African LanguagesHausa

Shin Mimiko ne kadai gwamnan jihar Ondon da ya cika wa’adinsa ya na raye kamar yadda ake zargi?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook na da’awar cewa Olusegun Mimiko ne kadai gwamnan jihar Ondon da ya cika wa’adinsa a mukamin gwamna ya na raye. 

Shin Mimiko ne kadai gwamnan jihar Ondon da ya cika wa’adinsa ya na raye kamar yadda ake zargi?

Sakamakon bincike: KARYA. Duk sauran gwamnonin da aka taba yi a jihar sun cika wa’adinsu cikin koshin lafiya, in banda wannan gwamnan wanda ya gamu da ajalinsa ranar 27 ga watan Disemba 2023.

Cikakken bayani

Gwamnan jihar Ondo mai ci yanzu, Rotimi Akeredolu, ya gamu da ajalinsa bayan da ya yi fama da rashin lafiyar da yanzu aka bayyana a matsayin cutar daji, a cewar Bamidele Ademola-Olateju, kwamishanan yada labarai da fadakarwa na jihar.

Ra’ayoyi mabanbanta sun bulla bayan rasuwar Akeredolu a jihar ta Ondo. Yayin da batun ya kasance da ban takaici ga magoya bayansa, wadansu na da ra’ayoyi na daban dangane da dan siyasar mai shekaru 67 na haihuwa. Ga wasu lokaci ne da ya kamata a tattauna abubuwan da ke faruwa a jihar.

Okori Foods wani mai amfani da shafin Facebook ta ce Olusegun Mimiko ne kadai gwamnan jihar wanda bai mutu kafin ya cika wa’adinsa na gwamna ba. Ta ce, “ashe Mimiko ne kadai gwamnan jihar Ondon da bai gamu da ajalinsa yayin da yake kujerar jagorancin jihar ba. Hmm, mutanen jihar Ondo, wai me ke faruwa ne?”

Ya zuwa ranar 27 ga watan Disembar 2023, mutane 420 sun latsa alamar like, na yi tsokaci 89 sa’annan an sake rabawa zuwa wasu shafukan sau 67, da ra’ayoyi mabanbanta.

Afolashade Bukola ta ce, “Wannan na nuna cewa Mimiko ta yi wa mutanen Ondo aiki yadda ya kamata, Allah ya ja zamaninsa.”

Ita kuwa Akande Joy ra’ayinta ya banbanta domin cewa ta yi “kina nufin sun rasu yayin da suke kujerar shugabanci ko kuma bayan da suka sauka, domin idan tune sarai da sadda Agagu ya rasu, kuma bayan ya sauka daga kujerar mulkin ne, da dadewa ma bayan nan.

Bisa la’akari da irin wadannan ra’ayoyin da mahawarorin da suka biyo baya ne DUBAWA ta yanke shawarar gano gaskiyar lamarin.

Tantancewa

Ta yin amfani da mahimman kalmomin da ke da alaka da jihar Ondo, mun gudanar da binciken da ya bayyana mana wadansu mahimman batutuwa dangane da jihar.

Tun bayan da Najeriya ta dawo bisa turbar dimokiradiyya, sau biyu ne kadai wani gwaman a jihar  ya sami damar yin tazarce ya je wa’adi na biyu: Olusegun Mimiko da Rotimi Akeredolu, a cikin wadannan mutanen biyo, Mimiko ne ya cika nasa wa’adin na shekaru takwas.

Wannan na nudin cewa ‘yan siyasa hudu ne suka jagoranci jihar tun shekarar 1999 – sadda dimokiradiyyar ta dawo, daga Adebayo Adefarati na jam’iyyar AD wanda ya jagoranci jihar daga 1999 zuwa 2003 kafin ya sha kaye a hannun Olusegun Agagu na PDP.

Wa’adin Agagu na biyu kuma ya zo karshe bayan da kotun daukaka kara a awatan Yulin 2008 ta baiwa Mimiko jagorancin kasar a karkashin inuwar jam’iyyar LP. Bayan da ya yi shekara daya yana mulki bayan zaben da aka yi a jihar ranar 17 ga watan Arilun 2007, Mimiko ya mika mulki ga Akeredolu na jam’iyyar APC a shekarar 2016.

DUBAWA ta gano cewa Adefarati, ya rasu ya na da shekaru 76 na haihuwa, ranar 29 ga watan Maris a Asibitin Tarayya da ke Owo, sakamakon wata cutar da ba’a bayyana ko mece ce ba. Magajin shi Agagu kuma ya yanke jiki ne ya fadi bai sake tashiwa ba a gidansa da ke Legas ranar 13 ga watan Satumban 2013, ya na da shekaru 65 na haihuwa, shekaru hudu bayan da kotun daukaka karar ta soke zaben shi a shekarar 2009.

Tunda Mimiko ya na nan cikin koshin lafiya tun bayan da ya kammala wa’adinsa a shekarar 2016, Akeredolu ne kadai gwamnan da ya mutu yayin da ya ke kan kujerar gwamna a jihar da shekaru 67 na haihuwa. Mataimakin Akeredolu, Lucky Aiyedatiwa  ya maye gurbinsa, jim kadan bayan rasuwarsa aka bayyana hakan.

A Karshe

Yayin da yawancin gwamnonin jihar ta Ondo ba su iya kammala wa’adinsu kafin aka tsige su, Akeredolu ne kadai ya gamu da ajalinsa yayin da ya ke shugabanci. Dan haka wannan zargin karya ne kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button