada ta sosai a shafin WhatsApp.

Did FBI find cash, gold worth billions of dollars in Buhari's New York residence?

Hoton sakon da aka yada a WhatsApp.

Lokacin da DUBAWA ta yi amfani da manhajar (“Who posted What”) a shafin Facebook, mun gano karin wasu wallafar kamar a wadannan wurare (here, here, here, here, da here)

Duba da yadda wannan labari ya yadu da hadarin da ke tattare da hakan DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan da’awar;

Tantancewa

Da’awa ta 1: FBI ta gano kudade Dala miliyan dubu 5 da gwala-gwalai da kudinsu ya kai Dala miliyan 700 a gidan Buhari da ke birnin New York.

Shin da gaske ne hukumar bincike ta Amurka FBI ta samu kudade da gwala-gwale na miliyoyin dubban Dalar Amurka a gidan Buhari na New York?

Hukunci: Yaudara ce 

Muhammadu Buhari ya kasance shugaban mulkin sojan Najeriya a tsakanin 1983 zuwa 1985, sannan aka sake zabensa a matsayin shugaban Najeriya a mulkin dimukuradiya a 2015, wanda gwamnatin ta mayar da hankali a yaki da cin hanci da rashawa da matsalar tsaro. Gwamnatinsa ta kawo karshe a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A shekarar 2015 jaridar Vanguard Newspaper ta ba da rahoto cewa Shugaba Buhari ya bayyana kadarar da ya mallaka kafin ya hau karagar mulki kamar yadda mashawarcinsa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya bayyana. Ga abubuwan da rahoton ya nunar da cewa Buhari ya mallaka:

  1. Naira miliyan 30 a asusunsa na banki (Union Bank).
  2. Gidaje biyar da suka hadar da gidaje biyu na laka a Daura.
  3. Filoti guda biyu, daya a Kano daya kuma a Port Harcourt.
  4. Gonaki da garke na shanu da suka hadar da shanu 270 da tumaki 25 da dawaki biyar da tsintsaye da shuke-shuke.
  5. Wasu motoci da suka hadar da guda biyu da ya siya daga asusun ajiyarsa, wasu kuma gwamnati ce ta bashi a matsayin tsohon shugaban kasa, wasu kuma masoyansa ne suka ba shi bayan da mayakan Boko Haram suka kai farmaki ga jerin gwanon motocinsa a 2014.
  6. A kwai kuma shiya-shiya da yake da su a kamfanonin fenti na Bergers da Union Bank da Skye Bank.

Babu labarin cewa yana da mallakin gida a New York kamar yadda aka zayyano a kadarorin da tsohon shugaban ya mallaka a tsawon shekaru takwas da shugaban yayi a kan karagar mulki.

Sai dai a ranar 27 ga watan Janairu, 2025, kwana guda kafin bayyanar wannan da’awa jaridar Business Day ta ba da labari a lokacin da yake ganawa da shugabannin jam’iyyar APC cewa:

“Bayan shekaru takwas na mulkin farar hula, na mallaki gidaje uku ne, ina da gidaje guda uku daya a garin Daura guda biyu kuma a Kaduna, na kuma ba da daya haya da shine nake samun kudade da nake cin abinci.”

A wannan jawabi na shugaban bai nuna cewa Buhari ya mallaki wani gida a New York ba.

Ga dai irin girman wannan zargi da aka alakanta da FBI, da ya kamata a ce wasu manyan kafafen yada labarai sun ba da rahoton, amma babu wata kafa da tayi labarin.

Da’awa ta 2: Shin Shugaba Donald Trump ya ba da umarni a farwa wasu kadarori mallakar ‘yansiyasa daga Najeriya?

Shin da gaske ne hukumar bincike ta Amurka FBI ta samu kudade da gwala-gwale na miliyoyin dubban Dalar Amurka a gidan Buhari na New York?

Hukunci: Karya ce

Tun bayan da aka rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu, 2025, Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan wasu dokoki ko umarni, da fadar White House ta ce sun haure ( 300 directives ) don ya samu damar cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa. Wadannan umarni ko dokoki sun hadar da shigar baki ba bisa ka’ida ba da batun aiki a kasar da tsare-tsare kan makamashi da dokoki da suka shafi muhalli da dokar da ta shafi jinsi da dokar zubar da ciki da harkoki da suka shafi aikin soja.

Sai dai duk da wadannan bayanai da tsare-tsare na Shugaba Trump (speeches and policy actions) babu wata sheda da ta nuna cewa yayi wani jawabi kan ‘yansiyasa daga Najeriya. Idan kuma akwai irin wannan to babu shakka za a ga an ba da rahoto daga wasu kafafen yada labarai masu inganci.

A Karshe 

Babu wata sheda da ta tabbatar da cewa Shugaba Buhari ya mallaki wata kadara a birnin na New York ko Hukumar FBI ta kai wa gidansa simame. Sannan shedu da ke a kasa babu inda suka nuna cewa Shugaba Trump ya ba da umarni a kai “simame kan wasu kadarori” mallakar ‘yansiyasa daga Najeriya.  

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »