African LanguagesHausa

Bidiyon dodannin gargajiyar da ke dukar jama’a ba na yakin neman zaben APC a jihar Ondo ba ne.

Zargi: Wani mai karfin fada a ji a tiwita ya yi zargin cewa dodannin gargajiya sun fito sun kori magoya bayan dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Ahmed Tinubu yayin da ya ke yakin neman zabe a jihar Ondo

Bidiyon dodannin gargajiyar da ke dukar jama’a ba na yakin neman zaben APC a jihar Ondo ba ne.

Wannan bayanin ba gaskiya ba ne. Ba’a dauki bidiyon a yakin neman zaben APC ba kuma bugu da kari ma bidiyon ba a jihar Ondo aka dauka ba

Cikakken bayani

Yayin da zaben 2023 ke karatowa mutane na nan na shirye-shirye. Yawancin manyan jam’iyyun da ke da ‘yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasr sun riga sun kaddamar da yakin neman zabe. To sai dai a jam’iyya mai mulki har yanzu ba’a kaddamar da yakin neman zaben ba saboda rigingimun cikin gidan da jam’iyyar ke fama da su.

Kwanan nan wani bidiyo ya fito inda aka ga wadansu dodanni irin na gargajiya sun koran mutane a yayin da wadansu dodunan ke kaiwa jama’an duka yayin da suke kokarin tserewa.

Daya daga cikin irin wadanda ke da karfin fada a ji a tiwita, irin wadanda akan kira influencers mai suna Demagogue PhD  ya ce an dauko bidiyon ne lokacin da jam’iyyar APC ke yakin neman zabe a jihar Ondo ranar 13 ga watan Oktoban 2022. Ya kuma ce dodannin sun yi amfani da hakan ne domin su nuna rashin gamuswarsu da jam’iyya mai mulki.

Ya rubuta: “Jiya, APC a jihar Ondo ta je yakin neman zabe wa Tinubu. Sai dai hakan ya fusata dodannin jihar sosai har sai da suka fito su bayyana hakan da dukar wadanda suka halarci yakin neman zaben.”

Mutane sama da dubu hudu suka yi ma’amala da wannan labarin kuma mutane 188,000 sun kalli bidiyon. Sai dai DUBAWA ta lura cewa babu wani abun da ya nuna cewa ana gangamin zabe ne a bidiyon.

Tantancewa

Bayan da dubawa ta karanta tsokacin da aka yi dangane da bidiyon babu wanda ya iya tabbatar da cewa lallai gangamin zabe ne ake yi a Ondo.

Karin binciken da DUBAWA ta yi kuma ya nuna cewa dodannin gargajiya a jihar Ondo su kan yo amfani da ganyen kwa-kwa ne dan girmama allahntakar kakanni. To amma a cikin bidiyon na dakikai 29 babu abin da ya nuna ganyan kwa-kwa ko ma yin amfani da su.

Da muka yi amfani da kalmomin mu ka yi binciken mutanen da dodannin gargajiya ke kora, shafin yanar gizon ya sada mu da wani rahoton da aka yi ranar 18 ga watan Satumba inda aka yi labarin cewa dodanni sun shiga coci suna koran mutane a al’ummar Shikal da ke karamar hukumar Langtang ta kudun da ke jihar Filato.

Rahoton ya bayyana cewa jami’in ‘yan sandan da ke hulda da jama’a DSP Alfred Alabo ya tabbatar da afkuwar lamarin bayan da ya zanta da DPOn yankin. Ya kuma bayyana cewa an shawo kan lamarin.

A Karshe

Bidiyon da ake yawo da shi a sunan yakin neman zaben APC a jihar Ondo, ba yakin neman zabe ba ne kuma ba daga jihar Ondo ya fito ba. Bidiyon ya fito daga jihar Filato ne inda wadansu dodanni suka ce suka tayar da zaune tsaye a wadansu cocuna. Dan haka wannan zargin karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button