African LanguagesHausa

Shin gaskiya ne wai alamar tantance shafuka a tiwita yanzu ta kai farashin dalan Amurka 20 kowane wata?

Zargi:Kamfanin Tiwita zai rika cazar dalar Amurka 20 kowanne wata dan sanya alamar tantancewa a shafukan tiwitar wadanda ke so

Shin gaskiya ne wai alamar tantance shafuka a tiwita yanzu ta kai farashin dalan Amurka 20 kowane wata?

Ko da shi ke, Mr. Musk ya sanar cewa sabon kamfanin na sa na gudanar da sauye-sauye. Binciken da mu ka yi bai nuna cewa ya fadi wani farashi ba musamman dangane da alamar tantancewar ba.

Cikakken bayani

A wani rahoton da wata kafar yada labaran fasaha mai suna The Verge ta wallafa ranar litini 31 ga watan Oktoba, ta sanar cewa akwai shirin da ake yi na kara farashin kudin wata-watan da akan biya dan samun bayanai a shafin tiwita wanda har zai shafi wadanda ke biya dan samun alamar da ke bayar da tabbacin cewa mai rike da shafin shi ne ainihin mai shi kuma yana samun wani alfanun da ba kowa ke samu ba a shafin.

Dama dai kowane wata a kan biya (dalan Amurka) $4.99 ma abin da ake kira da turanci Twitter Blue. Wannan alamar ruwan bula ce kuma taba bai wa duk mai shi damar samun labarai wadanda babu tallace-tallace a ciki. Sai dai yanzu akawai rade-radin cewa nan ba da dadewa ba za’a kara farashin zuwa $19.99. Idan har aka tabbatarda hakan kuma za’a bai wa masu cin moriyar Twitter Blue din kwanaki 90 domin sun yanke shawarar ko za su cigaba da amafani ko za su daina, idan kuma wa’adin ya wuce ba tare da sun biya ba, zasu rasa alamar.

Akwai labarin cewa ma’aikatan da ke karkashin sabon shugaban kamfanin Mr. Musk wanda ke wa kan sa inkiya da “Chief Twit” na fuskantar matsin lamba domin an tilasta mu su kammala duk wani shirin da ya danganci sauyin kafin 7 ga watan Nuwamba idan ba haka ba su ma su rasa na su aikin a kamfanin.

Ranar litinin 31 ga watan Oktoban 2022 wani labarin da kamfanin Spectator Index ya wallafa shi ma ya nuna cewa lallali za’a daga farashin zuwa $20.

Kasa da sa’o’i 18 da fitar da labarin mutane fiye da 50,000 suka nuna alamar amincewa da labarin har ma suka raba shi da ma’abotan shafukansu sau 11,000. Wasu masu amfani da shafin dariya suka rika yi wa masu biya a yayin da wadansu kuma suka ce ba za su biya ba. Bazwar batun da ma irin tasirin da zai yi kan masu amfani da alamar wadanda yawancinsu ‘yan jarida ne ya sa mu ke so mu tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da gudanar da bincike cikin Tiwita dan ganin ko wannan labari ya dace da wani abin da sabon shugaban Mr. Musk ya bayyana cikin na sa gajerun sakonnin amma ba ta komai ba.

Duk da cewa kamfanin soshiyal mediyar na sa ran samun mafi yawan kudaden shigarta daga wadanda za su rika biya su yi amfani da shafin ne, Mr Musk bai riga ya fito fili ya bayyana farashin da za’a sa ba.

Shugaban wanda mallakarsa ne kamfanonin Tesla da SpaceX wanda mai rajin kare hakkin fadar alabarkacin baki ne ya dade yana sukar wasu daga cikin manufofi da dokokin  kamfanin kafiya ya saye shi, inda ya ma bayyana a fili cewa duk ranar da ya mallaki kamfanin zai yi watsi da irin wadannan manufofin da dokokin da bai yarda da su ba. Shi ya sa ma bayan da ya sayi kamfanin abin da ya rubuta a shafinsa cewa “an saki tsuntsun”

Da ya ke mayar da martani ga wani mai amfani da shafin @johnkrausfotos wanda ya yi kira da a tantance shafin shi da alamar tunda ya na wallafa hotuna ne da suka shafi sama jannati da irin jirage ko rokokin da ke zuwa wurin kuma mutane da yawa na bin shafinsa, Mr Musk ya ce ana kan gyara yanayin tafiyar da tantancewar ne.

Wannan ya nuna alamar cewa akwai yiwuwar samun sauye-sauye a bangaren da ya shafi tantancewar amma bai nuna farashi ba. Haka nan kuma Mr. Musk bai bayyana ko wadanne irin sauye-sauye ake gudanarwa ba.

Binciken da DUBAWA ta yi a shafin google dangane da batun ya sake mayar da ita kan labarin da jaridar The Verge ta wallafa wadda ake ganin da ma ita mafarin wannan hasashen.

Yayin da ta ke kokarin danganta labarin da Mr. Musk ita ma jaridar da yi la’akari da martanin shi ga @johnkrausfotos ne inda ita ma ce martanin ya nuna cewa ana cikin gudanar da wadansu suaye-sauye.

A Karshe

Ko da shi ke, Mr. Musk ya sanar cewa sabon kamfanin na sa na gudanar da sauye-sauye. Binciken da mu ka yi bai nuna cewa ya fadi wani farashi ba musamman dangane da alamar tantancewar ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button