African LanguagesExplainersHausaMedia Literacy

Shin Majalisar Dokoki ta kasa za ta iya kirkirar jiha ita kadai?

Getting your Trinity Audio player ready...

Gabatarwa

A ‘yan kwanakin nan labarin yiwuwar kirkiro jihohi ya bulla tare da daukar hankulan jama’a inda aka rika mahawara da bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan ainihin wanda ke da alhakin kirkiro jihohi a kasar. Wannan rahoton ya fayyace wanda ke da alhaki ya kuma yi karin bayani daki-daki kan matakan da suka dace a dauka.

Ya zuwa yanzu, Najeriya na da jimillar jihohi 36 da kuma wani yanki da ke zama babban birnin tarayya (FCT) na kasar. Yayin da shiyyar Arewa-maso-Yamma ke da jihohi bakwai, Arewa maso Gabas, da Arewa ta Tsakiya, da Kudu-maso-Kudu da Kudu-maso-Yamma suna da jihohi shida kowacce. Kudu maso gabas ne kadai ke da jihohi biyar.

Kasancewar ta kasa mai al’umma iri daban-daban, ƙabilu daga kowane bangare na fafutikar ganin an samar da sabbin jahohi ta yadda za su samu cikakken iko da ikon mulkin waɗannan yankunansu. 

Duk da cewa neman ballewar na da kamar wuya saboda kasancewar Najeriya mai tsari irin na tarayya, kundin tsarin mulki ya sa kirkirar jiha ya zama kusan abinda ba zai yiwu ba, saboda ko mi za ayi dole ne ya kasance kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. 

DUBAWA ta yanke shawarar yin bincike domin fayyace wa al’umma yadda tsarin yake, a matsayin wani bangare na shirinta na wayar da kai da kuma sanarda al’umma bayanai (MIL).

Cece-kuce dake tattare da kirkiro jihohi

A shekarar 2023, babbar kungiyar al’adun kabilar Igbo, Ohaneze Ndigbo, ta yi barazanar kai karar gwamnatin Najeriya kan gazawarta na samar da karin jiha ga yankin Kudu maso Gabas, bukatar da yankin ya kwashe shekaru da dama yana nema..

Emmanuel Iwuanyanwu, tsohon shugaban kungiyar, ya bayyana damuwarsa akan yin adalci da daidaito a tsakanin jihohi, kasancewar yankin Kudu maso Gabas jihohi biyar kacal yake da.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da kiran, inda har wasu kungiyoyin ke cewa samar da sabbin jihohi a Najeriya zai zama wani abu almubazzaranci, yayin da wasu ke ganin cewa akwai bukatar hakan ne domin a kawar da fargabar wata kabila za ta yi mamaya a ko ina. 

A ‘yan kwanankin nan, masu amfani da shafukan sada zumunta da dama sun yi da’awar cewa Majalisar Dokoki ta kasa na shirin kirkiro sabbin jihohi a Najeriya. Amma, shin Majalisar Dokoki ta kasa za ta iya kirkirar jiha ita kadai?

Me doka ta ce kan kirkirar jiha? 

Binciken da DUBAWA ta yi ya nuna cewa, kafin a iya kirkirar wata jiha ana bukatar daukar tsauraran matakai da suka hada da tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma neman amincewa, ciki har da kuri’u kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar dokokin kasar da amincewar shugaban kasa, da kuma zaben raba gardama a yankunan da lamarin ya shafa.

Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya tanadi wasu sharudda da kudurin dokar kafa wata sabuwar jiha zai cika kafin ya zama doka.

Kamar yadda sashe na 8 (1) na Kundin Tsarin Mulki ya tanada, sai an fara gabatar da buƙata, wanda aƙalla kashi biyu bisa uku na membobin majalisa (wadanda ke wakiltar yankin da ke neman a kafa sabuwar jiha) ke goyon bayanta.

Mambobin da ake bukata su ne: Majalisar Dattawa da ta Wakilai, da Majalisar Dokokin Jiha, da na kananan hukumomi daga yankin, wadanda za su miƙa wa Majalisar Dokoki ta kasa.

Haka kuma sharadi ne: “A amince da kudurin kirkirar jiha a zaben raba gardama da akalla kashi biyu bisa uku na al’ummar yankin suka goyi bayan bukatar samar da jiha.

“Sakamakon kuri’ar raba gardama ya samu amincewa da mafi rinjaye na dukkanin Jihohin Tarayya da ke da rinjayen ‘yan Majalisar Dokoki na jiha; kuma

“An amince da bukatar ta hanyar gabatar da wani kuduri da kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar dokokin kasar suka amince da shi.”

Mahangar masana 

Da yake karin haske kan cece-kucen da ake yi kan samar da jihohi a Najeriya, Akin Rotimi, mai magana da yawun majalisar wakilai, ya shaidawa DUBAWA cewa, kwamitin ya duba shawarwarin da aka gabatar na kirkiro sabbin jihohi ne kawai kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. 

Ya ce kwamitin majalisar wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar ya karbi bukatu na samar da jihohi 31 a cikin aikin gyaran kundin tsarin mulki, hakan ne ya haifar da muhawara tsakanin ‘yan Najeriya daga yankuna daban-daban.

“Wadannan shawarwarin, waɗanda aka gabatar a matsayin bukata, wasu daidaikun mutane masu zaman kansu ne suka gabatar, ba sa wakiltar matsayin majalisar.

“Wadannan bukatun da aka gabatar za a yi nazari sosai a kansu majalisa, ciki har da sauraron ra’ayoyin jama’a, tuntubar masu ruwa da tsaki, da matakan amincewa daban daban kafin a iya aiwatar da wasu sauye-sauyen tsarin mulki,” in ji Akin Rotimi. 

Ya bayyana wa Dubawa cewa Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya ya gabatar da shawarwarin ne kawai a zaman majalisar a ranar Alhamis, 6 ga Fabrairu, 2025.

A Karshe 

Majalisar dokoki ta kasa ba za ta iya samar da wata jiha ba ita kadai, dole ne a samu amincewar mutane ta hanyar kuri’ar raba gardama da kuma wasu matakai da zasu biyo baya. Duk da cewa ana kiraye-kirayen samar da sabbin jahohi a Najeriya saboda batutuwan da suka shafi daidaito, adalci ko bai wa kowa fifikon da ya dace.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »