African LanguagesHausa

Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, jazaman ne mutun ya yi NYSC kafin ya sami mukami na siyasa?

Getting your Trinity Audio player ready...

National Youth Service Corps (NYSC) wato shirin yi wa kasa hidima a Najeriya shiri ne da aka kaddamar sama da shekaru 50 da suka gabata a karkashin dokar  Decree No.24 na ranar 22 da watan Mayin shekarar 1973 domin inganta dangantakar da ke tsakanin matasan Najeriya da kuma hadin kan kasa baki daya. Na tsawon shekara daya ne ake tilastawa duk ‘yan Najeriyar da suka kammala karatu a jami’a ko makamancin shi, wadanda kuma suke da shekaru kasa da 30 na haihuwa yi.

Mahimmancin wannan shirin wajen samun mukaman siyasa a matakan gwamnati na cigaba da janyo cece-kuce. A shekarar 2018, jaridar Premium Times ta yi rahoton yadda ministar kudin wancan lokacin, Kemi Adeosun, ta ki yin NYSC, kuma a maimakon haka ta gabatar da satifiket din karya, wanda daga baya ya kai ga murabus din ta. Haka nan kuma a watan Fabrairun 2023, wani rikicin ya sake kunno kai dangane da takardun NYSC na gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah. Yayin da akwai damuwa masu nagarta na cewa kotu na amfani da sahse na 177 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wanda bai bayyana NYSC a matsayin tanadi na tsayawa takarar gwamna ba, ya ma sake fayyace cewa zuwa NYSC ba lallai ba ne wa wanda ke so ya rike mukamin gwamnati. 

Kwanan nan, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya zabi wata wadda ta kammala NYSC, Nafisat Buge a matsayin daya daga cikin wadanda ya ke so a tantance a matsayin kwamishina. Wannan matakin ya sami yabo sosai daga wajen shugaban NYSC na jiharm Onifade Olaoluwa, sai dai wani mai amfani da shafin  X Chidi Odinkalu, CGoF (@ChidiOdinkalu) ya ce ba shi da wani mahimmanci.

Mr Odinkalu ya bayyana mamakin da ya je da ya sami labarin cewa an gabatar da wadda ta kammala NYSC domin a cewar shi, NYSC tanadi ne mai mahimmanci a dokokin kasa wanda ake amfani da shi wajen samun aikin yi.

Wannan rikicin wanda ya ki ci ya ki cinyewa dangane da takardun kammala NYSC din ta yadda ya shafi siyasa da aikin yi ne DUBAWA ta ce za ta gudanar da bincike a kai dan sanin gaskiyar abun da ya kamata.

Me doka ta ce? 

Dokar da ta girka NYSC, na daya daga cikin dokokin da ke kunshe a kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda kasar ke amfani da shi yanzu. Sashe na 315 (5) na kundin tsarin mulkin Najeriyar ya goyi bayan duk abubuwan da ke cikin dokar da ma a shekarar 1993. Sauran dokokin da ke da alaka da ita ma kamar dokar n

Sashe na 12 na dokar NYSC ya ce, “Duk wanda zai nemi aiki a ko’ina a cikin tarayyar, kafin a sami aikin, wajibi ne kamfanin da ke so ya dauki mutumin aiki ya tambayi ko yana da takardar kammala NYSC daga duk wanda ya ce ya yi kammala karatun digiri daga shekarar 1973 zuwa 1977. Sa’annan kuma bayan kowace shekara daga nan.

“Sashe na 11 na wannan dokar ya tanadin samar da wwafin satifiket na NYSC na wannan mutumin, kuma idan har shekarun shi/ta sun wuce wanda aka kayyade dole su gabatar da satifiket din ke cewa an zame su bisa la’akari da tanadin sashe na 17 na wannan dokar da sauran bangarorin da ke da mahimmanci kamar yadda dokar ta bayyana.

Dokar ta kuma ce alhakin wanda ke da na niyyar bayar da aikin ya gabatar da wannan takardar ga dan sanda, wanda mukaminsa bai yi kasa da sufeton ‘yan sanda ba, wato wannan satifiket din da duk wata takardar da za ta tabbatar da wannan.

Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, jazaman ne mutun ya yi NYSC kafin ya sami mukami na siyasa?

Dokar da ta girka NYSC. 

Shin wannan sashen wanda ke bayani a kan aikin yi ya na tasiri ma idan aka zo fannin mukamai na siyasa?

Abin takaicin shi ne, kundin tsarin mulkin ya bayyana tanadin dokar dangane da zaben Antoni Janar a sashe na 86, na gwamnoni a sashe na 177, sai kuma na ‘yan majalisa a sashe na 65.

A sashe na 86  kundin tsarin mulkin ya ce, “Shugaban kasa zai zabi Odita Janar na tarayyar bisa la’akari da shawarar da ya samu daga Hukumar da ke Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sa’annan majalisar dattawa ta tabbatar da zaben. (2) shugaban kasa ne ke da alhakin yaben Odita-Janar na kasa.”

Yadda ya shafi ofishin gwamna kuma, sashe na 177 ya yi bayanin cewa, “Mutun zai cancanci tsayawa takara wa mukamin gwamnan jiha ne idan har shi haifaffen Najeriya ne, kuma ya kai shekaru 35 na haihuwa, sa’annan shi kuma mamba ne na jam’iyya wanda ke rike da nagartattun takardun da ke shaida cewa akalla ya kammala karatu zuwa makarantar sakandare.”

‘Yan majalisa kuma sashe na 65 (1) na bayanin cewa, “bisa tanadin sashe na 66 na kundin tsarin mulki, mutun ya cancanci tsayawa takara dan samun kujera a majalisar dattawa idan har shi/ita dan asalin Najeriya ne kuma ya cika shekaru 35 na haihuwa, yayin da ake bukatar wanda ya kai shekaru 30 na haihuwa wa wanda ke neman kujera a majalisar wakilai.

Sashe na 65 (2) ya ce” mutun zai cancanci tsaywa takara a zabe a karkashin karamin sashe (1) na wannan sashen  idan har ya kammala karatun sakandare kuma mamba ne na jam’iyya wadda kuma ta dauki nauyin shi.

NYSC ba ya cikin abubuwan da ake bukata. Kuma ya kamata a yi la’akari da cewa ko kotu ma ta yanke hukunce-hukuncen da ke watsi da tanadin satifikat na NYSC din idan ya zo ga mukaman gwamnati. 

A shekarar 2018, wata kotun tarrayya a Abuja ta yanke hukuncin cewa Madam Adeosun ba ta karya wata doka ba sadda aka zabe ta a matsayin ministar kudi a shekarar 2015 duk da cewa ba ta je NYSC din ba. Haka nan kuma, a zaben da aka yi bara, irin hukuncin da kotu ta yanke ke nan dangane da batun rashin zuwa NYSC din gwamnan Enugu

Ra’ayin kwararru

Kwararriya kan shari’a, Elizabeth Achimugu, ta ce kafin yanzu, idan har mutun na neman aiki, ko kuma za shi neman digiri na biyu ko kuma ma dai ya na neman wani mukami na siyasa, dole sai kana da satifiket din NYSC amma yanzu abubuwa sun sauya.

Bisa la’akari da rikicin  satifiket din Kemi Adeosun, ta ce, “idan har ban manta ba, tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun ba ta yi NYSC ba, kuma dan haka ne ma aka cire ta a matsayin minista. Dan haka abu ne da aka dauka da mahimmacin gaske, kuma mutane sun damu da shi sosai. Duk da cewa ta kammala jami’a da dadewa, ba ta samu ta je ta yi wa kasar hidima ba.”

Duk da cewa mutane sun bayyana damuwarsu, kuma hukumar NYSC din kanta ta fito ta ce an  an sabawa dokar da ta girka NYSC din dan haka ya haramta, ta ce shugaba Tinubu ya bayar da umurnin cewa mutun na iya yin wani aikin a matsayin mai yi wa kasa hidima. Dan haka mutun na iya yin NYSC daura da wani aikin na daban.

Shi ya sa ta kara da cewa babban abun tambaya a nan shi ne ko umurnin shugaban kasar ya fi doka karfi (dokar NYSC).

“Ya kamata NYSC ya zam tilas wa duk wanda ya kammala karatu kuma yana da sha’awar samun wani mukami na siyasa, kuma shi ya sa Kemi Adeosun ta tafi, amma a wannan sabuwar gwamnatin hakan ba ya aiki domin ko gwamnan Enugu na yanzu bai gama NYSC ba. Ya gabatar da takardunsa inda NYSC suka ce bai kammala ba, amma shi gwamna ne yanzu. Duk da cewa haka doka ta tanadar, a zahiri dai ana iya cewa shugaba Tinubu ya sauya dokar.”

Wani masanin shari’ar shi ma, John Achile, da ya ke tsokaci dangane da batun ministar da aka zaba wadda ita ma har yanzu ta ke bautar kasa, ya ce akwai turjiya sosai a wannan gwamnatin.

A cewarsa, “Ya kamata ya zama tanadi, amma wasu lokuta, kamar sojoji a kan dauke mu su wannan nauyin. Amma a halin da ake ciki yanzu abun da ake yi ba daidai ba ne. 

Mun kuma tuntubi Inibehe Effiong dan jin ta bakinsa dangane da batun amma ba mu sami amsa ba. 

A Karshe

Yayin da dokar NYSC da masana dokoki suka ce yin NYSC na da mahimmanci dan samin aikin yi da mukami na siyasa, kundin tsarin mulki bai fayyace tanadin da kyau ba hukunce-hukuncen da aka yanke su ma sun yi watsi da wannan tanadin. Dan ko satifiket na NYSC na da mahimmanci wajen samun mukami na siyasa yanzu ya zama wani abin mahawara, bisa la’akari da bangaren da mutun ya ke.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button