Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Bayanan da ke yawo a soshiyal mediya kamar wadanda za ku iya gani a nan, nan, da nan na da’awar cewa kotun hukunta miyagun laifuka na ICC ta bukaci kama shugaban majalisar dokokin Najeriya Godswill Akpabio bisa zargin cin zarafin da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi.

Hukunci: Yaudara ce. Babu hujjojin da suka goyi bayan wannan da’awar. Bincike ya nuna mana cewa kotun ICC ba ta da hurumin shari’a kan batun cin zarafi irin wannan.
Cikakken bayani
Badakalar da ke tsakanin shugaban majalisar dokokin Najeriya sanata Godswill Akpabio da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya ta’azzara a watan Maris na 2025 bayan da sanatar ta yi zargin cewa ya ci zarafinta.
Majalisar ta dakatar da sanatan ne na tsawon watanni shida bayan da ta shigar da korafin da ke zargin Akpabio da cin zarafinta. Bacin haka ta sake shigar da karar cewar ya bata mata suna inda ta bukaci ₦100 billion saboda bayanan batancin da ta ce ya yi mata.
Wannan rikicin ya dauki hakalin al’ummar kada da kasa sadda Natasha ta je ta gabatar da korafinta a hadaddiyar majalisar kasa da kasa da ke birnin New York wato Inter-Parliamentary Union (IPU) in New York, inda ta ce dakatar da itan da aka yi ba komai ba ne illa bita da kullin siyasa. A waje guda kuma an ciga da zanga-zanga a harabar majalisar dokoki inda magoya bayan mutanen biyu suka rabu gida biyu wasu suna kira ga Akpabio din da ya yi murabus.
Wadanna batutuwan ne suka kara yada jita-jita a duniyar gizon inda da yawa ke kokarin fahimtar tasiri ko kuma ma dai sanya alamar tambaya kan abinda sabbin zarge-zargen nata zai haifar.
Yayin da tashin hankalin ke karuwa, haka ma bayanan da ba daidai ba suka cigaba da yaduwa a shafukan soshiyal mediya hatta wadanda suka shafi irin matakan da za’a iya dauka a kan Akpabio a matakin kasa da kasa.
Ranar 24, ga watan Maris 2025, wani shafin Facebook, All-Hubs, ya wallafa cewa kotun ICC ta bayar da umurnin kama Akpabio.
Kadan daga cikin labarin ya ce, “A wani mataki mai ban mamaki, Kotun hukunta miyaun laifuka ta ICC ta bayar da umurnin cafke shugaban majalisar dattawan Najeriya sanata Godswill Akpabio, ta kuma sanya shi cikin jerin wadanda aka hana tafiya. ICC ta bayar da umurnin kama shi da zarar a kan gan shi a cikin kowanne daga cikin kasashen da ke zaman mambobi.”
Bayanin ya kyma kara da cewa ICC ta yi bitan hujjoji na bidiyon da aka tura mata ta kuma bukaci shi kansa shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnatins da su dauki mataki.
Yadda batun ke daukar hankali ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan lamarin.
Tantancewa
Mun duba shafin ICC, sanarwar manema labarai, da shari’o’in da ke kotun inda muka ga cewa babu wani batun da ke da dangantaka da Akpabio. A cewar shafin, Kotun ta na da hurumin sauraron kararrakin da ke da nasaba da kisar kiyashi, laifukan yaki, laifukan da suka take hakkin dan adam, da laifukan nuna fin karfi ko murkushe wadanda ba su ji ba su gani ba — ba laifukan da suka shafi mutun daya na cin zarafi irin wanda ake zargi Akpoti–Uduaghan ya shigar ba.
Duk da cewa kotun ta bayar da umurnin kama manyan mutane irinsu Benjamin Netanyahu na Isra’ila da Osama ALmasri Najim na Libiya, wadannan shari’o’in na da alaka ne da take hakkin dan adam ba wai laifi na rashin da’a ko karya dokoki ba.
Mun gudanar da bincike na mahimman kalmomi kuma ba mu sami wannan bayanin a wata kafar yada labarai mai sahihanci b,a kuma ba wanda ya goyi bayan wannan da’awar abun da ya kara sanya alamar tambaya kan sahihancin batun.
A Karshe
Babu wani tabbaci daga ICC kuma babu wata kafar yada labaraia mai nagarta a ciki da wajen kasar da suka dauki wannan labarin na cewa an bayar da umurninSanata Godswill Akpabio. Bugu da kari laifin cin zarafi irin wannan kotun ICC ba ta da hurumi. Dan hakan wannan ba gaskiya ba ne.