African LanguagesHausa

Shin harin Amurka ya lalata gidan Gumi?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani shafin Facebook mai suna LAMBO GINI PROMOTION, yayi da’awar cewa Amurka ta kai hari a Kaduna a ranar 1 ga Janairu,2026 inda ta lalata gidan Sheikh Ahmad Gumi.

Shin harin Amurka ya lalata gidan Gumi?

Hukunci: Karya ne. Babu wata kafar yada labarai da ta tabbatar da cewa Amurka ta kai hari a jihar ta Kaduna a ranar 1 ga Janairu,2026, ko wani dalili da yayi sanadi na lalata gidan Sheikh Ahmad Gumi.

Cikakken bayani

Wani shafin Facebook, LAMBO GINI PROMOTION (kamar yadda ake gani nan),  a ranar 1 ga Janairu 2026, ya wallafa labarin cewa Amurka ta kaddamar da hari kan ‘yanta’adda a jihar Kaduna inda a wannan harin aka lalata gidan Sheikh Ahmad Gumi.

Ga abin da wani bangare na wallafar ke cewa “LABARI DA DUMI-DUMI wani harin da Amurka ta kai maboyar ‘yanta’adda a Kaduna ya lalata gidan Gumi, ya zuwa yanzu Amurka na ci gaba da lugudan wuta a maboyar ‘yanta’adda a Kaduna, a kalla sansanin ‘yan ta’adda uku ne harin ya lalata kafin daga bisani sojojin Najeriya suka shiga suka karasa cika aiki ga ‘yan’taddar, abin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana da cewa goron sabuwar shekara ne ga ‘yanta’adda.”

Ya zuwa ranar 1 ga Janiru, 2026 wannan wallafa ta samu masu tsokaci (comments) 300 da wadanda suka sake yadawa 128. Mun lura da dama masu tsokacin a Facebook sun jinjinawa wannan yunkuri ga misali Kolawole Paseda ya rubuta cewa “Godiya mai yawa shugaban kasa Allah Yayi maka albarka da kasar ka ta Amurka.”

Prince Awofeso Rasheed Ololade yayi tsokaci da cewa wannan harin ga gungun ‘yanta’addar na da tasiri ta fuskar tattalin arziki da zamantakewar al’umma a tsawon shekaru, mu kali shigar Amurka a matsayin taimakon Allah.”

Julius Emmanuel ya rubuta cewa “WOW wannan babban labari ne a sabuwar shekara.”

Mun kuma ga wannan wallafa a wasu shafukan sada zumunta irin na Instagram da aka yada kamar a wadannan wurare nan da nan da nan.

DUBAWA karkashin shirin gano gaskiyar labari an bibiyi wannan da’awa don tantancewa saboda abu ne da ya shafi tsaro kasancewar ko da a ranar 25 Disamba, 2025 ta kai hari a Najeriyar.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi kamar jihar Kaduna da harin Amurka da Trump da ‘yanta’adda. Sakamakon ya nunar da cewa babu inda Amurka ta kai hari a Kaduna ko shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ba da umarni a kai hari ranar 1 ga Janairu,2026.

Duba da girman wannan da’awa da tuni kafafan yada labarai na cikin gida da waje sun dauki labarin amma babu inda aka ga wannan labari.

DUBAWA har ila yau ya duba shafin sada zumunta na Shugaba Donald Trump amma babu inda yayi wannan kalami ko inda yayi wata magana kan kai hari a Kaduna a wannan rana.

An kuma duba shafin X na ma’aikatar harkokin wajen Najeriya babu inda ma’aikatar ta ba da tabbaci na wannan labari ko ta fitar da labarin cewa Amurka ta kai hari a Kaduna.

Bincike ya nunar harin Amurka na bayan nan da ta kai a Najeriya ya faru ne a ranar 25 da 26 ga Disamba, 2025 inda ta nufi mayakan da ke da alaka da ISIS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya musamman a jihar Sokoto ba jihar Kaduna ba, kuma wannan hari an kai shi da sanin gwamnatin Najeriya kuma ta yi amfani da jirgi ne mara matuki a yankin Tangaza da dajin Bauni.

Mun kuma bincika shafin Facebook na Sheikh Ahmad Gumi a ranar Alhamis 1 ga Janairu,2026, anan kuma babu wani labari da ya tabbatar ko ya ba da haske an kai hari a gidan malamin.

A Karshe

Babu wata hujja da ta nuna cewa Amurka ta kai hari a Kaduna a ranar 1 ga Janairu,2026, ko cewa an kai farmaki da lalata gidan Sheikh Ahmad Gumi. Labarin da ke yaduwa a shafin sada zumunta na karya ne. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »